Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Amurka ce ke haddasa yawancin "gibin kudi" a duk duniya
2019-05-20 20:58:04        cri

A kullum, kasar Amurka na daukar matakai tamkar "kura dake cewa kare maye" a lokacin da take addabar abokan hamayya. A 'yan kwanakin nan, tana amfani da irin wannan mataki kamar yadda wata mahaukaciya take yi.

Alal misali, a jajibirin zagaye na 11 na shawarwarin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka, ba zato ba tsammani, bangaren Amurka ya fitar da wasu bayanai, inda ta ci zarafin bangaren Sin, tana mai cewa, wai matsayin da bangaren Sin ke dauka kan shawarwarin yana haifar da "koma baya", har ma bisa wannan hujja, harajin kwastam da take bugawa kayayyakin kasar Sin da darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 200, kuma ake shigar da su kasar Amurka ya karu daga 10% zuwa 25%. Amma a hakika dai, bangarorin biyu sun sha tattaunawa kan wasu batutuwa, domin kokarin neman samun matsaya guda, da kuma tabbatar da su a cikin wata yarjejeniya, wannan ya kan faru a lokacin da ake yin shawarwari kan wani batu. Har yanzu, ba a kai ga daddale yarjejeniya ko guda ba tsakanin Sin da Amurka, ina dalilin da ya sa bangaren Amurka ya ce matsayin bangaren Sin ya haifar da "koma baya"?

Al'amuran da suka faru sun shaida cewa, kasar Amurka ce ta kan jefar da matsayar da bangarorin biyu suka cimma a gefe. Tabbas ana iya tunawa da cewa, a ran 19 ga watan Mayun shekarar 2018, bangarorin Sin da Amurka sun fitar da wata sanarwa tare, inda suka shelanta cewa, sun cimma matsaya daya ta daina yin yakin cinikayya. Amma ba zato ba tsammani, bayan kwanaki 10 kacal da hakan, gwamnatin Amurka ta musunta wannan sanarwa, har ta shelanta cewa yawan harajin kwastam da za ta buga kan kayayyakin kasar Sin da darajarsu ta kai dala Amurka biliyan 50 zai karu zuwa 25%. Sannan a watan Disamban bara, bangarorin biyu sun cimma ra'ayi daya kan yawan kayayyakin da kasashen Sin da Amurka za su yi ciniki, amma a yayin tarukan shawarwarin da aka yi a baya, sau da dama bangaren Amurka yana son neman karin moriya daga wajen kasar Sin, har ma ya sake yin kurarin cewa zai buga karin harajin kwastam kan kayayyakin kasar Sin. Sakamakon haka, an kawo cikas sosai ga shawarwarin da ake yi tsakanin bangarorin biyu.

Yanzu, wasu 'yan siyasa na Amurka suna daukar matakan mayar da baki fari, suna yunkurin lalata sunan kasar Sin, har ma sun zargi kasar Sin cewa, ta kawo barzana ga duk duniya, ko kasar Sin na "kai farmaki a fannin tattalin arziki", ko kasar Sin na "yin sata", ko sun ce, kasar Sin tana son "mulkin duk duniya", da sauran kalamai masu ban mamaki, domin kokarin kawo cikas ga ci gaban kasar Sin, da kuma kiyaye ikon Amurka na tafiyar da mulkin danniya a duk duniya da yake bata sannu a hankali.

Yadda kasar Amurka ke kokarin daukar wadannan matakai ya nuna rashin karfi a zuciyarta. Tana ta neman shafa wa kasar Sin kashin kaji, don boye karkata hankalin jama'ar duniya, ta yadda ba za su gane cewa kasar Amurka ce ke ta da kayar baya a duniya ba.

