Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin da Birtaniya za su shirya taron tattalin arziki da hada hadar cinikayya domin bunkasa hadin gwiwa
2019-06-12 20:26:43        cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, ya ce mataimakin firaminsitan kasar Sin Hu Chunhua, da shugaban ofishin baitulmalin Birtaniya Philip Hammond, za su jagoranci taron tattalin arziki da hada-hadar cinikayya, domin bunkasa hadin gwiwar kasashen biyu.

Za dai a gudanar da taron karo na 10 ne a ranar 17 ga watan Yunin nan, a gabar da kasashen biyu ke fatan ganin sun dada karfafa hadin gwiwa a fannin cinikayya, da zuba jari, da sauran muhimman batutuwa da suke shafar su. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China