Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta sha alwashin aiwatar da sakamakon dandalin FOCAC na birnin Beijing
2019-06-10 20:46:15        cri
Kakakin ma'aikatar kasuwancin kasar Sin Geng Shuang, ya ce kasar sa ta kuduri aniyar aiwatar da sakamakon da aka samu, daga dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka na FOCAC, wanda ya gudana a birnin Beijing tsakanin ranekun 24 zuwa 25 ga watan Yunin bana.

Geng Shuang ya bayyana hakan ne a Litinin din nan, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa. Ya ce an shirya gudanar da tsaron jami'an tsare tsare, domin fara aiwatar da sakamakon dandalin na FOCAC, ana kuma sa ran jami'ai daga bangaren kasar Sin, da kuma takwarorin su na kasashen Afirka 54 za su halarci taron.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China