Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sun Yang ya zama zakarar wasan ninkaya na duniya
2019-05-16 14:02:26        cri

A shekarar, 2008, Sun Yang ya kammala wasansa na Olympics na farko a Beijing, inda yayi tafiyar tsawon mita 1,500 a wasan karshe, a lokacin yana da shekaru 17 kacal a duniya.

A yanzu haka, yana da shekaru 28, Sun yayi wasan ninkayarsa na hudu a gasar Olympics. Inda ya samu lambobin zinare sama da 100, hakan ya bashi damar zama zakaran wasan ninkaya na farko a tarihi inda ya samu wannan babban matsayi a duniya a dukkan matakai na wasan ninkaya a mataki na tsakiya da matakin nisan zango, kama daga kan mita 200 zuwa mita 1,500. A yanzu haka dai Sun ya kafa tarihin samun matsayin fitaccen dan wasan ninkaya a duniya na wannan zamanin.

Kimanin shekaru 10 kenan, Sun ya taso ne tun yana dan karami yake da sha'awar wasan ninkaya, a wasu lokuta yana kuka da idanuwansa a lokacin da ake shiryar muhimman gasar iyo har lokacin da yakai mataki na babban kwararre a fagen ninkaya har ya zama jagoran babbar kungiyar wasan ninkaya ta kasar Sin.

"Ninkaya shine rayuwata. Na shafe dukkan rayuwata tun ina matashi wajen yin ninkata kuma farin cikina yana samuwa ne daga irin kokarin da nake yi da irin nasarorin dana cimma daga ruwa," inji Sun.

Dan wasan wanda ya samu lambobin zinare har sau uku kuma wanda ya zama zakaran wasan ninkaya na duniya sau 9 ya kasance wani babban darasi da abin koyi bisa irin namijin kokarin da yayi.

Mayar da ruwa baya cikin sauri kuma da karfi tare da cikakken kwarin gwiwa, Sun yana yin gwajin samun kwarewa a kusan awoyi 2 da rabi wata ran kuma da yamma, yayin tattaunawar da yayi da kociyansa game da irin nasarar da yake samu a gwajin da yake gudanarwa.

A wasu lokuta yana amfani da wasu fedoji, da takalmin ruwa, da kuma wani allo wanda yake yin amfani dashi wajen daurawa a jikinsa a lokacin da yake samun horo.

"Yana yin iyo sau 9, a kowanne ya kai nisan kilomita 8, kuma yana motsa jiki a sau 3 a cikin kowane mako," inji Denis Cotterell, babban kociyan kasa da kasa dake horas da Sun.

Sun, tare da 'yan wasan babbar kungiyar ninkayarsa, a yanzu haka suna samun horo a wani sansanin horo na hunturu dake Kunming, babban birnin lardin Yunnan dake kudu maso yammacin kasar Sin, inda suke shirye shiryen gasar wasan zakaru ta duniya ta shekarun 2019 da 2020 a Tokyo.

Yankin dake tsakiyar Yunnan-Guizhou mai manyan tsaunuka, Kunming tana da nisan tafiyar sama da mita 1,800 a saman teku.

"Yin horo a yankin mai tudu yana taimakawa 'yan wasa su samu karin kuzari mai cike da koshin lafiya," inji Zhu Zhigen, kociyan Sun Yang.

"shekarar 2019 tana da muhimmanci game da shirye shiryenmu na halartar gasar wasannin Olympics na Tokyo kuma zamu yi amfani da wannan damar a Koriya ta kudu, a matsayinmu na zakarun wasan ninkaya zamu je can domin halartar gasar cin kofin kwararru ta duniya ta wannan shekarar," Zhu ya kara bayyanawa.

Sun ya zauna a Kunming tsawon kwanaki 25 kuma a koda yaushe shine na farko da yake fitowa kuma na karshen komawa daga wajen samun horon ninkayar da ake gudanarwa a kullum.

"Wannan shine halayyata. Ina son na kara mayar da hankali," injishi.

Denis yana farin ciki game da yadda Sun Yang yake mayar da hankali game da aikinsa. "Na gani yadda yake da da'a da kuma yadda yake mayar da hankali. Yana cigaba da samun bunkasuwa kuma ina iya gane hakan a cikin ayyukansa."

Kashinsa ya kode, zanen yatsunsa sun goge, gadon bayansa duk ya jeme, kwanakin da ya kwashe yana samun horo duk ya nuna alamu a jikinsa, amma duk da hakan yana cike da kwarin gwiwa.

"Samun raunuka ba wani bakon abu bane ga 'yan wasa. Fama da wahalhalu wani bangare ne na wasanni, musamman idan kana son cimma nasarori masu inganci a dukkan yunkurin da kake. Amma ba abu ne mai sauki ba ka iya samun lambar yabo," ya bayyana hakan ne yana murmushi.

Sun yana dora muhimmanci kan gasar wannan shekara kuma yana da kwarin gwiwa wajen kare kambunsa a gasar kwararru ta duniya. "Ina tunanin zan iya kuma bazan baiwa kaina wahala mai yawa ba. Tabbatar da samun cikakkiyar lafiyata shine mafi muhimmanci."

"Gamuwa da cikas da wahalhalu ana iya cin karo dasu a kan hanya, amma yadda nake da jajurcewa da tsayawa tsayin daka da yadda nake bada hadin kai ga tawagata zai iya taimaka mini wajen samun sabbin nasarori na kafa tarihi," ya kara bayyana hakan.

Zakaran kungiyar wasan ninkayar yayi amanna cewa, yin amfani da lokaci shine abu mafi dacewa. "Lokaci ne kadai zai tabbatar da hakan. Samun kyakkyawan sakamako yana bukatar lokaci, kuma dolene a sa himma da kwazo."

Sun ya danganta irin nasarorin da ya samu da kungiyar wasan sa. "A cikin dogon lokaci, shugabannina, kociyoyina, da manyan shehunnan malamai a wannan fage da nake aiki da iyalaina dukkansu sun yi aiki tukuru matuka, wajen tabbatar da samun nasarata a rayuwa. Idan badon su ba, babu wata nasara da zan iya cimmawa."

"A shekarar 2020 watakila zan buga wasana na Olympics na karshe, kuma inason zan yi iya bakin kokarina wajen samun karshe mai kyau domin sakawa kokarin da iyalaina suka yi mini," Sun ya tabbatar da hakan. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China