Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan kamfanoni masu jarin waje dake birnin Beijing ya wuce dubu 43
2019-06-03 10:47:41        cri
A gun taron bajen kolin ba da hidimar cinikayya na kasa da kasa na shekarar 2019 da aka shirya a ranar 1 ga wata a nan kasar Sin, an kaddamar da rahoton cigaban kamfanoni masu jarin waje na Beijing na shekarar 2019. Inda rahoton ya nuna cewa, ya zuwa shekarar 2018, an kafa kamfanoni masu jarin waje sama da dubu 43 da suka fito daga kasashe da yankuna 165 na duniya a birnin Beijing, yayin da jimillar jarin wajen da aka zuba ya wuce dalar Amurka biliyan 155.

An ce, hada-hadar kudi, hidimar sadarwa, hidimar kimiyya da fasaha sun kasance muhimman bangarorin dake ciyar da bunkasuwar tattalin arzikin Beijing gaba, musamman ma bayan birnin ya kara bude kofa a fannin ayyukan ba da hidima, hakan ya kara kyautata yanayin kasuwar birnin.

Sannan rahoton ya nuna cewa, birnin Beijing dandali ne da kasar Sin ke amfani da shi wajen mu'amala da kasa da kasa. Ya zuwa shekarar 2018, akwai kasashe da shiyyoyi guda 231 da suke mu'amalar cinikayya da birnin Beijing, yayin da kungiyoyin kasa da kasa guda 8 dake aiki a tsakanin gwamnatoci suka kafa helkwatarsu a Beijing. Kana, an samu hukumomin kasashen waje na dindindin dake nan birnin Beijing da yawansu ya kai kimanin dubu 35, tare kuma da helkwatar shiyya-shiyya da cibiyoyin nazari sama da 4000. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China