Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta yabawa kasar Sin bisa amfani da kirkire-kirkire wajen sauya biranenta
2019-05-25 16:02:13        cri

Daraktar zartarwa ta hukumar kula da tsugunar da jama'a da raya birane ta MDD, Maimunah Mohd Sharif, ta yabawa kasar Sin bisa amfani da kirkire-kirkire wajen sauya biranenta da kara mayar da su muhallin da ya dace da rayuwar mazauna.

Maimunah Mohd Sharif wadda ta furta haka jiya a birnin Nairobin Kenya, gabanin taro na farko na zauren hukumar da za a kaddamar Litinin mai zuwa, ta ce kirkire-kirkire shi ne sirrin sauya wuraren hakar ma'adinai zuwa muhallin halittu.

Ta ce a kasar Sin, mutane ne ke gabatar da kudurin raya birane ga gwamnati, inda ita kuma gwamnati ke amfani da fasahohi wajen aiwatar da shi.

A cewarta, wannan ya nuna cewa, aiki tare da al'umma, shi ya kai kasar Sin ga samar da manyan gine-gine bisa amfani da fasahohi da kauyuka masu amfani da lantarkin da aka samar daga hasken rana da sadarwar intanet kyauta da cibiyoyin kiwon lafiya ga yara da kuma kulawa da bukatun kowa.

Har ila yau, ta yabawa gwamnatin kasar Sin bisa damawa da mutanen da suka yi ritaya cikin ayyukanta da kyautata rayuwarsu da kuma sanya su cikin sabuwar ajandar raya birane.

Bugu da kari, ta jinjinawa shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya", tana mai cewa ya kunshi tsarin sufuri a birane da garuruwa. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China