Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya halarci taron tattaunawar tattalin arzikin duniya a Saint Petersburg
2019-06-08 17:56:55        cri

Jiya Jumma'a 7 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping wanda ke ziyarar aiki a kasar Rasha ya halarci cikakken taron tattauna tattalin arzikin duniya karo na 23 da aka gudanar a birnin Saint Petersburg na Rasha, inda ya yi nuni da cewa, samun dauwamammen ci gaba shi ne dabara mafi dacewa da za'a iya amfani da ita a kokarin dakile matsalar da kasashen duniya ke fuskantar a halin da ake ciki yanzu, kasarsa tana son ci gaba da yin kokari tare da sauran kasashen duniya domin kyautata tsarin harkokin duniya, ta yadda za a ingiza kwanciyar hankali a fadin duniya, tare kuma da samar da duniya mai wadata.

Babban taken taron tattaunawa kan tattalin arzikin duniya karo na 23 da aka gudana a Saint Petersburg na Rasha shi ne "Tsara ajandar samun dauwamammen ci gaba".

A cikin jawabin da ya gabatar a gun taron, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, babban taken taron ya dace da yanayin da kasashen duniya ke ciki a yanzu, a don haka yana da babbar ma'ana, yana mai cewa,"A halin da ake ciki yanzu, yanayin duniya yana samun manyan sauye-sauyen da ba a taba ganin irinsu ba a cikin shekaru dari daya da suka gabata, kana kasashe masu saurin ci gaban tattalin arziki da kasashe masu tasowa suna samun bunkasuwa cikin saurin gaske, banda haka yuyin juya halin kimiyya da fasaha da sauye-sauyen sana'o'in da suka faru yanzu sun kawowa kasa da kasa gogayya mai tsanani, a karkashin irin wannan yanayi, tsarin tafiyar da harkokin duniya ba zai dace da sauye-sauyen yanayin duniya ba, a don haka ya dace kasa da kasa su yi kokari tare domin dakile matsalar, tare kuma da samun moriyar juna ta hanyar gudanar da hadin gwiwar dake tsakaninsu, a takaice dai ana iya cewa, samun dawwamammen cigaba zai samarwa kasashen duniya damammakin raya tattalin arzikinsu."

Shugaba Xi ya nuna cewa, ajandar samun dawwamammen cigaba nan da shekarar 2030 ta MDD tafi maida hankali kan batutuwa guda uku wato karuwar tattalin arziki da bunkasuwar zaman takewar al'umma da kuma kiyaye muhalli, batutuwan da zasu kawowa al'ummomin duniya makoma mai haske, bisa matsayinta na kasa mai tasowa mafi girma a duniya, har kullum kasar Sin ta nace ga cika alkawarin da ta dauka, a fannin kara karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa domin samun dauwamammen ci gaba, yana mai cewa,"Na gabatar da shawarar ziri daya da hanya daya a shekarar 2013, shawarar da take da buri iri daya da ta ajandar samun dauwamammen ci gaba nan da shekarar 2030 ta MDD, ya zuwa watan Aflilun bana, an shirya taron kolin dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa bisa shawarar ziri daya da hanya daya karo na 2 a birnin Beijing cikin nasara, inda sassa daban daban suka amince cewa, zasu nace ga maradun bude kofa da kiyaye muhalli da hana cin hanci da rashawa domin cimma burin kyautata rayuwar jama'a tare kuma da samun dauwamammen ci gaba bisa tushen tattaunawar juna da moriyar juna, kana za a hada shawarar ziri daya da hanya daya da ajandar MDD waje guda, ta yadda za a daidaita huldar dake tsakanin tattalin arziki da zamantakewar al'umma da kuma muhalli cikin lumana, a karshe za a cimma burin samun dauwamammen cigaba a fadin duniya."

Shugaba Xi ya kara da cewa, burin samun dauwamammen ci gaba buri ne na yawancin kasashen duniya, ba zai yiwu ba a hana yunkurin, kasar Sin tana son yin kokari tare da sauran kasashen duniya domin daukan hakikanan matakai tare dasu, ta yadda za a cimma burin samun dauwammamen ci gaba, yana mai cewa,"Zamu cigaba da nacewa ga manufar tattaunawa tare da ginawa tare da kuma samun moriya tare, domin gina tattalin arzikin duniya da zai dace da yanayin daukacin kasashen duniya, kana zamu kara maida hankali kan moriyar al'ummomin kasashen duniya domin samar da alheri gare su, a don haka ya dace mu nace ga manufar raya tattalin arziki bisa tushen kiyaye muhalli, tare kuma da tabbatar da zaman jituwa dake tsakanin bil Adama da hallitu masu rai da marasa rai."

Shugaba Xi ya sake jaddada cewa, kasar Sin zata kara bude kofa ga kasashen waje, tare kuma da kara bude kasuwarta ga kamfanonin ketare, ta yadda zata samar da muhallin kasuwa mai inganci gare su, yana mai cewa,"Zamu ci gaba da sanya kokari domin ingiza cudanyar tattalin arzikin duniya, tare kuma da kiyaye tsarin gudanar da harkokin cinikayya dake tsakanin bangarori daban daban, da daidaita matsalar rashin daidaiton cigaban tattalin arzikin duniya, tana son gudanar da hadin gwiwar cinikayya dake tsakaninta da sauran kasashen duniya bisa tushen daidai wa daida da martabar juna, ta yadda za a cimma burin samun moirya tare, kana muna fatan za a cimma burin samun dauwamammen ci gaba ta hanyar aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya tare kuma aiwatar da ajandar samun dauwamammen ci gaba nan da shekarar 2030 ta MDD, ban da haka kasar Sin tana fatan za a samar da karin damammaki ga kasashe masu tasowa ta hanyar kafa asusun samar da tallafi ga hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa da asusun shimfida zaman lafiya da tabbatar da zaman lafiya na kasar Sin da MDD. Haka zalika kasar Sin tana son amfanin sabbin sakamakon kimiyya da fasaha dake kumshe da fasahar 5G tare da sauran kasashen duniya, ta yadda za a gudanar da gogayya mai inganci tsakanin kasa da kasa tare kuma kyautata tsarin karuwar tattalin arzikin duniya yadda ya kamata."

Shugaba Xi ya ci gaba da cewa, kasar Sin tana fatan kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da sauran kasashen duniya a bangarorin yaki da talauci da samar da tabbaci ga zamantakewar rayuwar al'umma domin kawo alheri ga daukacin al'ummomin kasashen duniya baki daya.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China