Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Matakin Amurka na karawa Sin haraji zai kawowa duk bangarorin biyu illa
2019-05-10 17:44:25        cri
Da karfe 12 da minti 1 na daren ranar 9 ga wata bisa agogon Washington, wato karfe 12 da minti 1 na rana bisa agogon Beijing, kasar Amurka ta fara karawa Sin haraji da kaso 25% daga kaso 10%, kan kayayyakinta da darajarsu ta kai dala biliyan 200. A nata bangaren kuma, Sin ta bayar da sanarwa a wannan ranar da karfe 12 da minti 3 na rana cewa, dole ta dauki matakai domin mayar martani kan batun.

Lallai wannan abun bakin ciki ne, ganin yadda rigingimu tsakanin Sin da Amurka kan cinikayya ya kara tsananta. Dalilin da yasa haka shine, Amurka ta yi watsi da sahihancin da kasar Sin ta nuna, inda kuma ta ba kanta fifiko, lamarin da ya saba da ka'idar yin shawarwari ta girmama juna da adalci da moriyar juna, har ma ya haddasa tsanantar rigingimun.

Shawarwari yana shafar moriyar sassan biyu, yanzu haka bangaren kasar Sin ya riga ya nuna babban sahihancinsa ta hanyar daukar hakikanan matakai, shi ma yana fatan bangaren Amurka zai yi kokari tare da shi, hakika Sin da Amurka sun riga sun yi tattaunawa kan cinikayya da tattalin arziki sau tarin yawa a cikin shekara daya data gabata, kasar Sin ta fahimci matakan Amurka sosai, a don haka ya kamata Amurka ta fahimci matsayar kasar Sin, wato kasar Sin bata son yakin cinikayya, amma bata ji tsoro ba ko kadan, game da sabani da rigingimu kan cinikayya da tattalin arziki dake tsakanin sassan biyu, kasar Sin tana son daidaita su ta hanyar yin hadin gwiwa, amma dole ne a gudanar da hadin gwiwar bisa wani tushe wato kada a lalata babban muradin kasar da babbar moriyar al'ummun kasar ta Sin.

Yanzu ya kamata a lura da cewa, kasar Amurka ta daga harajin kwastam ne ba zato ba tsammani, bayan da ta sanar da cewa zata daddale wata yarjejeniya da kasar Sin har sau da dama. Lamarin ya sabawa alkawarin da ta yiwa kungiyar cinikayya ta duniya WTO, ya kuma keta ka'idojin cinikin da ya shafi bangarori daban daban, wanda ko shakka babu zai lahanta moriyar jama'ar kasashen Sin da Amurka, da daukacin duniya. Saboda haka, jama'ar kasashe daban daban, ciki har da na kasar Amurkan, dukkansu sun nuna rashin amincewa kan matakin da kasar Amurka ta dauka. A nasa bangare, shugaban kungiyar 'yan kasuwa ta kasar Amurka Tomas J. Donohue, yace bai yarda da yadda aka kaddamar da yakin ciniki ta hanyar karbar karin harajin kwastam ba. A ganinsa, a karshe dai jama'ar kasar Amurka da kamfanonin kasar ne suke biyan kudin harajin a maimakon 'yan kasashen waje. Wata kungiya mai taken "Tariffs Hurt the Heartland", wadda ke wakiltar kungiyoyin ciniki fiye da 150 na kasar Amurka, ita ma ta sanar da cewa, matakin daga harajin kwastam zai rage guraben aikin yi da yawansa zai kai miliyan 1 a kasar, kuma zai ba manoma, kamfanoni, da masu sayen kaya na kasar Amurka wahala.

Yanzu kasar Amurka ta kara sanya haraji, da nufin hana ci gaban kasar Sin, amma ba zata cimma burinta ba. Ana iya gano cewa, a cikin shekara daya da ta wuce, kasar Sin ta dauki matakin da ya dace wajen tinkarar haka, kana karfin kasar wajen tinkarar matsalar a fannonin tattalin arziki da zamantakewar al'umma da kuma jama'a na karuwa sosai. Yanzu haka, abubuwan dake amfanawa kasar Sin na kara karuwa, ta yadda kasar Sin zata iya fuskantar matsaloli yadda ya kamata, za kuma ta cika da imani wajen daidaita matsaloli daban daban. Kasar Sin zata yi kokarin kara yin kwaskwarima a cikin gida da bude kofa ga kasashen ketare, don ciyar da ci gaban tattalin arziki mai inganci, zata kuma kara samar da damar bunkasuwa ga duniya baki daya.(Masu fassara:Kande, Jamilah, Bello, Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China