Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'an kananan gwamnatocin Amurka: Takaddamar ciniki tsakanin Sin da Amurka ta kawo illa ga fitar da kaya da zuba jari
2019-06-13 13:11:21        cri

Ma'aikatar kasuwancin Amurka ta gudanar da taron koli kan zuba jari na shekarar 2019 mai taken "zabar Amurka" a Washington, babban birnin kasar, inda jami'an kananan gwamnatocin kasar kamar su jihohin Louisiana da Idaho suka bayyana cewa, huldar tattalin arziki da cinikayya dake tsakanin Sin da Amurka wadda ke fama da takaddama tana kawo illa ga jihohinsu a bangaren fitar da kayayyaki zuwa ga kasar Sin, haka kuma ta rage damammakin kansu a bangaren samun jarin da 'yan kasuwan kasar Sin zasu zuba.

Makasudin da yasa ma'aikatar kasuwancin Amurka ta shirya wannan taron koli kan zuba jari na bana a otel din Washington Hilton shine domin kara samun jarin da 'yan kasuwan kasashen waje suke zubawa, a cibiyar baje kolin da aka shirya yayin taron, wakilinmu ya ga jihohin kasar da manyan biranen kasar da hukumomin da abin ya shafa na kasar sun shirya baje kolinsu a cibiyar, inda suka yi cikakken bayani kan muhallin kasuwanci da manufofin da abin ya shafa, tare kuma da amsa tambayoyin da mahalartan taron suka yi musu, hakika a karkashin yanayin da ake ciki yanzu, wato huldar tattalin arziki da cinikayya dake tsakanin Sin da Amurka ta gamu da takaddama, wasu wakilai da suka zo daga kananan gwamnatocin jihohin Amurka sun nuna damuwa kan yanayin da suke ciki a bangaren fitar da kayayyaki zuwa ga kasar Sin, da makomar samun jarin da 'yan kasuwan kasar Sin zasu zuba,

Jami'in sashen raya tattalin arziki na ofishin gwamnan jihar Louisiana Don Pierson ya taba zuwa nan kasar Sin sau tarin yawa domin rangadin aiki, tare kuma da ingiza hadin gwiwar kasuwanci dake tsakanin jihar da kasar Sin, kan batun game da takaddamar cinikayya dake tsakanin Sin da Amurka, yana ganin cewa, kara buga harajin kwastam ba ma kawai ya kawo illa ga jiharsa a bangaren fitar da kayayyaki ga kasar Sin bane, har ma yasa adadin kayayyakin da ake jigilar su a tashar ruwan tekun dake kudancin jihar ya ragu, yana mai cewa, "Jiharmu ta Louisiana tafi maida hankali kan aikin gona, a don haka muna samar da kayayyakin aikin gona da dama misali auduga da wake da masara, cikin dogon lokaci kasar Sin ta kasance babbar kasuwarmu, yanzu an kara buga harajin kwastam, lamarin da ya kawo babbar illa ga manoma da tattalin arzikin aikin gonar jiharmu, kana adadin kayayyakin da ake jigilar su a tashar ruwan tekun dake kudancin jihar ya ragu yanzu, lamarin da ya kawo illa ga jiharmu a bangarorin samun aikin yi da jigilar da kayayyaki da kuma samar da kayayyaki."

Bisa sabbin alkaluman da sashen raya tattalin arziki na ofishin gwamnan jihar Louisiana ya samar, an ce, kasar Sin kasuwa ce mafi girma ta jihar, adadin rarar kudin dake tsakanin jihar da kasar Sin ya kai sama da dala biliyan 6, kana an samu labari daga ma'aikatar sufurin Amurka cewa, tashar ruwan tekun Louisiana dake kudancin jihar tasha ce mafi girma wajen jigilar da kayayyaki a kasar ta Amurka, kasar Sin kuwa tana sahun gaba a fannin cinikayya a tashar.

A cikin cibiyar baje kolin, jami'ar ma'aikatar aikin gona ta gwamnatin jihar Idaho wadda ita ma take mallakar fiffikon aikin gona Laura Johnson ta bayyana cewa, tattalin arzikin jihar yana dogaro ne kan fitar da kayayyaki zuwa ga kasashen waje, amma yanzu manufar cinikayyar da gwamnatin Amurka take aiwatar da ita ta sa manoman kasar suke damuwa matuka, tana mai cewa, "Ana sayar da rabin alkama da kaso daya bisa shida na dankalin Turawa da kaso daya bisa shida na madara da ake samarwa a jihar Idaho zuwa ga kasuwar kasa da kasa, a bayyane take an lura cewa, tattalin aikin jihar yana dogaro ne kan fitar da kayayyaki zuwa ga kasashen waje, a don haka manoman jiharmu suna damuwa matuka kan yanayin da ake ciki yanzu, muna sa ran za a daidaita matsalar cikin hanzari."

Ban da haka, kamfanonin Amurka su ma sun nuna damuwa kan rashin tabbacin manufar kasar, jami'in sashen raya tattalin arziki na ofishin gwamnan jihar Louisiana Don Pierson ya bayyana cewa, "Yanzu an ga kamfanoni sun jinkirta tsaida kuduri kan zuba jari, saboda sun ga an gamu da matsalar rashin tabbacin manufa, amma idan ba a tsaida kuduri kan zuba jari a kan lokaci ba, mai yiwuwa ne yanayin kasuwa zai sauya."

Pierson ya kara da cewa, yanzu ya dace kasashen Sin da Amurka su yi kokari domin samun moriyar juna, ta hanyar gudanar da tattaunawa, ta yadda za a sake samun tabbacin tattalin arziki da kasuwa a sassan biyu.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China