Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ba zata yi rangwame kan muhimman ka'idojin dake shafar ikon mulkin kasar ba
2019-06-03 14:06:45        cri

A jiya Lahadi, gwamnatin kasar Sin ta fitar da takardar bayani, mai taken "Matsayin kasar Sin kan shawarwarin da ake yi tsakaninta da Amurka kan batun takaddamar cinikayya". A cikin takardar, an bayyana muhimman bayanai kan yadda aka yi shawarwari kan batun takaddamar cinikayya tsakanin kasashen Sin da Amurka, sannan an bayyana matsayin da kasar Sin ke dauka kan shawarwarin. A cikin takardar, an kuma bayyana yadda bangaren Amurka ya yi watsi da alkawurran da ta taba dauka har sau uku. Bangaren Sin ya nuna cewa, hadin gwiwa ita ce hanya daya tilo da zata daidai bangarorin biyu. Kasar Sin tana son daidaita ra'ayoyi mabambanta da takaddamar cinikayya dake kasancewa tsakanin kasashen biyu ta hanyar yin hadin gwiwa, ta yadda za a iya kulla wata yarjejeniyar moriyar juna da bangarorin biyu dukkansu zasu iya samun nasara. Amma dole ne a yi hadin gwiwa da kuma yin shawarwari bisa ka'ida. A kan muhimman ka'idoji, kasar Sin ba zata yi rangwame ko kadan ba.

Wannan ne karo na biyu da gwamnatin kasar Sin ta fitar da irin wannan takardar bayani game da takaddamar cinikayya da ake yi tsakanin Sin da Amurka bayan ta fitar da irin wannan takarda a watan Satumbar shekarar bara.

A cikin takardar da aka fitar jiya, an nuna cewa, matakan kara buga harajin kwastam da kasar Amurka ta dauka ba kawai sun kawo barzana ga bangaren Sin bane, bangaren Amurka ma bai samu kyakkyawar moriya ba ko kadan. Ya zuwa karshen watan Afrilu, yawan kayayyakin kasar Sin da aka fitar dasu zuwa kasar Amurka ya ragu a cikin jerin watanni biyar da suka gabata. Sannan yawan kayayyakin Amurka da aka shigar dasu kasar Sin ya ragu cikin watanni 8 da suka gabata. A waje guda kuma, wannan yakin cinikayya bai sa kasar Amurka ta "Sake Farfadowa" ba. A yayin taron manema labaru da aka shirya jiya da safe, Mr. Wang Shouwen, mataimakin minista, kana mataimakin wakilin yin shawarwari kan batutuwan cinikayya na ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ya fitar da wasu alkulamai, yana mai cewa, "A hakika dai, bisa kididdigar da bangaren Amurka ta bayar, an ce, gibin kudin cinikayyar kaya da bangaren Amurka ya samu ya karu da 10.4%, yawan wake da aka fitar dasu daga kasar Amurka zuwa kasar Sin ya ragu da 50%, sannan yawan motocin da aka fitar daga Amurka zuwa kasar Sin ya ragu fiye da 20%. An gano cewa, matakan kayyade yin cinikayya sun kawo illa ga moriyar kwadago da manoma na Amurka. Amurkawa ne suke biyan kusan dukkan harajin kwastam da gwamnatin Amurka ta kara bugawa. Bugu da kari, bisa sakamakon da wata hukumar nazarin cinikayya ta Amurka ta bayar, an ce, idan kasar Amurka ta ci gaba da buga karin harajin kwastam kan kayayyakin kasar Sin da ake shigar dasu kasar Amurka, yawan guraben aikin yi da zasu bace a kasar Amurka zai kai miliyan 2 da dubu 230."

A cikin takardar, an kuma bayyana cewa, bayan da bangaren Amurka ya tayar da takaddamar cinikayya tsakaninta da kasar Sin, an kawo illa sosai ga cinikayya da zuba jari da ake yi tsakanin kasashen biyu. Sakamakon haka, bangarorin biyu dukkansu suna ganin cewa, ya zama wajibi da bangarorin biyu suka yi shawarwari domin kokarin daidaita matsalolin da ke kasancewa tsakaninsu. A yayin shawarwari sau da dama da aka yi, kasashen biyu sun cimma matsaya daya kan galibin matsaloli, amma an kuma samu tangarda sau da dama. A cikin wannan takardar da gwamnatin kasar Sin ta fitar, an ce, har sau uku, bangaren Amurka ya musunta alkawuran da ya taba dauka. Mr. Wang Shouwen yana mai cewa, "Dalilin da yasa aka kawo cikas ga shawarwarin shine, da farko dai, bangaren Amurka ya kara buga karin harajin kwastam kan kayayyakin da darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 200, kuma ake shigar dasu kasar Amurka daga kasar Sin daga 10% zuwa 25%, sannan ya kaddamar da ajandar buga karin harajin kwastam kan sauran kayayyakin da darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 300, kuma za a shigar dasu kasar Amurka daga kasar Sin. Bugu da kari, bisa dalilinta na tsaron kai, kasar Amurka ta sanya wasu kamfanonin kasar Sin a kan takardar kayyade sayar musu da kayayyaki."

A cikin takardar, gwamnatin kasar Sin ta nanata cewa, a kullum kasar Sin ta dauki matsayin zama daidai wa daida, da moriyar juna da kuma amincewa da juna a yayin shawarwarin. A jiya, Wang Shouwen ya sake nanata cewa, idan ana son sanya matsin lamba mafi tsanani kan kasar Sin domin tilasta kasar Sin da ta bada kai, wannan ba zai yiyu ko kadan ba. Wang Shouwen ya nanata cewa, "Bangaren Sin ya nanata cewa, dole ne a bi ka'idojin mutunta juna da, zama daidai wa daida, da samun moriyar juna. Mutunta juna dole ne a mutunta ikon mulkin kasa da moriya mafi muhimmanci na kowane bangare."

A cikin takardar, gwamnatin kasar Sin ta jaddada cewa, a kan shawarwarin da ake yi tsakaninta da Amurka kan takaddamar cinikayya, a kullum bangaren Sin ya yi hangen nesa maimakon yin waiwaya. Daga karshe ana bukatar yin shawarwari wajen daidaita takaddamar cinikayya tsakanin bangarorin biyu. Idan Sin da Amurka zasu iya kulla wata yarjejeniyar moriyar juna, zata yi daidai da moriyar kasashen Sin da Amurka, har ma ga duk duniya baki daya. (Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China