Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya aike da sakon murnar muhimmin aikin da ake yi domin "Ranar Muhalli" ta shekarar 2019
2019-06-05 14:19:04        cri

A yau Laraba, an kaddamar da wani muhimmin aiki a birnin Hangzhou na lardin Zhejiang dake gabashin kasar Sin domin murnar "Ranar Muhalli" ta shekarar 2019 a duk fadin duniya. Sakamakon haka, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da wani sakon murnar kaddamar da aikin.

A cikin sakonsa, shugaba Xi ya nuna cewa, duniya daya tak bil Adama ke da ita, kare muhalli da yanayin duniya, da kuma neman dauwamammen ci gaba, babban nauyi ne dake bisa wuyan kowace kasa. Ya ce yanzu, kasashen duniya na kokarin cimma burin da aka kafa a cikin ajandar neman dauwamamen ci gaba nan da shekarar 2030. Amma a waje daya, kowace kasa na fuskantar kalubalolin gurbata muhalli da sauyin yanayi da raguwar tsirrai da sauran matsaloli masu tsanani. Shugaban ya ce, idan ana son bunkasa duniya mai tsabta, ya kamata dukkan kasashen duniya su yi aiki tare wajen neman dauwamammen ci gaba maras gurbata muhalli.

Sannan shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, kasar Sin na mai da hankali sosai wajen kare muhalli. Yanzu a ganin gwamnatin kasar Sin, duwatsu masu cike da bishiyoyi sun kasance kamar duwatsun zinari ko azurfa. Tana mai fatan bil Adama da halittu za su kasance tare cikin lumana. (Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China