Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kaftin Asamoah Gyan na Ghana ya sauya aniyarsa ta yin murabus bayan tattaunawa da shugaban kasar Ghanan
2019-06-13 15:10:25        cri
Mai horas da 'yan wasan Ghana Asamoah Gyan ya sauya aniyarsa na yin ritaya daga babbar kungiyar wasan kwallon kafan kasar, Black Stars, bayan wata zantawa ta wayar tarho da suka yi da shugaban kasar Ghanan Nana Addo Dankwa Akufo-Addo.

A wata sanarwa da aka a ranar Laraba, Gyan yace bukatar da shugaban kasar ya nema abu ne da ba za'a iya yin watsi dashi ba ya kara da cewa, ya amince da rokon da shugaban kasar yayi masa da kyakkyawar zuciya kuma zai amince ya gabatar da kansa don zama kociyan wanda Kwesi Appiah zai zaba.

"Babban abinda nake buri shine taimakawa Ghana domin kawo karshen fafutukar da kasar ta shafe sama da shekaru 30 tana yi na neman daukar kofin gasar cin kofin Afrika na AFCON har yanzu ina da kwarin gwiwa kuma zan cigaba da jajurcewa domin yiwa wannan babbar kasa aiki da kuma alummar kasar Ghana baki daya," injishi.

Gyan, tsohon dan wasan gaban Shanghai SIPG, ya sanar da yin ritaya ne daga babbar kungiyar wasan kwallon kafa ta maza ta kasar a ranar Litinin kana zai janye jiki daga shiga harkokin wasan AFCON bayan matakin da ya dauka na mika ragamar aikin horas da 'yan wasan ga wani dan wasa na dabam.

Matakin ya zo ne kusan wata guda kafin fara gasar kofin (AFCON) a 2019 a kasar Masar.

To sai dai kuma, shugaba Akufo-Addo a daren ranar Talata ya bukaci dan wasan tsakiyar ya sauya aniyarsa na yin ritayar kuma ya gabatar da kansa don zama kociyan babbar kungiyar wasan kasar, domin biyan muradun kasar.

Ghana tana rukunin F a gasar ta AFCON tare da Kamaru, jamhuriyar Benin, da Guinea Bissau.

Gasar 2019 AFCON, zata gudana ne tsakanin ranar 21 ga watan Yuni zuwa 19 ga watan Yulin. (Amina Xu, Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China