A wannan mako, za ku ji wata hira wadda abokin aikinmu Murtala Zhang ya yi da Nuhu Yahaya, ma'aikaci a ma'aikatar kasafin kudi da tsare-tsare ta tarayyar Najeriya wanda yake karatun digiri na uku a kasar Sin, a fannin kimiyyar tattalin arziki a jami'ar Peking, jami'in ya bayyana yadda tsarin ci gaban da kasar Sin ta samu ya burge shi da kuma yadda ya ga sauye sauye ta fuskar ci gaba fiye da yadda yayi tsamammani tun da farko, kana ya bayyana gamsuwa game da tsarin ilmin kasar Sin. Ga dai yadda hirar tasu ta kasance.