Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Fa'idar sana'ar hidima ga ci gaban tattalin arzikin duniya
2019-06-13 14:58:38        cri

An bude taron samar da hidimomi na kasa da kasa na kasar Sin na shekarar 2019 a nan birnin Beijing a ranar Talata 28 ga watan Mayun shekarar 2019.

A sakon da shugaba Xi Jinping ya aike wa taron, ya yi nuni da cewa, kokarin raya tattalin arzikin duniya bisa tsarin bai daya, da samar da hidimomi , wani muhimmin bangare ne na harkokin cinikayya tsakanin kasashen duniya gami da hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya a tsakaninsu, wanda ya taimaka matuka ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya.

Manasa na cewa, wannan fanni yana da kyakkyawar makoma, don haka ya kamata a yi amfani da wannan dama don samar da kyakkyawar makoma ta samar da hidima a duniya da samun moriyar juna tare.

Xi Jinping ya jaddada cewa, Sin ta yi kokarin sa kaimi ga bude kofa ga kasashen waje da nuna goyon baya ga tsarin yin ciniki a tsakanin bangarori daban daban. Haka kuma, kasar Sin za ta fadada kasuwar jarin waje da kuma samar da yanayin ciniki mai inganci.

Sin tana son kara zuba jari da yin hadin gwiwa a fannin samar da hidima a tsakaninta da sauran kasashen duniya, da saukaka 'yancin yin ciniki da zuba jari, wanda hakan zai taimaka ga bunkasa tattalin arzikin duniya bisa tsarin bai daya mai salon bude kofa da daidaito da samun moriyar juna.

Masana na ganin cewa, sana'ar samar da hidima ta saukakawa dan-Adam harkokin rayuwa a fannonin daban-daban, kuma dokokin da aka tanada don kare sana'ar suna taka muhimmiyar rawa ga ci gaban tattalin arziki. (Ahmed, Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China