Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yunkurin rufe kasuwa wadda ke da mutane biliyan 1.4 mafarkin shashanci ne kawai
2019-05-24 20:11:35        cri

A kwanan baya, game da jita-jitar "dakatar da yin hadin gwiwa da kamfanin Huawei" da aka yi, daya bayan daya, kamfanonin da abun ya shafa sun fuskanci gaskiya, inda suka bayyana cewa, ba su dakatar da hadin gwiwa da kamfanin ba, kuma suna samar da kayayyaki ga kamfanin Huawei kamar yadda ya kamata, sabanin umarnin gwamnatin Amurka. Wannan ya bayyana cewa, umarnin hana samar wa kamfanin Huawei kayayyaki da gwamnatin Amurka ta fitar, ya kawo hasara ga moriyar kamfanonin kasa da kasa da dama, ciki har da wasu kamfanonin kasar Amurka. Sabo da haka, ana iya cewa umarnin bai samu yarda daga al'umma ba. Alal hakika dai wasu 'yan siyasar kasar ta Amurka ne kawai suke son kawo cikas ga wata babbar kasuwa kamar kasar Sin, wanda hakan mafarki ne na shashanci.

'Yan kasuwa sun fi mai da hankali kan damammakin kasuwanci. Dalilin da ya sa manyan kamfanonin kasa da kasa, kamar kamfanonin Toshiba, da Panasonic na Japan, da kamfanin Infineon na Jamus, da kamfanin sadarwa na EE na kasar Burtaniya, suka musunta jita-jitar ba tare da bata lokaci ba.

Da farko dai, matakin da bangaren Amurka ya dauka ba gaira ba dalili, ya saba wa ka'idojin tattalin arziki da ake bi a kasuwa, har ma ya illata moriyar a zo a gani ta wadannan kamfanoni. Alal misali, bayan da aka fitar da jita-jitar "dakatar da samar wa kamfanin Huawei kayayyaki", nan da nan, darajar takardar hannun jari ta kamfanin Infeneon ta ragu sosai fiye da kima. Wannan alama daga kasuwa ta sanya kamfanonin kasa da kasa sun gane cewa, ba za su iya bin umarnin gwamnatin Amurka na kakaba wa kamfanonin kasar Sin matsin lambar siyasa ba.

A 'yan shekarun baya da suka wuce, ta irin wannan hanya ce Amurka ta kai bugu, har ma ta wargaza wasu manyan kamfanonin kasa da kasa a Turai. Amurka ta kai bugu ga kamfanin Huawei da sauran kamfanonin kasar Sin a wannan karo, kamar yadda ta taba yi a kasashen Turai. Shin kamfanonin kasa da kasa ba su san abun da yake faruwa ba ne? Ba shakka ba za su mika wuya su taimakawa Amurka wajen kai bugu ga kamfanonin Sin sakamakon matsin lamba ba. Balle ma wa zai iya tabbatar da cewa, Amurka ba za ta ci zalinsu a nan gaba ba?

Kowa ya sani cewa, yanzu Amurka tana daukar matakai guda 2 wajen cin zalin kasar Sin, wato kara dora kudin haraji kan kayayyakin da kasar Sin take sayar mata da tayar da yakin cinikayya, da kuma yada jita-jita da shafa wa kasar Sin kashin kaji. Amma tana kara yunkurin cimma manufarta, kasar Sin tana kara samun ci gaba wajen yin amfani da jarin waje a zahiri, da kuma yin ciniki da ketare. Amurka ba za ta iya cutar da tsarin masana'antun kasa da kasa ba, wanda aka kafa sakamakon bukatun kasa da kasa na samun ci gaba, da kuma ka'idojin tattalin arziki irin na kasuwanci.

Yanzu haka kasuwannin kasar Sin suna kara samun ingantuwa, kana kuma Sin tana kyautata karfin masana'antunta, da kamfanoninta na yin takara daga dukkan fannoni, sakamakon manyan bukatun cikin gida da yin gyare-gyare kan tsarin tattalin arziki.

Kasuwar kasar Sin mai al'ummar da yawanta ya kai biliyan 1.4, ba wata kasuwa ce da za a iya raina ta ba, muddin dai mutum na da sanin ya kamata. Ban da haka, a nan kasar Sin ana samun kasuwar kayayyakin da ake bukata wajen samar da kaya, gami da kasuwar kayayyakin masarufi, don haka ba dole ne ta dogaro kan kasuwannin ketare ba. Hakan ya ba ta damar tinkarar kalubale daga ketare, da neman ci gaba mai cikakken inganci. Yayin da kasar Amurka, a nata bangare, tana dogaro ne kan kasuwannin kasa da kasa matuka.

An kwashe shekaru da yawa ana kokarin neman dunkulewar duniya waje guda. Zuwa yanzu ba za a iya raba tattalin arziki duniya, da kebance su cikin kasashe daidaiku ba, kamar yadda ba za a iya sanya ruwan teku ya koma cikin kananan koguna da tabkuna ba. Sa'an nan tattalin arziki na Sin yana kunshe da kudi, da kayayyaki, da fasahohi, da kamfanoni na kasashe daban daban, don haka zai iya jure duk wahalar wani kalubalen da zai shafe shi.

Komai matakan da kasar Amurka ta dauka don toshe hanyar kasar Sin, Sin za ta tsaya kan manufarta na gyare-gyare, da ci gaba da bude kofa ga kasashen waje, ta yadda za ta kare matsayinta na wani wuri mai kyau ga ayyukan zuba jari da cinikayya. Sa'an nan a nasu bangare, 'yan siyasar kasar Amurka, suna kokarin kafa katanga don kebe kasar su daga duniya. (Sanusi Chen, Tasallah Yuan, Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China