Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hotunan ganawar Xi Jinping da Putin
2019-06-04 11:29:23        cri

Gobe Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai fara ziyarar aiki a kasar Rasha, ziyarar da ta zama irinta ta farko bayan da Xi ya sake zama shugaban kasar ta Sin, wadda ta jawo hankalin mutane sosai.

Xi Jinping ya ce alakar dake tsakaninsa da Vladimir Putin alaka ce ta abokan arziki kuma ta kut da kut, shi kuma Putin ya ce Xi amininsa na arziki.

A shekaru shida da suka wuce, Xi da Putin sun gana da juna har sau 28, abun da ya shaida irin kyakkyawar dangantakar dake tsakanin Sin da Rasha, da kuma muhimmancin raya ta a ajandar diflomasiyyarsu.

Bayan da Xi Jinping ya zama shugaban kasar Sin a watan Maris din shekara ta 2013, Putin ya zama shugaban kasa na farko da ya zanta da Xi ta wayar tarho, kana kasarsa wato Rasha ta zama kasa ta farko da Xi ziyarta.

1  2  3  4  5  6  7  8  9  10  

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China