Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kaddamar da bikin baje kolin kanana da matsakaitan kamfanoni na kasa da kasa
2019-06-25 13:24:55        cri
A jiya Litinin, an kaddamar da bikin baje kolin kanana da matsakaitan kamfanoni na kasa da kasa karo na 16 a birnin Guangzhou na kasar Sin. Kamfanoni kimanin 3000 na gida da waje da kasashe da kungiyoyin duniya kusan 38 ne suka halarci bikin.

Ministan masana'antu da sadarwa na kasar Sin, Miao Wei ya bayyana cewa, bikin ya kasance mafi kasaita da kuma tasiri a kasar Sin ta fannin bunkasa kanana da matsakaitan kamfanoni, wanda kuma ya taimaka ga hadin gwiwa da mu'amala a tsakanin kamfanonin sassan duniya. Kasar Sin na son hada kai da sauran kasashen duniya, ta yadda bikin zai taka rawarta yadda ya kamata, don taimakawa kanana da matsakaitan kamfanoni wajen samun ci gaba, tare da samar da gudummawa ga ci gaban tattalin arzikin duniya.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China