Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ra'ayoyin kasar Sin a taron G20
2019-06-25 13:09:21        cri


A wannan sati, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai je birnin Osaka na kasar Japan don halartar taron kolin kasashe 20 masu karfin tattalin arziki a duniya wato G20. Tun daga shekara ta 2013 ya zuwa yanzu, sau shida Xi ya halarta ko kuma ya jagoranci taron kolin G20, wanda ya dade da bayyana cewa, kungiyar kasashen G20, ta duniya ce baki daya, ba membobinta 20 kadai ba. Xi ya kara da cewa, G20 na son samar da bunkasuwa da alheri ga daukacin kasashen duniya gami da jama'arsu.

A halin yanzu, ana kara samun dunkulewar tattalin arziki a duniya. A karon farko, Xi Jinping ya halarci taron kolin G20 a birnin Saint Petersburg na kasar Rasha a shekara ta 2013, inda ya bayyana ra'ayoyin gwamnatin kasar Sin na goyon-baya gami da bunkasa tsarin budadden tattalin arzikin duniya wanda ko wace kasa za ta iya amfana. Kamar yadda ya ce, ya kamata kasa da kasa su kara bude kofarsu ga juna domin yin mu'amalar tattalin arziki. Idan an dauki matakan ba da kariya ga harkokin kasuwanci ko kuma samar da agajin kasuwanci fiye da kima, babu wanda zai ci alfanu.

Wani muhimmin aikin da kungiyar kasashen G20 ke yi shi ne neman samun sabon kuzari ga habakar tattalin arzikin duniya. Xi ya ce, ba kirkire-kirkire a fannonin kimiyya da fasaha da masana'antu kawai ya kamata a yi ba, kamata ya yi a yi su a fannonin da suka shafi manufa da ra'ayi da salon bunkasuwa. A wajen taron kolin G20 wanda aka yi a birnin Brisbane na kasar Australiya a shekara ta 2014, shugaba Xi ya jaddada cewa, ya kamata a yi kirkire-kirkire ga manufofi da ra'ayoyi gami da hanyoyin samar da bunkasuwa, da kara mai da hankali kan inganci da amfanin bunkasuwar. Xi ya ce, ya zama dole a yi kwaskwarima ga bangarorin tattalin arziki da kudi da zuba jari da cinikayya da samar da aikin yi, a kokarin raya tattalin arziki mai dorewa ta hanyar daidaita manufofin tattalin arziki da na zaman rayuwar al'umma.

Zuwa shekara ta 2015, tattalin arzikin duniya na ci gaba da tafiyar hawainiya, inda a wajen taron kolin G20 a birnin Antalya na kasar Turkiyya, shugaba Xi ya bayyana batutuwa biyu da ya kamata a mai da hankali kansu domin tinkarar matsalar tattalin arzikin duniya, wadanda suka hada da, na farko, a kara fahimtar ainihin yanayin tattalin arzikin duniya, na biyu, a samar da kyawawan dabarun farfado da tattalin arzikin duniya da kara samar da guraban ayyukan yi, inda kasar Sin ta nuna wasu ra'ayoyinta guda hudu na lalubo bakin zaren daidaita koma-bayan tattalin arzikin duniya. Na farko, a kyautata manufofin tattalin arziki daga dukkan fannoni, na biyu, kara azama wajen yin gyare-gyare da kirkire-kirkire, don samar da dauwamammen ci gaban tattalin arzikin duniya. Na uku shi ne, inganta tsarin raya budadden tattalin arzikin duniya wanda kowa zai iya cin gajiya. Na hudu wato na karshe shi ne, tabbatar da ajandar neman dauwamammen ci gaba nan da shekara ta 2030.

Sai kuma a shekara ta 2016, aka shirya taron kolin kasashen G20 a birnin Hangzhou na kasar Sin, inda shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa, ya zama tilas a sauya salon kasashen G20, daga shawo kan matsalolin ba-zata zuwa kafa tsarin neman ci gaba mai dorewa, don bayar da gudummawa ga tattalin arzikin duniya baki daya. Shugaba Xi ya kuma jaddada cewa, ya kamata a yi kokarin kafa tsarin daidaita tattalin arzikin duniya mai adalci da amfani, da kafa budadden tsarin kasuwanci da zuba jari na duniya, da raya makamashi ba tare da gurbata muhalli ba, tare kuma da kafa tsarin bunkasuwa dake kunshe da bangarori daban-daban a duniya.

Zuwa shekara ta 2017, a wajen taron kolin G20 wanda aka yi a birnin Hamburg na kasar Jamus, shugaba Xi ya ci gaba da bayyana wasu manufofin daidaita harkokin tattalin arzikin duniya, inda ya ce, ya kamata a ci gaba da shawo kan hadurra da za su kunno kai a kasuwannin hada-hadar kudi, da raya tattalin arziki ta hanyar da ta dace, haka kuma ya yi kira ga bangarori masu ruwa da tsaki su zama tsintsiya madaurinki daya domin raya ci gaba mai dorewa.

Bara wato shekara ta 2018 ta cika shekaru 10 da fara gudanar da taron kolin G20, inda a birnin Buenos Aires na kasar Argentina, Xi Jinping ya bayyana makomar kungiyar G20. A cewarsa, a cikin shekaru 10 da suka wuce, kungiyar ta nuna himma da kwazo wajen farfado tattalin arzikin duniya. A shekaru 10 dake tafe kuma, ya kamata kasashen G20 su kara azama wajen ciyar da tattalin arzikin duniya gaba.

Daga ranar 28 zuwa 29 ga wata, za'a yi taron kolin G20 a birnin Osakar kasar Japan, inda a karo na bakwai shugaba Xi Jinping, zai halarci taron.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China