Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban kasar Sin tare da uwargidansa sun halarci bikin nune-nunen al'adun Asiya tare da sauran shugabannin kasashe daban daban
2019-05-16 14:42:43        cri





A jiya Laraba da dare, shugaban kasar Sin Xi Jinping tare da uwargidansa Peng Liyuan sun halarci bikin nune-nunen al'adun Asiya tare da sauran shugabannin kasashe daban daban da suka halarci taron tattauna wayewar kan nahiyar Asiya, bikin da ya kasance wani muhimmin bangaren na taron. A madadin gwamnatin kasar Sin da ma al'ummarta ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi lale marhabin da baki da masu nuna fasahohin al'adu na kasashe daban daban, kuma a jawabin da ya gabatar ya bayyana cewa, "Kasashen Asiya suna da dadaddun al'adu nagari, al'adun da suka bambanta da juna tare kuma da zama lafiya da juna. Nau'o'in al'adu iri daban daban sun kara wa al'adun kasashen Asiya armashi da kuma dorewa. A yau da dare, nune-nunen al'adu da za a nuna za su cike gibin bambanci da ke tsakanin kabilu daban daban, tare kuma kara fahimtar juna a tsakanin al'ummominsu. Baya ga haka, bikin zai nuna wa duniya nahiyar Asiya kyawawa da ke cike da kuzari, da zaman lafiya da kuma ci gaba."

Shugaba Xi ya jaddada cewa, tun zamanin gargajiya, al'ummar Sinawa sun kasance masu son zauna lafiya da makwabtanta, da kuma masu fatan alheri ga makwabtanta. Jama'ar kasar Sin na fatan ganin kasashen Asiya za su kasance masu taimakon juna da goyon bayan juna, ta yadda za su tabbatar da makomarsu kyakkyawa da ma ta duniya baki daya.

An kaddamar da bikin a yayin da matasa da kungiyoyin mawaka da suka fito daga kasashe daban daban suke rera waka mai taken "Nahiyarmu ta Asiya" tare, wakar da aka tsara musamman domin wannan biki. Masu kallon bikin ma sun hada kan mawakan suna rera wakar tare. Matasan kasashen Asiya daban daban da ke rike da tutocin kasashensu sun taru a dandalin bikin, a yayin da kuma motocin wasa da suke wakiltar kasashe daban daban sun yi ta wucewa.

Nahiyar Asiya ta kasance daya daga cikin muhimman mafarai na wayin kan dan Adam, kuma a nahiyar, al'adun al'ummomi daban daban na nuna kyaunsu na musamman. A wajen bikin, masu fasahohin al'adu na kasashen Asiya sun bayyana al'adunsu na musamman, da kuma zumuncinsu da ma fatan alheri bisa ga wake-wake da raye-raye da suka samar.

Ban da 'yan wasa na kasashen Asiya, shahararren mawakin kasar Italiya Andrea Bocelli ya kuma yi wata shahararriyar waka mai taken "Babu wanda zai yi barci a wannan dare", wakar da ta burge masu kallo a wajen bikin.

A karshen bikin, wata waka mai taken "haskaka Asiya" da mawaka da dama suka rera tare, ta bayyana burin al'ummar kasashen Asiya ta samun makoma guda da zaman alheri, wakar ta kuma dasa aya ga bikin. Masu kallo kimanin dubu 30 a wajen, sun ganewa idonsu wannan gagarumin biki na nuna al'adu. (Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China