Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Takaddamar ciniki tsakanin Amurka da Sin babban koma baya ne ga tattalin arzikin duniya
2019-06-20 08:26:23        cri

Batun takaddamar ciniki da wasu matakan nuna bangaranci da kuma bada kariya kan harkokin ciniki da gwamnatin kasar Amurka ta dauka a kwanan baya da kuma yadda ta tayar da takaddama ta hanyar kara dora kudin haraji kwastam kan kayayyakin da kasar Sin ke fitarwa zuwa Amurka, wasu jami'an kasashen waje da masana tattalin arziki na kasa da kasa suna ganin batun ba zai haifar da mai ido ba ga bangarorin biyu da ma duniya baki daya, wasu da suka halarci taron cudanya da kasashen waje na kwamitin koli na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin sun bayyana cewa, kuskuren da Amurka ta yi ya kawo illa ga ita kanta da kuma kasashen duniya baki daya. A cewarsu babu wanda zai goyi bayan abubuwan da Amurka ta yi.

Bisa kididdigar da ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ta bayar ya nuna cewa, a cikin farko watanni 5 da suka gabata na bana, yawan jarin waje da aka yi amfani da shi a kasar Sin ya kai kimanin kudin RMB yuan biliyan 369, wato ya karu da kaso 6.8%, bisa makamancin lokacin bara. A lokacin da yawan jarin waje da ake zubawa a duk fadin duniya yake raguwa, jarin waje da aka zuba a kasar Sin ya alamta cewa har yanzu kasar Sin kasa ce da aka fi son zuba jari. Ko shakka babu, maganar wai kamfanoni masu jarin waje za su kaura daga kasar Sin sakamakon karin harajin kwastam da ake bugawa ba shi da tushe ko kadan.

Yanzu kasar Sin na kokarin inganta yanayin tattalin arzikinta, ta yadda za ta iya ci gaba da jawo hankulan kamfanoni masu jarin waje da su zuba karin jarinsu a kasarta. Idan an duba jarin waje da aka zuba a kasar Sin a cikin farkon watanni 5 da suka gabata na bana, za a iya ganin a bisa yanayin da ake ciki yanzu, baki 'yan kasuwa na kokarin zuba jari a masana'antun fasahohin zamani na kasar Sin, maimakon hada-hadar wasu kayayyaki kadai. Dalilan da suka sanya kasar Sin ke iya janyo jari daga kasashen waje, sun hada da yadda kasar ta mallaki cikakken tsarin da ya shafi dukkan sana'o'i a cikin gida, da tsarin jigilar kayayyaki cikin sauki, da dimbin kwararru a fannoni daban daban, gami da kwarewa a fannin samar da sabbin fasahohin zamani. Duk wadannan abubuwa sun rage kudin da kamfanonin ketare ke kashewa, gami da taimakawa wajen samar da sabbin fasahohi don raya tattalin arzikin kasar. (Ahmad/Saminu/ Sanusi)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China