Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wu Lei ya ja hankalin jagoran La Liga
2019-05-16 14:04:08        cri

Dan wasan kasar Sin Wu Lei, dake bugawa RCD Espanyol ta Sifaniya tamaula, ya ja hankalin masu ruwa da tsaki a gasar La Liga ta Sifani, har ma jagoran gasar ta La Liga Javier Tebas, cikin wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ke cewa, Wu Lei ya taka rawar gani a tsarin wannan gasa, yana mai cewa, akwai yiwuwar shigar da karin 'yan wasa Sinawa cikin tsarin ta.

Tevas wanda ya zanta da kafar kamfanin dillancin labarai ta kasar Sin Xinhua a baya bayan nan, ya ce Wu Lei ya yi namijin kwazo, ya kuma baiwa kulaf din da yake bugawa tamaula gudunmawa a wasanni da dama. Ya ce himmarsa ta zaburar da burin karin kulaflikan dake buga wannan gasa, wajen daukar karin 'yan wasan Sin masu kwarewa, ciki hada manyan kulaflikan Sifaniya.

Tebas ya ce "Ko shakka ba bu: da yawa daga kulaflikan La Liga na da sha'awar shigar da 'yan wasan kwallon kafa daga Sin cikin kungiyoyin su, kuma tuni ma suka fara daukar matakan tabbatar da hakan. Wasun su sun riga sun isa Sin domin hakan, yayin da wasu kuma 'yan wasan ke shirin tawo wa nan.

A da can, manyan kungiyoyin kwallon kafa, kamar Real Madrid da Barcelona ne ke da tasiri a kungiyoyin kwallon kafar Sin. Amma a baya bayan nan, La Liga na kara maida hankali ga matsakaitan kulaflika, ta yadda su ma za su zamo masu shiga a dama da su a wannan fanni, ciki hadda kungiyoyi irin su Espanyol. Hakan na nufin, muna da burin ganin karin kulaflika su shiga harkar zakulo 'yan wasa daga Sin," a cewar Tebas.

Wannan dai tsokaci na shugaban hukumar La Liga na zuwa ne, yayin da hukumar ke daukar matakan tallafawa kanana, da ma tsakaitan kungiyoyin kwallon kafar dake cikin wannan tsarin gasa ta Sifaniya, da yadda za su bude shafuka a dandalin sada zumunta da Sinawa ke mu'amala da su, ta yadda Sinawa za su rika cudanya da su yadda ya kamata. Muna kuma fatan karin Sinawa 'yan kwallon kafa za su samu damar shiga tsarin gasar La Liga ba tare da bata lokaci ba." A cewar Tebas.

Da ya tabo dabarun da hukumar sa ke bullowa da su, domin jan hankalin Sinawa masu sha'awar kwallon kafa kuwa, Tebas ya ce sanya lokutan buga wasanni, da tsara su daidai da lokutan da za a iya kalla, na da muhimmanci wajen janyo kasuwar kasar Sin. Ya ce hukumar La Liga na da shirin saita lokutan gudanar da wasanninta, ta yadda za su dace da lokuta mafiya dacewa ga 'yan kallo Sinawa. Kafin hakan, hukumar na samar da tallafi ga karin kulaflika, ta yadda za su samu damar buga wasa a kasar ta Sin. Tebas ya kuma bayyana burin sa na ganin Espanyol ta samu damar buga wasa a Sin cikin lokacin bazarar bana.

A madadin La Liga, Mr. Tebas ya ce ya cimma wata yarjejeniya da hukumar kwallon kafar kasar Sin ta (CFA), game da batutuwa da suka shafi horas da matasan 'yan wasa, da gina tsarin gasanni, da samar da tsaro a filayen wasa, da samar da tambarin kulaflika, da batun habaka kungiyoyin kwallon kafar mata. Ya ce hadin kai daga dukkanin fannoni, musamman a bangaren horas da matasan 'yan wasa, na cikin abubuwan da za a bunkasa.

A ganin wannan babban jami'i, juriya na cikin muhimman matakai da ya dace a dauka, wajen bunkasa kulaflikan kwallon kafar kasar Sin, musamman a bangaren horas da matasan 'yan kwallo.

Ya ce Sifaniya na maida hankali matuka ga horas da matasan 'yan wasa, kuma Sin na da matasa masu tarin yawa dake da basirar taka leda, ciki hadda kwararru masu tarin yawa. Ya ce yana da imanin cewa Sin za ta ci gajiya mai tarin yawa daga hakan.

Jagoran na La Liga ya kara da cewa "kwallon kafar kasar Sin na kan turba ta gari. To sai dai kuma nasara ba abu ne da za a iya samu cikin dan kankanen lokaci kamar shekara 2 ko 3 ba, abun da ya dace a sa a gaba shi ne juriya. Na yarda da burin Sin na ganin ta cimma nasara cikin sauri, amma Sifaniya ita ma sai da ta shafe shekaru sama da 90 kafin ta dauki kofin duniya a karon farko." A cewar Tebas.

Game da kwazon da kasar ke yi domin cimma wannan buri kuwa, Tebas ya ce Sin na dukufa matuka, kuma tana da damar kaiwa ga wannan nasara muddin ta ci gaba da nacewa hakan.

Game da gasar zakarun kulaflikan kasar Sin ta CSL kuwa, jami'in ya ce gasar na da ikon samar da kwararrun 'yan wasa, idan har ta ci gaba da samun kudaden gudanarwa da kulawar da ta kamata. Idan har hakan ya samu, a cewar sa CSL na iya shiga jerin gasanni 5 ko 6 na farko mafiya karfi a duniya baki daya.

Tebas ya ce cikin kungiyoyin kwallon kafa dake taka leda a gasar CSL, Beijing Guoan ta burge shi matuka. Ya ce ya jima yana lura da wannan kungiya, kasancewar ta wadda ke da dadadden tarihin samun nasarori tsakanin daukacin kungiyoyin kwallon kafar kasar baki daya.

Daga nan sai ya yi fatan ganin 'yan wasan kwallon kafa Sinawa sun ci gaba rike matsayin su tsakanin takwarorin su na sassan duniya, yana mai musu fatan samun karin nasarori, a gasannin su na gida da na kasa da kasa.(Saminu Alhassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China