Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD za ta tallafawa noman danko da busasshen Inabi a Afirka
2019-05-24 09:35:39        cri
Hukumar samar da abinci da aikin gona ta MDD (FAO) ta bayyana cewa, tana shirin taimakawa wajen ganin an samar da danko da busasshen Inabi a nahiyar Afirka.

Jami'in kula da gandun daji a hukumar ta FAO, Erdward Kilawe ya bayyana cewa, hukumar ta FAO tana shirin gabatarwa hukumar gudanarwar kungiyar tarayyar Afirka wannan shiri.

Jami'in ya bayyana yayin taron karawa juna sani game da musayar bayanai da Ilimi da kwarewa kan gadun daji a Afirka cewa, tuni suka goyi bayan matakin hukumar gudanarwar AU(AUC) da majalisar kula da noman danko da busasshen Inabi a Afirka(NGARA) na bullo da dabaru tare da goyon bayan aiwatar da shirin daga shekarar 2017-2030.

Kilawe ya kuma lura da cewa, goyon bayan zai karkata ne ga bangaren musayar bayanai game da samarwa da ciniki, horaswa da kuma musayar fasahohi.

A halin yanzu dai, akwai kasashe 16 dake yankin kudu da hamadar saraha dake samar da danko da busasshen Inabi, da suka hada Burkina Faso da Kamaru, da Chadi da Eritre da Habasha. Sauran sun hada da Kenya da Mali da Mauritaniya da Nijar da Najeriya da Senegal. Sai kuma Somaliya da Sudan ta kudu da Tanzaniya da kuma Uganda.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China