![]() |
|
2019-05-24 11:38:08 cri |
Ma'aikatar aikin gona da raya karkara ta ce, kimanin kashi 80 bisa 100 na kauyukan kasar Sin sun shiga cikin shirin tsabtar muhallin, inda aka samu nasarar tsabtace sharar da aka fitar daga gidaje sama da ton miliyan 30 da kuma tsabatace wurare masu kazanta sama da ton miliyan 13 a yankunan karkara.
Gwamnatin Sin ta kaddamar da wannan shiri ne a karshen shekarar da ta gabata, inda ta bukaci al'umma mazauna yankunan karkara su tsabtace muhallansu, kana an gudanar da shirin ta hanyar bin matakai daban daban.
Yu Xinrong, mataimakin ministan aikin gona ya ce, za'a cigaba da sa himma da kwazo domin tabbatar da ganin shirin ya dore duk da irin wahalhalun da za'a iya cin karo dasu a lokutan yanayin zafi.
Yu, ya bukaci kananan hukumomi dasu kara azama wajen kyautata muhallin yankunan karkara, kuma su sa kaimi wajen gaggauta daukar matakan magance matsalolin da suka shafi muhalli.(Ahmad)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China