Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ana yaki da masifun fari da ambaliyar ruwa a kasar Sin
2019-06-12 11:11:11        cri

A halin da ake ciki yanzu, yankunan kasar Sin na shiyyoyin kudu zuwa arewa sun riga sun shiga lokacin saukin aukuwar masifar ambaliyar ruwa, a don haka gwamnatin kasar ta bukaci a kara maida hankali kan batun domin rage hadarorin da za a iya fuskanta.

Kasar Sin tana da girman gaske, shi yasa wasu yankunan dake shiyyar kudancin kasar sukan shiga lokacin saurin aukuwar masifar ambaliyar ruwa a watan Maris, amma yankunan dake shiyyar arewancin kasar kuwa sukan shiga lokacin ne a watan Yuni.

Babban sakataren sashen bada umurni kan aikin yaki da masifun fari da ambaliyar ruwa na kasar Sin kuma mataimakin ministan ma'aikatar kula da aikin madatsar ruwa ta kasar Ye Jianchun ya bayyana yayin taron yayata manufar da ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya shirya jiya Talata cewa, bisa hasashen da aka yi kan yanayin ruwan sama, an dauka cewa, yanayin da kasar Sin ke ciki a lokacin saukin aukuwar ambaliyar ruwa bashi da inganci, a don haka akwai matsala a gudanar da aikin yaki da masifun fari da kuma ambaliyar ruwa, yana mai cewa, "Bisa hasashen da aka yi, an ce, yanayin kasar Sin a lokacin saukin aukuwar ambaliyar ruwa bashi da inganci, a takaice dai ana iya cewa, adadin ruwan saman yankunan dake kudancin kasar zaifi na yakunan dake arewacin kasar, kana ambaliyar ruwa ta faru a wasu yankuna da dama a fadin kasar, amma a birnin Beijing da birnin Tianjin da lardin Hebei da lardin Shanxi da yankin tsakiyar jihar Mongolia ta gida, da wasu yankunan dake arewa maso yammacin kasar, kila ne za a iya fuskanatar masifar fari, akwai babbar matsala yayin da ake fama da masifun fari da ambaliyar ruwa a bana."

An samu labari cewa, hukumomin da abin ya shafa na gwamnatin kasar Sin suna gudanar da aikin magancewa da kuma yaki da masifun fari da ambaliyar ruwa yadda ya kamata, a wasu wurare a fadin kasar, an shirya atisaye cikin hadin gwiwa sau tarin yawa, kana an gyara madatsrun ruwa a fadin kasar har da yawansu ya kai sama da dubu 41, ban da haka kuma, babban kamfanin zirga-zirgar jirgin kasa na kasar Sin shima ya tantance layukan dogo, inda suke da saukin gamuwa da aukuwar ambaliyar ruwa har wurare fiye da 1400, haka zalika, sashen kula da aukuwar masifu cikin gaggawa na kasar shima ya ajiye kayayyakin ceto masu yawan gaske domin bada tallafi ga masu bukata yayin fama da masifun, abu mafi muhimanci shine kasar Sin tana kara maida hankali kan aikin horas da masu aikin bada ceto cikin gaggawa, babban sakataren sashen bada umurni kan aikin yaki da masifun fari da ambaliyar ruwa na kasar Sin kuma mataimakin ministan ma'aikatar kula da aikin madatsan ruwa ta kasar Ye Jianchun ya bayyana cewa, "A wasu yankunan da suka fi hadari a fannin aukuwar masifun ambaliyar ruwa, mun tura tawagogin masu aikin bada ceto cikin gaggawa da yawansu ya kai 360, wadanda ke kumshe da masu aikin kusan dubu 140, kana adadin jiragen saman bada ceton da muka shirya ya kai sama da 200, gaba daya adadin masu aikin bada ceton da suke gudanar da ayyukan madatsar ruwa da samar da lantarki da sufuri da sadarwa da sauransu ya zarta miliyan daya da dubu 100."

Jami'in ya jaddada cewa, a halin da ake ciki yanzu, gwamnatin kasar Sin zata kara bada muhimmanci kan aikin magancewa da kuma yaki da masifun ambaliyar ruwa da guguwar iska da zasu faru ta hanyar kimiyya, ta yadda za a daidaita duk matsalolin cikin lumana, yana mai cewa, "Za mu kara himmantuwa kan aikin yaki da manyan masifun ambaliyar ruwa da fari bisa matakai daban daban ta hanyar kimiyya, gwamnatin kasar ta bukaci hukumomin da abin ya shafa su sauke nauyi dake bisa wuyansu, haka kuma, su yi kokarin magance aukuwar masifun, tare da bada ceto akan lokaci idan masifun sun faru."

Bisa alkaluman da aka samu, ya zuwa ranar 10 ga wata, larduna 22 a fadin kasar Sin sun taba gamuwa da ambaliyar ruwa, musamman ma a jihar Guangxi da lardunan Jiangxi da Fujian da Guangdong, adadin mutanen da masifun suka rutsa dasu ya kai miliyan 6 da dubu 750, adadin da ya ragu da kaso 48 cikin dari bisa shekaru biyar da suka gabata.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China