Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Firaministan Sin ya jaddada muhimmancin kara horas da ma'aikata
2019-05-24 10:17:03        cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya bayyana muhimmancin kara horas da ma'aikata dabaru na ayyukan hidima, ta yadda za a samar da ma'aikata masu ilimi da kwarewa da basirar kirkire-kirkire.

Li wanda ya bayyana hakan cikin wata takardar umarni da ya aikewa taron horas da kwararru. Ya ce, kafa makarantun koyar da sana'o'i da dama, shi ne muhimman mataki na karawa jama'a damar samun aiki yi da karfin masana'anta da saukin magance matsalolin aikin yi, da kara samar da ayyukan yi, baya ga bunkasa tattalin arziki mai inganci.

Firaminista Li ya kuma jaddada kyakkyawan amfani da asusun marasa aikin yi da ragowar jarin samar da horo ga ma'aikata na Yuan biliyan 100, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 14.8 da aka tanada.

Don haka ya ce, ya kamata hukumomi su kara samar da horo ga wasu rukunin ma'aikata dake bakin aiki, da ma'aikata dake aikin karba-karba a kamfanoni dake fadi tashi, da muhimman kungiyoyin ma'aikata da leburori marasa karfi.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China