![]() |
|
2019-06-16 17:03:03 cri |
Har wa yau, a wannan rana, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kuma karbi lambar yabo ta girmamawa, wadda itace lambar yabo mafi daraja a kasar Tajikistan, kuma shugaban kasar Tajik Emomali Rahmon ya mika lambar yabon ga shugaba Xi.
A lokacin bikin wanda aka gudanar a fadar shugaban kasar, Rahmon yayi cikakken bayani game da irin muhimmiyar gudunmowar da shugaba Xi ke bayarwa wajen raya cigaban dangantakar dake tsakanin Sin da Tajikistan, yace a shiye yake ya yi aiki tare da Xi wajen gina kyakkyawar alakar dake tsakanin kasashen biyu domin cimma manyan nasarori.
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China