Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ba wanda zai iya rusa babbar kasuwar kasar Sin
2019-05-21 20:10:46        cri

Ga kamfanin GAP wanda ke samar da tufafin yau da kullum na Amurka, shekarar 2019 shekara ce mai ma'ana sosai. A lokacin da ake shirin murnar cika shekaru 50 da kafuwarsa, kamfanin ya fitar da shirin rufe daruruwan kantunansa dake yankin Amurka ta arewa, ta yadda zai fi mai da hankali kan bunkasa kasuwancinsa a kasar Sin. A watan Afrilun bana kawai, ya bude kantuna 11 a babban yankin kasar Sin, kuma bisa shirinsa, yawan sabbin kantunan da zai bude a babban yankin kasar Sin zai kai a kalla 40.

Bayan an shiga shekarar 2019, ba kamfanin GAP kawai ke da shirin zuba karin jari a kasar Sin ba, sauran masu zuba jari na kasa da kasa ma suna yin haka.

Bisa alkaluman da aka bayar, an ce, daga watan Janairu zuwa na Afrilun bana, yawan jarin waje da aka riga aka zuba a kasar Sin ya kai fiye da kudin Sin yuan RMB biliyan 305, wato ya karu da 6.4% bisa makamancin lokacin bara

Yanzu jarin da ake zubawa a tsakanin kasa da kasa yana gudana sannu a hankali, amma yawan jarin da ake zubawa a babban yankin kasar Sin yana ta karuwa, wannan ya alamta cewa, masu zuba jari na kasa da kasa suna cike da imani ga bunkasuwar kasar Sin a nan gaba.

Da farko dai, babban dalilin da ya sa masu zuba jari na kasa da kasa suke da imani shi ne, kasar Sin wata babbar kasuwa ce, inda ake da masu sayayya kusan biliyan 1.4, wadanda suke kunshe da wani rukunin masu matsakaiciyar rayuwa dake samun ci gaba cikin sauri, su ne kuma suka kafa wata babbar kasuwa a kasar Sin. Sabo da haka, a 'yan kwanakin nan, Warren Buffett wanda ya kware sosai wajen cinikin takardun hannun jari a Amurka ya bayyana cewa, kasar Sin wata babbar kasuwa ce, "muna son babbar kasuwa", a cikin shekaru 15 masu zuwa, zai yi wasu muhimman abubuwa a wannan babbar kasuwa ta kasar Sin.

Na biyu kuma, masu zuba jari na kasa da kasa suna nuna karfin zuciya kan kasar Sin sakamakon kasuwa na ci gaba sosai a kasar. A cikin watanni 4 na farko a bana, halin musamman da kasar Sin take da shi a fannin jawo jarin waje ya sha bamban sosai. Aikin kera kaya bisa fasahar zamani, da kuma aikin ba da hidima bisa fasahar zamani suna kasancewa a matsayin sabbin bangarorin da suka kara azama kan bunkasuwar tattalin arzikin Sin.

Kasar Sin tana aiwatar da manufofi da dokoki masu alaka da tabbatar da rashin nuna bambanci a tsakanin kamfanonin Sin da masu jarin waje, da kara karfin kiyaye ikon mallakar ilmi. Don haka tana nan tana zama wani wurin da ke jawo hankalin wasu kamfanonin fasahar zamani masu jarin waje, ta yadda za su sabunta fasaha, da raya fasahar 5G, da fasahar na'urori masu sarrafa kansu. Alal misali, kamfanin Dell ya hada kansa da wasu shahararrun kamfanoni wajen kafa kawancen kera kaya a nan kasar Sin.

Har ila yau kuma, masu zuba jari na kasa da kasa sun nuna karfin zuciya kan kasar Sin, saboda ana tabbatar da daidaito a kasuwannin kasar Sin. Yanzu haka ana kara samun rashin tabbaci a makomar tattalin arzikin duniya. Masu zuba jari na kasa da kasa sun fi mai da hankali kan tabbatar da daidaito a kasuwannin wata kasa, da kuma yiwuwar cimma manufa a kasuwannin. Yanzu gwamnatin Sin tana aiwatar da manufofi masu nagarta, wajen tinkarar matsalolin raya tattalin arziki da take fuskanta, da kuma wadanda za ta gamu da su a nan gaba. Tana kuma zurfafa yin gyare-gyare a gida, da kara bude kofa ga ketare daga dukkan fannoni. Masu zuba jari na kasa da kasa sun kwantar da hankalinsu, saboda ganin kasar Sin ta gaggauta kyautata yanayin kasuwanci, inda ake tafiyar da harkoki bisa doka, tare da bude kofa ga ketare, da samar da sauki ga 'yan kasuwa.

A kwanakin nan, kasar Sin ta zama kasa daya tak da asusun ba da lamuni na duniya IMF ya yi hasashen cewa, za ta kara sauri a fannin karuwar tattalin arziki.

Har ila yau, kungiyar 'yan kasuwan kasar Amurka dake kasar Sin, ta sanar da wani rahoto game da muhallin ayyukan kasuwanci a kasar Sin, wanda ya nuna cewa, kashi 80% na kamfanonin Amurka da aka tambaye su, sun ce muhallin zuba jari na kasar Sin na kara kyautatuwa, yayin da kashi 62% daga cikinsu na kallon kasar Sin a matsayin daya daga cikin kasashen 3 da suka fi son zuba musu jari.

Babu shakka, yadda kamfanonin kasashe daban daban ke kara zuba jari ga kasar ta Sin, ya nuna yadda ake da imani kan kasuwannin kasar, wadanda suke da girma, da wani yanayi na samun karuwa da karko.

A nasa bangare, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya furta wajen taron dandalin tattaunawar hadin kan kasa da kasa karkashin shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya", wanda ya gudana a birnin Beijing a kwanakin baya, cewa kasar Sin za ta ba da izini ga kamfanonin kasashen waje, domin su shiga karin sana'o'i, da kara kokarin hadin gwiwa da kasashe daban daban, wajen kare ikon mallakar fasahohi, da shigo da karin kayayyaki da hidimomi daga ketare. Sauran manufofin da shugaban ya yi alkawarin gudanar da su, sun hada da neman daidaita manufofin tattalin arziki na kasashe daban daban, da kokarin aiwatar da manufar bude kofa ga kasashen waje da yin gyare-gyare a gida.

Ganin wadannan abubuwa sun sa ana fahimtar cewa, kasar Sin tana da cikakkiyar niyya da kwarewa a kokarin raya tattalin arzikinta, don haka kashin kajin da ake neman shafawa kasar ba zai yi amfani ba, sa'an nan ba wanda zai iya hana tasowar tattalin arzikin kasar ta Sin. (Sanusi, Tasallah, Bello)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China