Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hana ci gaban kasar Sin bisa fasahohin da wani ya mallaka, mafarki ne da ba zai tabbata ba
2019-05-22 19:55:57        cri

Bayan da ya dauki matakin hana fitar da kayayyaki ga kamfanin Huawei a kwanan baya, bangaren Amurka ya sake lalata sunan kamfanin DJ-Innovations, wato DJI na kasar Sin, inda ya ce akwai bayanai masu hadari, a cikin jiragen sama marasa matuki da kamfanin ya kera, sannan ya yi barzanar cewa, nan da wasu makonni masu zuwa, zai sa niyyar ko zai sa kamfanin Hikvision na kasar Sin wanda ke samar da na'urorin bidiyo na sa ido a kan takardar kamfanonin da ba zai yarda da su sayi fasahohin zamani daga kamfanonin kasar Amurka ba ko a'a. A 'yan kwanakin nan, har ma wasu tsirarrun 'yan siyasa na Amurka sun ce, nasarar da kamfanin CRRC na kasar Sin ya samu a yayin gasar zana shirin gina sabon layin dogo dake karkashin kasa na birnin New York, "za ta kawo barazana ga tsaron kasar Amurka", sun nemi a yi bincike kan gasar.

A cikin wasu gajerun kwanaki kawai, wasu 'yan siyasa na Amurka sun sha kawo wa kamfanonin kimiyya da fasaha na kasar Sin matsaloli. A ganin galibin mutane, sun yi haka ne ba zato ba tsammani, amma a hakika dai, tabbas ne za su yi hakan. Kasar Amurka, wato kasaitacciyar kasa mai fada a ji daya tilo a duk fadin duniya, ko da yake tana kan gaba sosai a duk fadin duniya a fannonin kimiyya da fasaha, da aikin soja da tattalin arziki da kuma sauran fannoni daban daban, amma wasu 'yan siyasa ba su da hakuri ko kadan, ba su son sauran kasashen duniya su samu ci gaba kamar yadda ya kamata, balle su ketare kasar Amurka a wasu fannoni.

Bisa kokarin ka'in da na'in da Sinawa suka yi a cikin shekaru 40 da suka gabata, bisa babbar manufar bude kofa da yin gyare-gyare a gida, kasar Sin ta samu ci gaba sosai a wasu fasahohin zamani. Kamfanonin Huawei da DJI da Hikvision, sun kasance kamar wakilan kamfanonin kasar Sin wadanda suke mallakar fasahohin zamani da kuma samar da ingatattun kayayyaki bisa farashi mai dacewa, sun samu amincewa a kasuwannin kasashe daban daban. Kasashe da yawa, ciki har da kasar Amurka sun riga sun bincika kayayyakinsu wajen batun tsaron kai, sun kuma tabbatar da cewa, kayayyakinsu ba za su haifar da matsalolin tsaron kai ba.

Yanzu haka, 'yan siyasar da suka mayar da Amurka a gaban kome sun yi watsi da ka'idar yin takara cikin adalci a kasuwanni, wadda suka taba yin alfahari kanta. Sun yi amfani da karfin gwamnati sun ci zalin kasar Sin ta fuskar fasaha, da sunan wai kila kasar Sin ta aikata laifi. Suna yunkurin hana ci gaban kimiyya da fasahar kasar Sin, da kiyaye yadda Amurka take yin babakere a duniya. Sa'an nan kuma, suna matsa wa kasar Sin lamba fiye da kima, yayin da yakin ciniki ya kara kazanta. Abubuwan da Amurka ta yi sun katse huldar da ke tsakanin masana'antun dake sarrafa kaya a matakin farko, da masana'antu dake sarrafa kaya a matakin karshe, sun kuma kawo babbar illa kan karuwar tattalin arzikin duniya, da ci gaban kimiyya da fasahar dan Adam, da cin gajiyar sakamakon al'adu.

Alal misali, ainihin yunkurin Amurka na kai wa kamfanin Huawei hari shi ne fasahar 5G da yadda ake amfani da ita, fasahar da take da muhimmiyar ma'ana wajen hada abubuwa iri daban daban tare, da kara azama kan hadewar yanar gizo ta Intanet da manyan bayanai, fasahar na'urori masu sarrafa kansu da sassan tattalin arziki. Ana bukatar kasashen duniya su inganta hada kansu, a kokarin kawo wa 'yan Adam alheri. Amma Amurka mai son kai ta yi dabara, ta ci zalin kamfanin Huawei, duk da kawo cikas wajen raya fasahar aikin sadarwa ta duniya. Abun da Amurka ta yi, ba a ga irinsa a tarihin ci gaban kimiyya da fasahar 'yan Adam a karni na 21 ba, bai kuma yi daidai da ci gaban al'adun Bil'Adama ba.

Hakika, duk da cewa wasu 'yan siyasa na kasar Amurka suna ta zargin kayayyakin kamfanonin Huawei da DJI, da "yiwuwar haifar da mummunan tasiri ga tsaron kasar Amurka", amma har zuwa yanzu, ba a samu shaida ko daya ba tukuna wadda za ta iya tabbatar da zargin.

Matakan rashin kima da 'yan siyasan kasar Amurka suka dauka sun sa wasu masanan kasar damuwa. Misali, shahararren masanin ilimin tattalin arziki, Jeffrey Sachs, ya taba bayyana cewa, "kuskure" kadai da kasar Sin ke da shi, shi ne yadda ta mallaki al'ummar da yawanta ya kai biliyan 1.4. Idan kasar Koriya ta Kudu mai mutane miliyan 50 ce ta samu wasu fasahohi masu ci gaba, to, kasar Amurka za ta mai da kasar abar yabawa, bisa ci gaban da ta samu. Wannan shi ne gaskiyar batun. Saboda kasar Sin wata babbar kasa ce, don haka Amurka na tsoron ganin kasar Sin ta girgiza matsayinta na shugabancin duniya.

Game da kamfanonin kasar Sin, wadanda suka taba jure wahalhalu sosai a kasuwannin ketare, matakin danniya a fannin fasahohi da kasar Amurka ta dauka ya zame musu wani sabon kalubale, wanda zai dan ba su wahala cikin wani gajeren lokacin. Amma, duk da haka, mun san duk wata nasarar da aka samu, an same su ne bayan jure wahala. Nan gaba, kamfanonin kasar Sin za su mai da matakin toshe hanyar da kasar Amurka ta yi musu ya zama wata damar raya fasahohi, da dogaro da kansu.

Ta hanyar nuna hakuri da juriya, gami da kokarin neman ci gaban kanta, kasar Sin za ta mayar da martani ga duk wani matakin da aka dauka karkashin ra'ayi na danniya. (Sanusi, Tasallah, Bello)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China