Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na daukar batun yanayin jin kai a Syria da muhimmanci
2019-05-29 09:20:01        cri

Jakadan kasar Sin na din-din-din a MDD Ma Zhaoxu, ya ce kasar Sin na daukar batun yanayin jin kai a Syria da muhimmanci sosai, yana mai bukatar al'ummomin kasa da kasa su lalubo mafita ga matsalar.

Ma Zhoxu ya shaidawa kwamitin sulhu na MDD a jiya cewa, kasar Sin na daukar matsalar jin kai a Syria da muhimmanci, kuma tana mara baya ga namijin kokarin da MDD da sauran masu ruwa da tsaki ke yi na inganta yanayin.

Da yake alakanta matsalar Idlib da 'yan ta'addan da suka kwace iko da yankin, jakadan ya ce ya kamata a daidaita dabarun yaki da dukkan kungiyoyin 'yan ta'adda da kwamitin sulhu ya zayyana.

Ya ce, ba take hakkin fararen hula da masu aikin agaji kadai 'yan ta'addan yankin ke yi ba, har ma da kai hari a kai a kai, kan sansanonin sojin Rasha da yankunan da gwamnatin Syria ke rike da su, inda suke barazana ga tsaro da zaman lafiya a yankin da ma kasar.

Ma Zhaoxu, ya ce idan ba a kawar da barazanar 'yan ta'adda daga Idlib ba, al'ummar Syria ba za su samu zaman lafiya ba, haka zalika ba za a shawo kan matsalolin jin kai da al'ummar Idlib ke fuskanta ba. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China