Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta kashe makudan kudade wajen ba da tallafin samar da gidajen kwana
2019-06-10 10:50:35        cri

Yawan kudaden da gwamnatin kasar Sin ke kashewa wajen ba da tallafin gidajen kwana ya karu a shekarar 2018, a kokarin da gwamnatin ke yi na rage wahalhalun mallakar gidajen kwana da kuma inganta zaman rayuwar al'ummar kasar.

A shekarar da ta gabata, jimillar kudaden da gwamnatin ta kashe wajen bayar da tallafin gidajen kwana ta kai yuan biliyan 737.2 kwatankwacin dala biliyan 107, wato ya karu da kashi 46.4 bisa 100 idan an kwatanta da makamancin lokacin bara, ma'aikatar kudin kasar ne ta sanar cikin wani jawabi ta shafin intanet.

Kudaden sun taimaka wajen yi wa gidaje miliyan 6.26 kwaskwarima a wasu kananan garuruwa da birane, sannan da gyaran wasu gidajen miliyan 1.9 da suka lalace a yankunan karkara, kana kudaden sun taimaka wajen aikin samar da kayayyakin gina wasu gidajen haya na al'umma kimanin 300,000, in ji ma'aikatar.

Ma'aikatar kudin ta sha alwashin ci gaba da sanya ido da kuma samar da kudaden tallafin gina gidajen kwana a shekarar 2019, da kuma aikin zamanantar da rukunin gidajen karkara.

An samu daidaito kan farashin gidaje a shekarar da ta gabata, sakamakon yadda gwamnatin Sin ta dauki matakan daidaita tsarin gidajen kwanan da al'umma ke amfani da su.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China