Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sama da baki 1,300 daga Afrika za su halarci bikin baje kolin ciniki na Sin da Afrika karo na farko
2019-05-30 10:23:45        cri

Ya zuwa ranar 24 ga watan Mayu, adadin baki 1,388 wadanda suka hada da 'yan kasuwa daga kasashen Afrika 52 ne suka rattaba hannu don nuna sha'awarsu na halarci bikin baje kolin ciniki da tattalin arziki na Sin da Afrika a karo na farko, kwamitin tsare-tsaren bikin ya sanar da hakan a Talata.

Za'a gudanar da bikin ne tsakanin ranakun 27-29 ga watan Yuni a birnin Changsha, helkwatar mulki ta lardin Hunan ta kasar Sin, inda za'a gudanar da muhimman taruka, da dandali, da kuma nune-nune, kawo yanzu bikin ya ja hankalin wasu ayyukan hadin gwiwa kimanin 233, wadanda aka kiyasta kudinsu kusan dala biliyan 74.7.

An tanadi cibiyoyin nune-nune kimanin 6 wadanda fadinsu ya kai mita 43,000, wanda ya kushi manyan runfunan taro na kasa da wuraren nune-nune, domin kamfanoni su samu damar baje hajojinsu don samar da damammaki na hadin gwiwar ciniki da tattalin arziki na Sin da Afrika.

Za'a gabatar da wani tsarin baje koli ta shafin intanet da samar da babban dakin nune-nunen kayayyakin Afrika masu inganci na dogon lokaci.

Kaddamar da shirin karkashin dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika, bikin baje kolin zai samar da wasu sabbin manufofin bunkasa hadin gwiwar ciniki da tattalin arziki tsakanin kasashen Sin da Afrika. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China