Ga misali, kasar Amurka ta kan dora moriyar ta bisa wani matsayin da ya fi yarjejeniyoyin kasa da kasa. Sa'an nan tana daukar manufar "tabbatar da moriyar kasar Amurka da farko", da janye jikinta daga wasu kungiyoyin kasa da kasa, lamarin da ya keta ka'idojin kasa da kasa, da lalata tsarin kasancewar bangarori daban daban a duniya, da sanyawa a gamu da matsala a fannin kula da harkokin kasa da kasa. A shekarar 2017, an gabatar da wani rahoto bisa nazarin a aka yi, kan hukuncin da aka yanke game da takaddamar da aka samu cikin kungiyar ciniki ta duniya WTO, inda aka gano cewa, kasar Amurka ita ce wadda ta fi nuna kin yarda ga hukucin da kungiyar WTO ta yanke, sa'an nan kashi 2 cikin kashi 3 na kararrakin da aka kai wa WTO suna da nasaba da kasar Amurka.

A sa'i daya, kasar Amurka, bisa manufarta, wai "wanda ya samu nasara ya cinye duka", tana ta neman ta yi rikici da sauran kasashe. Misali, tana kokarin gina wata babbar katanga a kan iyakar dake tsakaninta da kasar Mexico, da rura wuta a yankin gabas ta tsakiya, da kwan-gaba kwan-baya yayin da take kula da harkokin kasa da kasa, lamarin da ya lalata imanin da ake da shi tsakanin kasa da kasa, gami da girgiza tushen hadin gwiwarsu, tare da haddasa tsanantar takaddamar ciniki, da rikicin siyasa a duniya.

Ban da haka, kasar Amurka ta kan nuna fin karfi a wurare daban daban na duniyarmu, da haddasa matsalalolin jin kai masu tsanani, ta yadda ta hana ruwa gudu ga yunkurin neman samun zaman lafiya a duniya. Kudin da kasar Amurka ta ware don biyan bukatunta na gudanar da ayyukan soja a bana ya kai dalar Amurka biliyan 600. Sa'an nan wannan jimillar za ta kai biliyan 750 a shekarar 2020 mai zuwa, wadda ta fi ta duk wata kasar dake duniya. Dangane da lamarin, tsohon shugaban kasar Jimmy Carter ya taba bayyana cewa, "kasar Amurka ita ce kasa mafi son ta da yake-yake a tarihin dan Adam".

A 'yan shekarun baya da suka wuce, Amurka ta yi ta cin zalin manyan abokan cinikinta da sunan kudin kwastam, a yunkurin tabbatar da yadda take yin babakere a fannonin tattalin arziki da kimiyya da fasaha, ta sanya takunkumi kan kamfanin Huawei, da sauran kamfanonin kimiyya da fasaha na zamani. Da gangan kuma, ta yi barna kan tsarin masana'antun duniya, abin da take yi yana tsananta matsalar bunkasuwa a duniya. A watan Afrilun bana, asusun ba da lamuni na duniya wato IMF ya rage karuwar tattalin arzikin duniya na shekarar 2019, wanda ya yi hasashen samun karuwa zuwa 3.3%, ya kuma yi kashedin cewa, mai yiwuwa ne karuwar tattalin arzikin duniya zai ci gaba da raguwa sakamakon tsanantar matsalar cinikin duniya.

Yanzu lokaci ya yi da dukkan 'yan Adam suke kokarin raya al'umma mai kyakkyawar makoma. Kamar yadda shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya fada, wajibi ne kasashen duniya su tafiyar da harkokin duniya tare, haka kuma su tsara ka'idojin kasa da kasa tare, sa'an nan ba shakka su ci gajiyar bunkasuwa tare, su yanke hukunci kan makomarsu da kansu. Tuni dai aka yi watsi da siyasar masu fada a ji. Abubuwan da Amurka ta yi ba su tafiya daidai da tarihi, ba su dace da halin da ake ciki a duniya ba, ba su bin ra'ayoin al'umma. Kana kuma sun rika tsananta matsalar tafiyar da harkokin kasa da kasa, sun zama abun da ya fi hana ci gaban duniya yanzu. (Sanusi Chen, Bello Wang, Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China