Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'in Uganda: takaddamar ciniki tsakanin Sin da Amurka zai kawo illa ga Afirka
2019-06-14 14:30:39        cri

Yayin da Nassur Gaddafi, shugaban sashen matasa na jam'iyyar NRMO ta kasar Uganda yake zantawa da wakiliyarmu a kwanakin baya, ya bayyana cewa, muhimmin dalilin da ya haifar da abkuwar takaddamar ciniki tsakanin kasashen Sin da Amurka shi ne, Amurka na daukar ci gaban kasar Sin a matsayin barazana. A ganin malam Gaddafi, takaddamar ciniki tsakanin Sin da Amurka za ta kawo illa ga kasashe masu tasowa, musamman ma kasashen Afirka. Ya kamata Amurka ta nuna sahihancinta, a kokarin warware matsalar ta hanyar tattaunawa.

Nassur Gaddafi ya taba kawo wa kasar Sin ziyara sau da dama, inda ya yada zango a biranen Beijing, Shanghai, Shenzhen, Chengdu da dai sauransu. Dangane da takaddamar ciniki tsakanin Sin da Amurka, yana ganin cewa, kasashen Sin da Amurka sun fi girma a duniya ta fuskar tattalin arziki. Illar da matsalar ciniki da ke tsakaninsu ta kawo wa kasashen duniya ta fi illar da za ta yi musu, musamman ma ga kasashe masu tasowa. Ana damuwa sosai kan cewa, kila takaddamar cinikin za ta kawo illa ga zaman rayuwar 'yan Afirka da kuma wadatar nahiyar. "Fada a tsakanin manyan mutane kan kawo illa ga dukkan mutane. Don haka ina zura ido kan takaddamar ciniki da ke tsakanin Sin da Amurka, wadda za ta kawo illa ga bunkasuwa da wadata a Afirka da ma duk duniya baki daya. Kamata ya yi su koma kan teburin shawarwari."

Ya yi bayani da cewa, muhimmin dalilin da ya sa Amurka ta tayar da takaddamar ciniki a tsakaninta da Sin shi ne, don Amurka na yunkurin hana bunkasuwar Sin. "Sin ta samu saurin ci gaba ainun. Kila Amurka ba za ta so ganin Sin ta fi ta ci gaban tattalin arziki ba. Tana cin zalin Sin. Yawancin kasashen yammacin duniya suna jin tsoron ci gaban Sin. Amma a ganina, zai fi kyau su amince da ci gaban kasar ta Sin. Saboda kasar Sin tana raya kanta ta hanya mai dacewa, kuma tana hada kai da kasashen duniya yadda ya kamata. Tana bude kofarta ga waje."

Kasar Sin ta dauki shekaru da dama a jere tana matsayin abokiyar Afirka mafi girma ta fuskar yin ciniki. Malam Gaddafi ya nuna cewa, Uganda ta gaza wajen raya ababen more rayuwar jama'a, amma kasar Sin tana taimaka wa kasarsa shimfida hanyoyi, gina tashoshin samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da ruwa da sauran ababen more rayuwar jama'a. A ko wace shekara kasar Sin na bai wa Uganda tallafi da yawa, wadanda Uganda ke matukar bukata.

Yayin da malama Gaddafi yake ziyarar kasar Sin, ya taba ziyartar babban zauren kamfanin Huawei da ke birnin Shenzhen. Birnin Shenzhen, wanda ya shahara a fannin kirkire-kirkire, ya burge malam Gaddafi. Dangane da urmunin haramta Huawei da gwamnatin Amurka ta bayar, yana ganin cewa, "Amurka ta saba wa yarjejeniyar ciniki ta kasa da kasa. Kamata ya yi kamfanin Huawei ya gabatar da kara ga hukumar ciniki ta duniya wato WTO. Kamfanin Huawei, babban kamfani ne. Yana sayar da kayayyakinsa a Afirka bisa farashi mai adalci, wadanda suke samun karbuwa sosai. Kamfanin na Huawei ya kafa wani asusu a Uganda domin taimaka wa wata jami'ar kasar yin kirkire-kirkire. Yayin da muke ziyartar babban zaurensa, sun gwada mana wasu kayayyaki masu ban sha'awa, kamar fasahar 5G. Sun kware matuka a fannin fasahar 5G."

Har ila yau Nassur Gaddafi ya ce, ya yi imani da cewa, kasar Sin ba za ta ja da baya ba. Kuma Amurka na bukatar kara nuna sahihanci. Ra'ayin nuna bangaranci yana raunana tattalin arzikin duniya. Ya yi imani da cewa, Sin da Amurka za su yi ciniki yadda ya kamata, amma ana bukatar kasashen 2 su yi kokari tare. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China