Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yadda wasu kungiyoyi masu zaman kansu a Najeriya ke kokarin ba da tallafi ga mabukata a watan Ramadan mai tsarki
2019-05-28 14:46:23        cri

Bisa koyarwar addinin Musulunci, ya kamata musulmai masu hali su kara tallafawa mabukata musammam a wannan wata na Ramadan. Don haka a cikin shirinmu na yau, za mu gabatar muku wasu labarai ne kan yadda kungiyoyi masu zaman kansu a Najeriya ke ba da tallafi a wannan wata na Ramadan mai tsarki. Mun tsamo wadannan Labarai ne daga shafin Intanet na Leadershipayau dake Najeriya.

Da farko dai bari mu leka kungiyar mata musulmai ma'aikatan kotu na jihar Filato, wato Judiciary Muslim Women Association of Plateau State (JMWAPS). An ce, sun kaddamar da wani shiri na musamman game da ciyar da almajirai abinci a wannan watan na Ramadan, domin rage yawan yadda almajiran ke yawo a kan tituna da sunan neman abin da za su yi Sahur ko kuma buda-baki da shi. Rahoton ya ce, a kashi na farko na wannan shirin, kungiyar ta ciyar da kimanin almajirai 208 da kuma mata nakasassu guda 45 a cikin Jihar.

A cewar kungiyar, tun a makon da ya gabata ne suka fara kaddamar da shirin a harabar babbar kotun yanki ta uku, da ke Kasuwar Nama a cikin karamar hukumar Jos ta arewa. Shugabar kungiyar, Hajiya Rahamatu Magaji, ta ce 'ya'yan kungiyar sun hada da Alkalai ne da ma'aikata a sashen na shari'a, wadanda suka harhada kudi daga albashinsu domin su fara kaddamar da wannan shirin.

Hajiya Rahamatu Magaji, ta yi nuni da cewa, kwanan nan ne kungiyar za ta fara daukan nauyin tura almajira makarantu, kama daga makarantar Firamare har ya zuwa ta Sakandare. Ta ce, sun fara ne da wannan shirin na ciyar da almajiran saboda almajiran ba su da gata na samun muhimman abubuwan da suke bukata na rayuwa, a kullum suna yawon neman abincin da za su ci, amma idan har sun koshi, tabbas za su zamo mutanan kirki. Bugu da kari, Hajiya Rahamatu ta ce, bayan ciyar da su abinci, mambobin kungiyar za kuma su mayar da hankali ne a kan sha'anin ilmantar da su, duk da ba su cimma matsaya a kan ko guda nawa ne za su fara da su ba, amma dai tabbas za su dauki nauyin wasun su tun daga makarantar Firamare har zuwa Sakandare.

Ban da kungiyar mata musulmai ma'aikatan kotu na jihar Filato, a jihar Kaduna ma ana kokarin ba da irin wannan tallafin. Yanzu bari mu karkata kan Gidauniyar samar da abinci da tufafi dake titin Rasad, wato RSFCF.

A farkon wannan wata na Ramadan ne, shugabar gidauniyar Hajiya Rabi'at Ibrahim ta bayyana shirinsu na kai tallafin watan Azumi ga wasu makarantun Islamiya dake garin Samaru a karamar hukumar Sabon Gari a jihar Kaduna.

Shugabar ta jaddada kudurin cewa, gidauniyar za ta ci gaba da bayar da tallafi ga marayu har bayan ranta a matsayinta na Shugabar gidauniyar ta kasa kuma wacce ta kafa gidauniyar ta farko a halin yanzu.

Ta kara da cewa, gidauniyarta ba ta hadaka ba ce babu hannun kowa a cikin abin da suke bayarwa, daga abin da Allah ya horewa mata ne take tallafa wa marayu da gajiyayyu da shi.

Don haka ne ta yi kira da dukkan masu hali da su taimakawa marayu domin hakan na kara yawan arziki tare da kariya ga arzikin, bayan lada mai tarin yawa da mutum zai samu a wajen Allah musamman a cikin wata mai Alfarma wato Ramadan.

Daga karshe ta ce, tallafawa marayu zai rage yawaitar barace-barace da ake fama da shi a jihohin Arewa.

Ta kuma ce, da yawa wahala ta kan sa munanan tunani ga yara da manya don haka ta yi roko ga duk mai hali ya yi kokari wajen taimakawa kasarsa wajen samun tsari na gari da zai sa gobe kiyama a yi alfahari da shi. Shugabar ta yi fatan yadda aka fara azumi lafiya Allah ya sa a gama lafiya kuma ta yi fatan samun zama lafiya a kasa baki daya.

Makarantar Malama Hauwa Khalil na daya daga cikin makarantun da suka sami tallafin kayan masarufin da suka hada da hijabai da sabulai da karawa daliban kwarin gwiwar yin ibada a wannan wata mai alfarma.

Malama Hauwa Khalil ta bayyana jin dadinta ga shugaban gidauniyar RSFCF Hajiya Rabi Ibrahim bisa ga irin kokarinta tana mai cewa, da za a sami irin masu halinta to da an samu ci gaba a kasa sosai musamman a bangaren taimako ga al'umma.

Har ila a jihar ta Kaduna, a makon da ya gabata ne, kungiyar tallafa wa marayu wadda ke garin Yatama ta karamar hukumar Kudan a jihar Kaduna, ta bayar da tallafi ga marayu maza da kuma mata su 480, domin su ma su yi bikin sallah a cikin farin ciki.

