Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Afirka ta kasance muhimmin yankin dake hadin gwiwa da kamfanonin saka na kasar Sin
2019-06-17 12:18:33        cri

A halin da ake ciki yanzu ana gudanar da bikin baje kolin kayayyakin saka na kasar Sin karo na hudu a kasar Afirka ta Kudu, inda kamfanonin samar da kayayyakin sakar kasar Sin sama da 150 suke halartar bikin da aka shirya, ana saran za a kara habaka kasuwar kayayyakin sakar kasar Sin a nahiyar Afirka, hakika Afirka ta riga ta kasance muhimmin yankin dake gudanar da hadin gwiwa a bangaren da kamfanonin kasar Sin.

A cikin 'yan shekarun da suka gabata, kamfanonin samar da kayayyakin saka na kasar Sin suna kokarin habaka kasuwarsu a kasashen wajen bisa manufar bude kofa da gwamnatin kasar take aiwatarwa, a don haka babbar kasuwar kasashen Afirka wadda ke samun saurin ci gaba tana kara jawo hankalinsu, gaba daya adadin jarin da kamfanonin sakar kasar Sin suka zuba a Afirka tsakanin shekarar 2015 zuwa ta shekarar 2018 yakai dalar Amurka miliyan 253, kana adadin tufafin da kamfanonin kasar Sin suka fitar dasu zuwa kasashen Afirka a shekarar 2018 ya kai dala biliyan 18 da miliyan 55, hadin gwiwar dake tsakanin Sin da kasashen Afirka yana kara habaka sannu a hankali.

Mataimakin shugaban hadaddiyar kungiyar masana'antun saka ta kasar Sin kuma zaunannen mataimakin shugaban kungiyar sana'ar saka ta hukumar sa kaimi kan ciniki ta kasar Sin Xu Yingxin ya bayyana cewa, a halin da ake ciki yanzu, muhallin zuba jari a kasashen Afirka yana da inganci, saboda kasashen Afirka sun nuna fifiko a fannonin albarkatu masu arziki, da 'yan kwadago masu yawa da manufofin da suka dace, da karfin asirce a bangaren sayayya da sauransu, ana iya cewa, duk wadannan suna jawo hankalin kamfanonin saka domin su kara zuba jari a kasashen, Xu Yingxin yana mai cewa, "Gwamnatocin kasashen Afirka suna aiwatar da manufar nuna goyon baya ga ci gaban sana'ar samar da kayayyakin saka, hakika sana'ar samar da kayayyakin saka tana taka muhimmiyar rawa kan rayuwar al'umma, saboda ba ma kawai tana samar da tufafi gare su bane, har ma tana samar da guraben aikin yi, kana tana taimakawa wajen habaka kasuwar kasa da kasa, tare kuma da samar da kudin musanya, ban da haka kuma sana'ar zata ingiza ci gaban tattalin arziki, duk wadannan sakamako sun fi dacewa da bukatun kasashen Afirka, kamar su Habasha da Masar da Kenya da sauransu, haka zalika, kasashen Afirka suna da yawan 'yan kwadago, da gonaki masu fadi, da arzikin makamashi, haka kuma sun daddale yarjejeniyar cinikayya maras shinge a nahiyar, har sun samu sharudan samun tallafi daga wasu kasashen Turai da kuma Amurka, duk wadannan sun fi jawo hankalin kamfanonin kasar Sin."

A shekarar 2018, an yi nasarar kammala taron kolin Beijing na dandalin hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, taron da ya tabbatar da makomar ci gaban huldar dake tsakanin sassan biyu, tare kuma da aza harsashi mai inganci ga hadin gwiwar dake tsakanin kamfanonin sassan biyu daga dukkan fannoni, misali siyasa da tattalin arziki da al'adu da kuma kwanciyar hankali, Xu Yingxin yana mai cewa, "Tun bayan da aka fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje a nan kasar Sin shekaru 40 da suka gabata, sana'ar saka ta kasar Sin ta riga ta samu ci gaba cikin sauri, har an kafa wani cikakken tsari domin gudanar da sana'ar, a don haka babu shakka cikin sauki ana gudanar da hadin gwiwar dake tsakanin Sin da kasashen Afirka."

A halin yanzu kasar Sin tana gudanar da hadin gwiwar dake tsakaninta da kasashen Afirka a sana'ar samar da kayayyakin saka da kuma sana'ar samar da tufafi, musamman ma a yankunan dake arewaci da gabashi da kuma kudancin nahiyar.

Rukunin Sunshine na lardin Jiangsu na kasar Sin ya riga ya gina wani kamfani a Habasha, inda ake samar da kayayyaki saka da tufafi. Shugaban sashen cinikin waje na kamfanin Gu Yajun ya gaya mana cewa, "Mun kafa yankin masana'antu a Habasha, adadin jarin da muka zuba bisa matakin farko yakai dala miliyan 100, kawo yanzu mun riga mun fara samar da tufafi tun daga watan Mayun da ya gabata, kuma mun yi hayar ma'aikata sama da 700 a kasar ta Habasha, kana mun horas da wasu saura fiye da 100 a kasar Sin domin su bada gudumowa kan aikin saka na kasarsu a nan gaba."

Yanzu masana'antun sakar kasar Sin ya riga ya kafa tsarin sana'ar wanda ya kai sahun gaba a fadin duniya, ana sa ran hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka a bangaren zai taimaka kan ci gaban tattalin arzikinsu, har ma zai taimakawa ci gaban sana'ar sakar kasashen duniya.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China