Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bude babban taron UN-Habitat karo na farko a Nairobi
2019-05-28 13:51:46        cri

An bude babban taron hukumar kula da tsugunar da jama'a da raya birane ta MDD (UN-Habitat), karo na farko, kan muhallin halittu, a birnin Nairobin kasar Kenya a jiya Litinin. Babban taken taron shi ne kirkire-kirkire na kyautata rayuwar mazauna birane.

Taron wanda aka bude a jiya, ya samu mahalarta sama da 3,000 daga kasashe da yankuna 113 na duniya. Cikin jawabin da ya gabatar ta hoton bidiyo yayin bikin bude taron, babban sakataren MDD, António Guterres, ya ce, makasudin bude babban taron UN-Habitat karo na farko shi ne, tattauna dabarun inganta rayuwar al'umma mazauna birane.

Babbar daraktar hukumar UN-Habitat mai lura da muhallin halittu kuma mataimakiyar babban sakataren MDD, Maimunah Mohd Sharif ta bayyana a yayin bikin bude taron cewa, dalilin da ya sa aka bude babban taron shi ne, musayar ra'ayi tsakanin kasashen duniya, la'akari da cewa, da yawa daga cikinsu na tsayawa da kuma cika alkawarinsu dangane da ra'ayin kasancewar sassa daban daban a duniya da kuma raya birane ta hanyoyi masu dorewa. Ta ce yanzu ana inganta karfin raya birane a duniya, kuma yayin babban taron, za a tattauna kalubalen da ake fuskanta wajen raya birane, tare da fito da dabarun daidaita wadannan batutuwa ta hanyar yin kirkire-kirkire, a kokarin kara azama kan samun ci gaba mai dorewa. Inda ta ce, "Nan da shekarar 2050, kaso 70 bisa dari na al'ummun duniya za su rika rayuwa ne a birane, wanda hakan ka iya haifar da sabbin kalubale ga wasu kasashe cikin dogon lokaci, kamar kangin talauci, rashin daidaito ta fuskar tattalin arziki, matsalar jin kai, gurbatar iska, sauyin yanayi, rashin samun aikin yi, wadanda suke kara karuwa a birane. Dole ne mu ba da muhimmanci ga raya birane ta hanyoiyi masu dorewa, domin warware wadannan batutuwa a birane."

A nasa bangaren, Uhuru Kenyatta, shugaban kasar Kenya ya ce, Kenya za ta kara bai wa hukumar UN-Habitat tallafin kudi, a kokarin ba da taimako wajen raya birane masu dorewa. Inda ya ce, "Hakika dai, Kenya da wasu kasashe sun gano cewa, yaduwar matsugunan matalauta ta tsananta lalacewar muhalli. Muna bukatar daukar matakan kirkire-kirkire ta hanyar kimiyya. Babban taron a wannan karo ya zo a lokacin da ya dace. Ina fatan ci gaban birane zai kara azama ga bunkasuwar tattalin arziki."

A yayin babban taron, wasu biranen kasar Sin sun yi musayar kyawawan fasahohin raya kansu tare da takwarorinsu na kasa da kasa. A ranar bikin bude taron, hukumar UN-Habitat ta kaddamar da rahotanni 2 dangane da bunkasuwar birnin Shenzhen da wasu yankunan karkara da ke yankin delta na kogin Yangtse.

Shehun malami Raffaele Scuderi na jami'ar Kore ta Enna a kasar Italiya, wanda ya shiga ayyukan rubuta rahotanni, ya yi bayanin cewa, birnin Shenzhen ya sami babban ci gaba wajen daidaita batutuwan karuwar yawan mutane, da raya kimiyya da fasaha ta zamani, da inganta zaman rayuwar mutane a birnin. Inda ya ce, "Birnin Shenzhen ya gwada yadda ake daidaita kalubalen ci gaban tattalin arziki cikin gajeren lokaci. Kyawawan fasahohinsa za su taimaka wa rukunoni da dama wadanda suke kokarin raya kansu, wajen tinkarar batutuwan da suka shafi zaman al'ummar kasa da muhalli."

Za a rufe babban taron a ranar 31 ga watan nan. Za a rika shirya babban taron hukumar ne duk bayan shekaru 4. UN-Habitat hukuma ce ta koli dake da alhakin yanke hukunci kan batutuwan da suka shafi raya birane ta hanyoyi masu dorewa. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China