Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin Ta Fara Binciken Kamfanin Aike Da Sako Na FedEx
2019-06-01 21:14:19        cri

Duba da yadda kamfanin aike da sako na FedEx na kasar Amurka ya yi babban kuskuren tura sakwannin kamfanin Huawei ba bisa adireshi da suna yadda ya kamata ba, hukumomin kasar Sin sun sanar da cewa, za su fara gudanar da bincike kan wannan batu saboda kamfanin FedEx ya keta hakkokin mai aika da sakon da karya dokar kasar Sin ta fannin aikewa da sako.

Tuni a ranar 24 ga watan Mayu, kamfanin FedEx ya aike da wasu kayan kamfanin Huawei guda biyu zuwa Amurka, wadanda da ma kamfanin ya shirya aikewa da su daga Japan zuwa kasar Sin, har ma FedEx ya yi kokarin aikewa da sauran wasu kayan Huawei guda biyu zuwa Amurka wadanda aka shirya aikewa da su daga kasar Vietnam zuwa ofisoshin Huawei dake sauran wasu kasashen Asiya. Duk da cewa kamfanin FedEx ya nemi gafara bayan aukuwar lamarin, amma ya tsaya da cewa kuskure ne wannan, ba tare da sa hannun wata kasa ba. Amma tun bayan da kasar Amurka ta sanya kamfanin Huawei a cikin jerin kamfanonin da aka takaita shigar da kayansa, FedEx, a matsayinsa na abokin hadin-gwiwar Huawei, ba sau daya ba kuma ba sau biyu ba ya yi haka, wato aikewa da sako zuwa wuraren da bai kamata ba, shin wannan kuskure ne kuwa?

Bisa dokokin sana'ar kai sakonni na kasar Sin, kamata ya yi kamfanoni masu kai sakonni su tabbatar da 'yancin masu aikewa da sakonni, kuma kada su yi kuskuren aikawa wani wuri, ko boye shi ko bude sakonni ba tare da samun amincewa ba, ko kuma kai sakonni hannun wadanda bai dace ba. Don haka, Hukumomin da abun ya shafa na kasar Sin sun yi fadi tashi da kamfanin FedEx, tare kuma da soma bincike kansa.

A matsayinsa na kamfani mai kai sakonni da ke gudanar da ayyuka har shekaru sama da goma a kasar Sin, kamfanin FedEx na da nauyin ba da hadin kai ga hukomomin da batun ya shafa na kasar Sin kan binciken, kana hukumomin da batun ya shafa na kasar Sin suna da ikon yanke masa hukunci bisa sakamakon bincike. Ya kamata a kiyaye halaccin iko da moriya na dukkan kamfanoni da jama'a wajen samun hidimar kai sakonni bisa doka.

kawo yanzu, kasar Sin ta fitar da tsarin jerin sassan da ke da rauni ta fuskar cinikayya, kuma bisa dokokin kasar Sin, za a dauki matakan da suka wajaba kan sassan da aka sanya su cikin jerin. Yadda ake gudanar da bincike kan kamfanin FedEx ya zama kashedi ga kamfanonin waje da ma kungiyoyi da daidaikun mutane da suka karya dokokin kasar Sin.

Kasar Sin na da babbar kasuwa da ke iya fitar da riba mai tsoka, kuma tana maraba da kamfanoni kasashen waje su zo su zuba jari, amma da sharadi, wato ya zama tilas su martaba dokokin kasar da kuma ka'idojin kasuwa da yarjejeniyoyin kwagila, kuma ba za su iya katse samar da kayayyaki ga kamfanonin kasar Sin domin wasu dalilai da ba na cinikayya ba, sannan ba za su iya lalata halaltacciyar moriyar masu sayayya na kasar ba. Ta hakan ne kuma za su samu damar bunkasuwa a kasar ta Sin.(Masu fassara:Murtala, Bilkisu, Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China