Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta yi maraba da ci gaban siyasa da aka samu a Mali
2019-05-07 11:25:30        cri

Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya yi maraba da sanya hannu kan yarjejeniyar siyasa tsakanin gwamnati da bangarori masu adawa a Bamako da kuma kafuwar majalisar zartaswar gwamnati da ta kunshi dukkan bangarori cikin 'yan kwanakin da suka gabata.

Cikin wata sanarwar da kakakinsa Stephane Dujarric ya fitar, Antonio Guterres ya jaddada kudurin MDD na ci gaba da mara baya ga al'umma da gwamnatin Mali, a kokarinsu na neman zaman lafiya da kwanciyar hankali. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China