Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Matakan kakaba haraji ba za su tsorata kamfanonin ketare da ke kasar Sin ba
2019-05-23 19:04:30        cri

A kwanakin baya kasar Amurka ta shelanta cewa, a sakamakon yadda kasar Amurka ta kara sanya haraji kan kayayyakin da take shigowa daga kasar Sin, wasu kamfanoni za su kaura daga kasar Sin zuwa Vietnam da ma sauran kasashen Asiya, a yayin da kuma wasu kamfanonin Amurka za su koma gida. Amma furucin ya saba wa dokokin tattalin arziki da kasuwanci, wadda Amurka ta kirkiro domin cimma burinta na musamman.

Sanin kowa ne cewa, wasu kanana da matsakaitan kamfanonin saka tufafi da kera alkalami da huluna sun bar kasar Sin ne a sakamakon yadda kasar Sin ke inganta bunkasuwar tattalin arzikinta, kuma hakan ya faru ne a bisa ga dokokin kasuwanci, a maimakon matakan da Amurka ta dauka na kara sanya haraji.

Amma kasar Amurka tana hada kan sassan biyu, da nufin amfani da batun kara sanya haraji don tilastawa kamfanonin kasashen ketare dake nan kasar Sin su janye daga kasar, ta hanyar amfani da koma bayan tattalin arziki don ta bata sunan kasar Sin.

Amma, kasar Amurka ba ta cimma wannan burin nata ba. Kwanan baya, hukumar kula da harkokin cinikayyar ketare ta Japan ta fitar da rahoto cewa, bisa manyan tsare-tsaren kamfanonin kasar Japan a fannonin fitar da kayayyaki, zuba jari da kuma cinikayyar yanar gizo ta ketare, kasuwar kasar Sin ce ke matsayin farko. A cikin watanni 4 na farkon bana, jarin waje da aka zuba a Sin ya karu da kashi 6.4 cikin dari, yawan jarin da Amurka ta zuba a Sin ya karu da kashi 24.3 cikin dari.

Ban da wannan kuma, bisa takardar bayanin da kungiyar 'yan kasuwar Amurka dake kasar Sin ta bayar kan yadda kamfanonin Amurka ke gudanar da ayyukansu a kasar Sin a shekarar 2019, an gano cewa, kaso 98 cikin dari na kamfanonin Amurka da aka ji ra'ayoyinsu sun bayyana aniyarsu ta ci gaba da gudanar da ayyukansu a kasar Sin.

Me ya sa kamfanonin Amurka ba su so su koma gida duk da cewa Amurka tana ta sanyawa kayayyakin kasar Sin harajin kwastam? Amsar ita ce, saboda na'urorin sadarwa da kwamfuta da sauran kayayyakin latirori da ma kayayyakin kimiyya su ne muhimman fannonin da Amurka ta fi zuba jarinta a ciki a nan kasar Sin, wadanda ke bukatar ma'aikata masu yawa da kwarewa sosai.

Kasar Sin, ita ce kasa daya tak a duniya, dake da dukkan sassan masana'antu. Tana da ingantaccen tsarin samar da kaya da na masana'antu, kana kuma akwai tarin kwararru, lamarin da ya rage yawan kudin da kamfanonin Amurka suka kashe. Bari mu yi misali da kamfanin Apple. Akwai kamfanonin kusan dari 8 wadanda suke samar masa kayayyaki a duk duniya, rabi daga cikinsu na nan kasar Sin. Rahoton nazari da kamfanin Goldman Sachs ya kaddamar a shekarar 2018 ya nuna cewa, idan kamfanin Apple ya kera ya kuma sarrafa kayayyakinsa a Amurka, kudin da zai kashe zai karu da kaso 37%.

Ban da wannan kuma, Sin na da babbar kasuwa mai mutane biliyan 1.4, kashe kudi na zama wani karfi mafi muhimmanci dake ingiza bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin. Ya zuwa yanzu, yawan kudin shiga da kamfanonin Amurka dake kasar Sin suke samu a kowace shekara wajen sayar da kayayyaki ya kai dala biliyan 700, yayin da ribar da suke da su ya haura dala biliyan 50. Takardar bayani da kungiyar 'yan kasuwar Amurka dake Sin ta fitar na cewa, duk da karin haraji da Amurka ta sanyawa kayayyakin kasar Sin, kashi 69 cikin dari na kamfanonin Amurka dake kasar Sin na kara samun riba. Amma idan sun bar kasar Sin, ba wata kasuwa da za ta kai matsayin kasuwar Sin da kamfanonin Amurka za su koma su kuma samu riba mai armashi.

Abu mafi muhimmanci shi ne, a cikin shekara daya da ta gabata kasar Sin ta ci gaba da aiwatar da manufar kara bude kofa ga kasashen waje bisa shirin da ta tsara, matakin da ya sa kamfanonin kasar Amurka kwantar da hankalinsu yayin da suke gudanar da harkokinsu a kasar Sin. Kana bayan da kamfanin ExxonMobil ya zuba jari a kasar Sin domin gudanar da aikin man fetur a kasar, kuma kamfanin Tesla ya fara gina kamfanin kera motoci masu amfani da wutar lantarki na farko dake ketare a birnin Shanghai na kasar Sin, yanzu haka kamfanin samar da motoci mai dogon tarihi na Ford ya sanar da cewa, zai kaddamar da aikin kera motoci samfurin Lincoln a kasar ta Sin kafin karshen shekarar bana da ake ciki.

A hannu guda kuma, gwamnatin Amurka ta kasa kula da muradun jama'arta da kuma kamfanoninta, har tana kara sanya haraji kan kayayyakin da ake shigowa da su cikin kasar daga wasu kasashen duniya, lamarin da ya haddasa rashin daidaito da rashin tabbas ga kasuwar duniya, a sanadin haka, tun daga shekarar bara, wasu kamfanonin Amurka sun fara kaurar da harkokinsu zuwa ga wasu kasashe, domin biyan bukatun kasuwar kasar Sin da ta sauran kasashen duniya.

Sa'an nan birnin Chicago, birni na uku mafi karfin tattalin arziki cikin biranen kasar Amurka, kai tsaye ya kulla yarjejeniyar hadin gwiwa da kasar Sin, kan wasu manyan sana'o'i tsakanin shekarar 2018 zuwa ta 2023. Sana'o'in da suka hada da kiwon lafiya, da samar da kaya, da kirkire-kirkire, da hada-hadar kudi, da aikin gona da abinci, da kayayyakin more rayuwar jama'a, da dai makamatansu.

Matakin kara harajin kwastam da kasar Amurka ta dauka ba zai tsoratar da kamfanonin kasashen waje da suke gudanar da harkokinsu a kasar Sin ba, maimakon haka ma, matakin ya tilasta wasu kamfanonin kasar Amurka barin kasarsu ta asali, lamarin da ya kara tsananta matsalar da kasar Amurka ke fuskanta a fannin masana'antu. Sa'an nan wanda ya jefa kasar Amurka cikin wannan mawuyacin hali shi ne shugabannin gwamnatin kasar wadanda ke tsananin son kansu. (Lubabatu, Kande, Tasallah, Bilkisu, Murtala, Bello, Jamila, Amina)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China