Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Nijeriya na da muhimmanci sosai wajen raya shawarar "Ziri daya da hanya daya" a Afrika
2019-05-30 14:36:27        cri

Nijeriya kasa ce dake da yawan mutane da tattalin arziki mafi girma a Afrika, shawarar "Ziri daya da hanya daya" da Sin ta gabatar, na dacewa da tsarin kasar na ingiza tattalin arziki, a sanadin hakan, gwamnati da jama'ar kasar na matukar maraba da wannan shawara, haka kuma, Nijeriya na kan matsayin kasa mai muhimmanci wajen raya wannan shawara a nahiyar Afrika.

Ya zuwa yanzu, ana hadin kai sosai karkashin shawarar "Ziri daya da hanya daya", Sin da Nijeriya na samun ci gaba mai armashi a fannin ababen more rayuwa da karfin samar da kayayyaki. Alal misali, an fara amfani da dogon layi na zamani tsakanin Abuja da Kaduna daga watan Yuli na shekarar 2016, wanda ke kan matsayin layin dogon farko a Afrika dake amfani da kimiyya da ma'aunin kasar Sin, kuma ga jirgin kasa mai tafiya a cikin birnin Abuja, wanda aka fara yin amfani da shi daga watan Yuli na shekarar 2018, da kuma sabon babban gini dake cikin filin jiragen sama na Abuja a karshen shekarar 2018, har ma ana kokarin gina tashar ruwa mafi girma a yammacin Afirka a Lekki, da kuma tashar samar da wutar lantarki ta karfin ruwa ta Zungeru, kana da layin dogo tsakanin Lagos da Ibadan, har ma da hanyar mota dake tsakanin Abuja da Keffi da Makurdi da dai sauransu.

Mambar jam'iyyar APC mai mulki a kasar, kuma shugaban taron hadin kan Beijing da Abuja Mista Sam Nda-Isaiah ya nuna cewa, wannan shawara dai ta kasance mataki da ba a taba gani ba, wadda ta hada kasar Sin da dukkanin duniya gaba daya da kawo moriyar juna, ya ce:

"Shugaba Xi ya gabatar da wannan shawara, tsari ne dake shafar kasashe fiye da 150 a fannonin raya manyan ababen more rayuwa da zuba jari a duk fadin duniya, wadda kuma za ta sa kaimi ga tuntubar al'ummomi daban-daban a duniya, da amfanar jama'ar duniya har kaso 65 cikin dari."

A shekarun baya baya nan, Nijeriya na kan matsayin farko a Afrika dake da kwangiloli mafi yawa ta fuskar gine-gine, kuma tana kan matsayi na biyu a Afrika da Sin ke shigar da kayayyaki, kana tana matsayi na uku a Afrika ta fuskar cinikayya da muhimmiyar kasa da Sin take zuba jari a kai. Yawan kudi da ya shafi ciniki tsakanin bangarorin biyu a shekarar bara ya kai dala biliyan 15.3, adadin da ya karu da kashi 10.8 cikin dari, idan an kwatanta da na makamancin lokaci na shekarar 2017.

Ban da wannan kuma, yankin ciniki cikin 'yanci na Ogun-Guangdong da na Lekki na bunkasa yadda ya kamata. Matakin da ya samar da kayayyaki a Nijeriya dake hadin kai da kasar Sin na sa kaimi ga bunkasuwar masana'antu a Nijeriya. Shugaban kwamitin raya dangantakar Sin da Nijeriya na majalisar wakilai ta Nijeriya Yusuf Buba Yakub, ya bayyana matsayinsa kan wannan shawara cewa:

"Wannan shawara wani muhimmin mataki ne na ingiza raya tattalin arzikin duniya bai daya, da kyautata tsarin gudanar da harkokin duniya, wadda kuma ta mai da hankali sosai kan gudanar da ayyuka daban daban yadda ya kamata. Ban da wannan kuma, shawarar tana kokarin daidaita rikicin rashin daidaito tsakanin kasashe masu wadata da kasashe masu tasowa. Nijeriya kuma na da makoma mai haske ta fuskar kawar da talauci, da rashin aikin yi, saboda ganin ta shiga dandalin koli na tattaunawar hadin kan kasa da kasa karkashin wannan shawara."

Tuntubar jama'a na kasancewa wani babban tushe na wannan shawara, yanzu kuma, Sin da Nijeriya na kara hadin kansu a fannoni kimiyya da fasaha, ba da ilmi, al'adu, wasannin motsa jiki, kiwon lafiya da dai sauransu, wanda ya samar da tubali mai inganci ga raya wannan shawara tsakaninsu tare.

Shugaban kungiyar daliban dake karo ilmi a kasar Sin ta Nijeriya Muhammad Sulaiman ya ce, wannan shawara ta amfani kowa da kowa, wadda ke da burin sa kaimi ga kasashe da shawarar ke shafa da su kara hadin kansu. Ya ce:

"Muradun wannan babbar shawarar shi ne hada al'adu da al'umomi daban-daban waje guda, da dunkule nahiyoyi daban-daban, ta yadda za a habaka ciniki, da sa kaimi ga bunkasuwar tattalin raziki. Muna maraba sosai da ita, saboda muna imani da cewa, za ta sa kaimi ga bunkasuwar dankon zumuncin tsakanin kasashen biyu cikin dogon lokaci. " (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China