Tun farko a jawabinsa, shugaban kungiyar Alhaji Idris Aliyu Kudan ya ce tun farko sun yi tunanin kafa wannan kungiyar ce, domin ganin sun rungumi marayun da suke yankinsu, inda suka kuduri aniyar samar musu da abinci a lokuta daban-daban da kuma tufafi, musamman a lokutan bukukuwan karama ko babbar sallah.

Ya ci gaba da cewar, kafin su fara ba marayun tallafi, a makarantar Islamiyya da suke karatu, sai suka dauke musu kudin makaranta da suke biya, domin tausaya musu, daga nan sai suka fara tunanin tallafa wa marayun da tufafi, wanda ya ce sun fara da marayu hudu ne kacal.

Alhaji Idris Kudan ya ci gaba da cewar, taron da suka yi a wannan shekara ta 2019, shi ne na 13, amma batun tallafa wa marayu da suke yi karkashin wannan kungiyar, shugaba ya tabbatar da cewar, a duk lokacin da suka sami wata faraga, suna tallafa wa marayu da kayayyakin abinci da kuma tufafi.

Game kuma da nasarorin da suka samu, shugaban ya ce, babbar nasara ita ce, sun fara da tallafa wa marayu hudu, ya zuwa wannan shekara ta 2019, sun yi taron tallafa wa marayu 480, kamar yadda ya ce, wannan babbar nasara ce ga wannan kungiya da kuma shugabannin kungiyar baki daya.

Sai dai kuma, shugaba Alhaji Idris Aliyu Kudan ya nuna matukar damuwarsa kan yadda wasu 'yan asalin wannan gari ke zundensu, na ayyukan tallafa wa marayu da suke yi, ya ce, ya dace in suna yin kuskure ne a ayyukan tallafa wa marayu da suke yi a fito fili a bayyana masu kura-kuransu, ba a rika yi masu suka maras ma'ana ba, sai dai ya tabbatar da cewar, zuwa lokacin wannan taro da suka yi, dukkanin abubuwan da suke aiwatarwa, kwarin gwiwa suke samu, wanda shi ne sirrin nasarorin da suke samu a duk shekara, na karin marayun da ake tallafa musu a duk shekara, maimakon a ce suna yin kasa wajen tallafa wa marayun.

Shugaba Alhaji Alhajki Idris Aliyu Kudan ya kuma yi kira ga daukacin al'ummar wannan gari, da su hada hannu da wannan kungiya ta tallafa wa marayu, domin su zo a hadu wajen samun sakamako nagari a gobe.

Ita ko Malama Bilkisu Abdurrahman Kudan, jigo a wannan kungiya, shawara ta ba takwarorin ta mata, kan yadda wasu mata ke musguna wa marayun da aka bar su a inda suke aure, wato wadda kishiyarta ta rasu ta bar yara, ta ce, ya zama wajibi matan da suke yin wannan mummunan hali, su tuna su ma za su bar marayu a nan gaba.

Masu sauraro, yanzu bari mu leka jihar Nasarawa.

A kwanan nan ne Shugabar Gidauniyar FATMOBUW DIKA Dakta Gimbiya Fatima Muhammad Goni, wadda ta shahara wajen tallafawa marayu, almajirai da marasa gata, ta kaddamar da Masallaci, sabon masallacin da ta gina gami da rijiyar tuka-tuka a karamar hukumar Dorawar Karu ta Jihar Nasarawa. A ci gaba da tallafawa marasa gata, Dakta Fatima Muhammad Goni ta dinkawa almajirai sama da 300 kayan sawa, baya ga mutane daban-daban da ta bai wa jari daga bangaren abin da ya shafi almajirai da sauran jama'a, da kuma samar da guraben karatu ga matasa daban-daban a cikin babban birnin Tarayya Abuja da wasu sassa na jihohin Najeriya, domin ba ta taba fita wani taro ta dawo ba tare da ta bada tallafin wani abu ba, tsakanin gyara masallatai, makarantun Islamiyya da sauransu.

Wakilin LEADERSHIP A YAU ya tattauna da ita jim kadan bayan kaddamar da wadannan muhimman ayyuka, inda ya tambaye ta dalilin gina wannan masallatai da rijiyar tuka-tuka, sai ta ce, irin wadannan ayyuka na alkhairi su ne Allah madaukakin Sarki ya umarci dukkkan Musulmin da Allah ya hore masa ya rika samarwa, domin ta hakan ne Allah yake karawa dukiya albarka ya kuma tsare dukiya da mai dukiyar daga dukkan sharri.

Da wakilinmu ya tambaye ta ko wane irin kira za ta yi ga masu hannu da shuni? Sai ta ce, " Ni kiran da zan yi ga masu hannu da shuni shi ne, su yi wa Allah, su rika taimakawa masu karamin karfi, kuma shi taimako ba sai mutum ya fita waje ba, cikin dangi akwai masu bukatar taimako, makota ma akwai mabukata, abokai akwai mabukata. To idan ba a taimakawa juna ba zamu zauna lafiya ba.

Duk Nijeriya kabilar Hausa Fulani aka sani da yawon bara mazanmu da matanmu, me ya jawo mana hakan? Rashin taimakawa juna, don haka an taimakawa juna, za mu fita daga kangin talauci.(Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China