Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ana kyautata muhallin tafkin Baiyangdian dake sabon yankin Xiong'an
2019-06-10 12:53:10        cri

Yanzu ana ci gaba da gudanar da aikin gina sabon yankin Xiong'an dake birnin Baoding na lardin Hebei na kasar Sin, nan gaba kuma za a kara bada muhimmanci kan aikin kyautata muhallin tafkin Baiyangdian dake yankin, har an riga an kyautata ingancin ruwa a tafkin.

Tafkin Baiyangdian dake sabon yankin Xiong'an na birnin Baoding na lardin Hebei, tafki ne mafi girma dake sararin kasa na Huabei na kasar Sin, wanda ke kumshe da kananan tafkuna sama da 140, mataimakin shugaban hukumar tsara shirin gina sabon yankin Li Tong ya bayyana cewa, kiyaye muhallin halittu masu rai da marasa rai na tafkin Baiyangdian muhimmin aiki ne yayin da ake gina sabon yankin Xiong'an, yana mai cewa, "Sabon yankin Xiong'an zai kai sahun gaba a duniya a fannin ci gaban birane, a don haka ya dace a yi kokarin kiyaye muhallin halittu masu rai da marasa rai na tafkin Baiyangdian ta hanyar yin amfani da sabuwar kimiyya da fasaha, da haka za a gina wani birnin da zai bada abin koyi ga sauran biranen kasashen duniya, har zai kasance wani birni mai ma'anar musamman a tarihin ci gaban bil Adama."

Sinawan dake yankunan arewacin kasar Sin su kan mayar da tafkin Baiyangdian a matsayin lu'u lu'u dake kan sararin kasa na Huabei na kasar, amma a cikin shekaru sama da goma da suka gabata, tafkin ya taba gamuwa da fari, kana ruwan tafkin shi ma ya taba kazancewa saboda an raya tattalin arzikin yankin ta hanyar da bata dace ba, amma a cikin shekaru biyu da suka gabata, wato tun bayan da aka fara gudanar da aikin gina sabon yankin Xiong'an, an riga an samu babban ci gaba wajen kyautata ingancin ruwan tafkin, mataimakiyar shugabar hukumar kiyaye muhallin halittu masu rai da marasa rai ta sabon yankin Xiong'an Wu Haimei ta bayyana cewa, "Ya zuwa shekarar 2018, adadin sinadaran dake kazantar da yankin kewayen tafkin Baiyangdian kamar su sinadaran phosphorus da ammonia nitrogen sun ragu bisa babban mataki, har sun kai kaso 35.16 bisa dari da kuma kaso 45.45 bisa dari, ana iya cewa, an samu babban ci gaba a fannin kyautata muhallin tafkin."

Kauyen Shaozhuangzi na gundumar Xin'an yana kan tsibirin dake cikin tafkin Baiyangdian, mazaunar kauyen Yang Huimin tana sa rai cewa, tana fatan zasu iya sake shan ruwan da ake diba daga tafkin kai tsaye, ta gaya mana cewa, kafin shekaru 30 da suka gabata, sun taba shan ruwan tafkin kai tsaye, babu kazanta ko kadan a wancan lokaci, amma daga baya ruwan ya yi datti saboda kazantar da aka zuba masa, ba zai yiwu suci gaba da shan ruwan ba. Yanzu gwamnatin gundumar Xin'an tana gudanar da aikin gina manyan gine-ginen tsabtace ruwan sha da datti da bayan gida bisa shirin da aka tsara, jami'i mai kula da aikin na kauyen Shaozhuangzi kuma mataimakin babban manajan kamfanin kimiyya da fasahar tsabtace ruwa na yankin Xiong'an Zhang Te ya jaddada cewa, bisa ma'aunin kolin da aka tsara domin kiyaye muhallin sabon yankin Xiong'an, ana gudanar da aikin tsabtace ruwa a daukacin kauyukan yankin, yana mai cewa, "Kauyen Shaozhuangzi yana bunkasa yawon shakatawa domin samun karin kudin shiga, a don haka adadin ruwan da ake amfani dashi a kowace rana ya yi yawa har ya kai tan 50 zuwa 60, a karshen mako ko kuma lokacin bukukuwa, adadin zai karu har zai kai tan 70 zuwa 80, shi yasa mun kafa na'urar tsabace ruwa tan 80 a kowace rana a kauyen."

A daukacin kauyuka 640 dake gundumomi 3 na sabon yankin Xiong'an, kowace rana adadin dattin da ake zubarwa ya kai tan 1260, yanzu haka ana iya daidaita su akan lokaci., muhallin yankin ya samu kyautatuwa a bayyane.

Yao Zhishen, mai aikin tuka jirgin ruwan yawon bude ido dake cikin ni'imtaccen tafkin Baiyangdian ya gaya mana cewa, bisa zurfafuwar aikin kyautata muhallin tafkin, yanzu ba zasu zubar da ruwan datti cikin tafkin kai tsaye ba, an kuma gyara bayan daki, manoman kauyukan basu kiwon kifi a cikin tafkin, har ba su yin kiwon agwagi a ciki, muhalli mai inganci a tafkin yana kara jawo hankalin masu yawon shakatawa daga wurare daban daban.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China