Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'in kungiyar kwallon kafan mata na kasar Sin yana da kyakkyawan tsammani a gasar cin kofin duniya da za'a buga a Faransa
2019-06-13 15:10:21        cri

Jia Xiuquan, mai horas da 'yan wasan kungiyar kwallon kafan mata ta kasar Sin, ya bayyanawa kamfani dillancin labarai na Xinhua cewa kungiyarsa a koda yaushe tana cikin shirin taka rawar gani a gasar cin kofin duniya da za'a gudanar a kasar Faransa.

Tsohon jami'in kungiyar wasan kwallon kafan maza 'yan kasa da shekaru 19 ta kasar Sin mai shekaru 56 a duniya ya nanata cewa basa tsammanin daukar kofi a gasar amma kuma suna da babban mafarki a gasar.

"Hakika, nine na fada cewa burinmu shine mu kai matsayin karshe a gasar cin kofin duniya na mata, sai dai kuma zamu iya samun nasarar da tafi wannan, inda zamu kara matsawa gaba har mu kai ga lashe kofin gasar. Tabbas, ban sauya ra'ayina ba koda an tambayeni. Wannan shine burin da na tsarawa kungiyar wasana," inji kociya Jia.

"Amma dukkannin 'yan kungiyar wasana da ni kaina mun jima muna da kyakkyawan tsammani," injishi.

"Mun san cewa akwai tazara mai girma tsakaninmu da manyan 'yan wasan kwallon kafa mata na duniya, amma muna cigaba da yin aiki tukuru domin cike gibin dake tsakanin manyan kungiyoyin 'yan wasan da mu kanmu."

Jia, bayan ya karbi ragamar aiki daga wajen Sigurdur Ragnar Eyjolfsson a ramar 1 ga watan Yunin shekarar 2018, ya fadawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a lokacin wata tattaunawarsu bayan da kungiyar wasan ta tashi kunnen doki a gasar cin kofin mata da aka gudanar a watan Disambar da ya gabata tsakaninsu da Steel Roses, wanda ta samu matsayin kungiyar wasa ta 5 a nahiyar Asiya kana matsayi na 15 a duniya, mafi karancin matsayi da ake bukata.

Kunnen dokin da kasar Sin ta yi a rukunin daya da manyan kungiyoyinn wasan kwallon kafa na kasashen Jamus da Spaniya, da kuma babbar kungiyar wasan kwallon kafa a Afrika daga kasar Afrika ta kudu, wata alamace dake nuna cewa akwai nasara babba a nan gaba ga Jia da kungiyar wasansa.

Wasan kwallon kafan na mata na 2019 FIFA za a fara shine a ranar 7 ga watan Yuni a Faransa abin alfahari ne ga kungiyar wasan kwallon kafan matan kuma kasar Sin tana burin kafa wani muhimmin tarihi ta hanyar samun babban sakamako.

Jia, daya daga cikin kociyoyi wanda yayi aiki a kungiyoyin wasan kwallon kafan kasar Sin, ya shafe mafi yawan rayuwar aikinsa wajen mayar da hankali don horar da 'yan wasan kwallon kafa maza kafin daga bisani ya karkata zuwa ga kungiyar wasan kwallon kafa mata na kasar.

Ya shafe sama da shekaru 20 yana aiki a kungiyar wasan kwallon kafan maza, Jia ya taba samun lambar yabo na kociya a shekarun 2015 da 2016 saboda aikin da ya gudanar a Henan Jianye a gasar wasannin Super League ta kasar Sin. (Amina Xu,Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China