Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurka ta sanar dage haramcin da ta sanyawa kamfanin Huawei
2019-05-21 16:27:46        cri
Shafin internet na ma'aikatar cinikayya ta kasar Amurka ya wallafa cewa, an baiwa kamfanin Huawei da kamfanonin da suke hadin gwiwa wa'adin kwanaki 90. An ce, an dauki wannan mataki ne domin baiwa sassan biyu daidaitawa tare da hukumomi da kamfanonin da abin ya shafa.

A yau Talata, shugaban kamfanin Huawei na kasar Sin Ren Zhengfei ya yi hira da 'yan jaridan kasar Sin a cibiyar kamfanin Huawei dake birnin Shenzhen na kasar, inda ya ce, wa'adin da kasar Amurka ta baiwa kamfanin shirme ne. Kuma hakan ba zai yi tasiri ga raya fasahar 5G da kamfanin Huawei ke kokarin samarwa ba. A wannan fanni, babu kamfanoni da za su iya zarce kamfanin Huawei a cikin shekaru 2 ko 3 ba.

Hakazalika, Mr Ren ya bayyana cewa, ba sa adawa da kananan na'urorin laturoni na Amurka, amma ya kamata bangarori biyu su samu ci gaba tare. Amma idan akwai matsalar samar da na'urorin, kamfaninsa yana da kayayyaki a ajiye don daidaita matsalar. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China