Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Li Zhanshu ya gana da Mahamadou Issoufou
2019-05-29 19:57:29        cri
Yau Laraba, shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Li Zhanshu ya gana da shugaban Jamhuriyar Nijar Mahamadou Issoufou.

Li Zhanshu ya bayyana cewa, kasar Sin da kasashen Afirka suna da tarihi iri daya na samun 'yancin kai daga Turawan mulkin mallaka, kuma suna fuskantar babban aiki na saukaka fatara da rashin ci gaba gami da namen bunkasuwa.

Akwai wasu abubuwan da kasashen yammacin duniya ba su so su yi, amma kasar Sin da kasashen Afirka sun yi cikin hadin-gwiwa, kana ba tare da gindaya wani sharadin siyasa ba, al'amarin da ya bude wani sabon salo na inganta hadin-gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa. Majalisar wakilan jama'ar kasar Sin na matukar son karfafa mu'amala da majalisar dokokin Nijar, domin ci gaba da zurfafa hadin-gwiwasu.

A nasa bangare, Mahamadou Issoufou ya ce, kasarsa tana godewa kasar Sin saboda goyon-baya da taimakon da ta dade tana ba ta, inda ya ce, Nijar na fatan yin koyi da kasar Sin, da shiga cikin ayyukan shawarar "ziri daya da hanya daya", domin karfafa hadin-gwiwa a tsakaninsu daga dukkan fannoni.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China