Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yadda Amurka ta tsananta takaddamar ciniki a tsakaninta da Sin ya kawo rashin tabbaci ga tattalin arzikin duniya
2019-06-21 15:11:56        cri

Masanan kasar Sin da dama sun bayyana jiya Alhamis a nan Beijing cewa, ba za a iya raba kasashen Sin da Amurka ta fuskar tattalin arziki ba. Yadda Amurka ta tsananta takaddamar ciniki a tsakaninta da Sin ya raunana moriyar masu sayayyar kasar da kamfanoninta, har ma ya kawo rashin tabbaci ga tattalin arzikin duniya. Sun yi nuni da cewa, a halin yanzu, dole ne kasar Sin ta kara azama kan raya tsarin sana'o'i,ta hanyar yin gyare-gyare kan tattalin arziki.

Gwamnatin Amurka tana gudanar da wani taro na sauraron ra'ayoyin jama'a kan batun kara dora kudin haraji kan kayayyakin da kasar Sin take sayar mata, wadanda darajarsu ta kai misalin dalar Amurka biliyan 300, wanda ya samu kin yarda matuka daga kamfanoninta. A yayin taron bita kan muhimman batutuwan da suka shafi takaddamar ciniki da tattalin arziki a tsakanin Sin da Amurka, wanda kwalejin nazarin tattalin arzikin kasar Sin daga manyan fannoni ya shirya jiya Alhamis, Bi Jiyao, mataimakin shugaban kwalejin yana ganin cewa, zurfafa hadin gwiwa a tsakanin Sin da Amurka ta fuskar tattalin arziki da ciniki ya kawo wa kamfanonin Amurka dammarmaki da yawa, da karfafa sayar da kayayyakin Amurka a Sin, da kara samar da guraben aikin yi, farfado da tattalin arzikin Amurka, da kara kawo wa Amurkawa alheri. Amma kara dora kudin haraji kan kayayyakin Sin zai lahanta moriyar masu sayayyar Amurka da kuma kamfanoninta."Kayayyakin kasar Sin da gwamnatin Amurka ta shirya kara dorawa kudin haraji, su ne kusan dukkan kayayyakin da kasar Sin take sayarwa a Amurka, wato kayayyaki ne da suke shafar zaman rayuwar Amurkawa baki daya, kamar tufafi, takalma, wayar salula, kekuna da dai sauransu. Nan gaba, tabbas farashinsu zai karu. Kusan ba zai yiwu Amurka ta sayi kayayyakin da sauran kasashe suka kera a maimakon kayayyakin kasar Sin ba. A ganina, yanzu kowa ya san haka daga wannan taro na sauraron ra'ayoyin jama'a. Masu sayayya na Amurka ne za su biya karin kudade kan kayayyakin kasar Sin wadanda za a kara dora kudin haraji a kansu. Ma iya cewa, za a kara dora kudin haraji ne kan masu sayayya na Amurka. Don haka mutane da yawa sun ki yarda da haka."

Madam Zang Yueru, shugabar cibiyar nazarin kasuwanni da farashi ta kwalejin nazarin tattalin arzikin kasar Sin daga manyan fannoni ta yi bayani da cewa, watakila takaddamar ciniki da Amurka ta tayar a tsakaninta da Sin ta raunana karfin zuciya kan tattalin arzikin duniya, da tsananta rashin kwanciyar hankali a kasuwannin manyan hajjoji da hada-hadar kudi, da saba wa ka'idojin tafiyar da harkokin kasuwanni a duniya. "Takaddamar ciniki da Amurka ta tayar tsakaninta da Sin ta raunana kwarin gwiwar da ake da shi kan tattalin arzikin duniya. Akwai yiwuwar za ta haifar da koma-bayan tattalin arzikin duniya a karo na 2, tun bayan shekarar 2008."

Har ila yau kuma, Huang Qifan, mataimakin darektan cibiyar yin mu'amalar tattalin arziki tsakanin kasa da kasa ta kasar Sin ya jaddada cewa, sakamakon abkuwar takaddamar ciniki, ya sa kasar Sin ta kara azama kan tsarin sana'o'i ta hanyar yin gyare-gyare kan tattalin arzikinta."Ya kamata mu kara yawan rukunonin tambura cikin tsarin sana'o'inmu, mu kyautata tsare-tsaren da suka taimaka wajen raya tsarin samar da kayayyaki, kana mu inganta haduwar tsarinmu da tsare-tsaren kasa da kasa a fannoni daban daban. Haka zalika kuma, dole ne gwamnatinmu ta kyautata muhallin kasuwanci da kuma rage kudin kashewa. Kamfanoni fa? Kamata ya yi su kyautata karfinsu a fannonin da suka gaza. Ta haka za mu iya tinkarar takaddamar ciniki a halin yanzu."

Mista Huang ya kara da cewa, a ganinsa, kamfanonin Amurka, jama'arta, da masananta masu ilmin tattalin arziki za su yi tunani sosai. Za su sa kaimi kan gwamnatinsu wajen gyara kuskurenta. "Idan Sin da Amurka suka hada hannu sosai, to za su samu alheri, tare da kara azama kan ci gaban tattalin arzikin duniya. Amma idan suka yi takaddama a tsakaninsu, to babu wadda za ta ci nasara, kuma za a haifar da koma baya ga tattalin arzikin duniya. Don haka akwai dalilai masu yawa da za su sa Sin da Amurka su ci gaba da hada kai ta fuskar ciniki. Amma babu wani dalilin da ya sa kasashen 2 za su yi fada da juna."(Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China