Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An yi amfani da sabbin fasahohi wajen raya aikin noma a garin Shihezi na kasar Sin
2019-05-07 06:58:05        cri

 


Garin Shihezi yana jihar Xinjiang ne dake yammacin kasar Sin. A baya mazauna yankin na dogoro kan fasahohin gargajiya wajen gudanar da ayyukan noma, amma yanzu an fara amfani da wasu sabbin fasahohi na zamani, matakain da ya haifar da babban ci gaba a fannin aikin noma a wurin.

Tsarin ban ruwa ga tsirrai sannu a hankali yana daga cikin fasahohin da ake amfani da su wajen noman rani. Bisa wannan tsari, a kan jika taki a cikin ruwa, sa'an nan a rika fesa wa daidaikon tsirrai ruwan kadan-kadan a kowane lokaci. Ta wannan hanya, za a iya tsimin ruwa gami da taki baki daya. Wakilin CRI ya je garin na Shihezi a kwanakin baya, inda ya ga yadda tsarin ban ruwa sannu a hankali ya kankama a garin. Dangane da wannan ci gaban da aka samu, Yang Wansen, mataimakin babban manajan wani kamfani mai kula da fasahohin ban ruwa, ya ce kamfaninsa ya shigo da fasahar tsarin ban ruwa ga tsirrai sannu a hankali daga kasar Isra'ila shekaru 20 da suka wuce, sa'an nan ya inganta fasahar. A cewarsa,

"Fasahar ban ruwa ga tsirrai sannu a hankali a karkashin leda, ita ce fasahar ban ruwa a fannin aikin noma daya tak da kasar Sin take fitarwa zuwa kasashen waje. Yanzu haka ta shiga kasashe kusan 17."

Yang ya kara da cewa, wannan fasaha ta taimaka wajen rage wahalar aikin gona, da tsimin ruwa. Ta yadda manoma suke iya kula da karin gonaki, tare da samar da karin amfanin gona. Yang ya ce:

"Muna bukatar zamanintar da aikin noma, kuma muna bukatar kwararrun manoma da suka fahimci tsari na zamani. Mun sa sun kafa kungiyar hadin gwiwa, sa'an nan sun samar da wani tambari na bai daya ga kayayyakinsu. Mun horar da su, da ba su damar samun rance, da ire-iren kayayyakin da suke bukata."

An kafa kungiyar hadin gwiwar manoma ta Hong-Xing-Xiang a shekarar 2018, wadda ke kula da filayen noma da fadinsu ya kai kadada 1500. Yanzu a wannan kungiyar, ana amfani da taraktoci masu sarrafa kansu, wadanda ke gudanar da aiki bisa taimakon tsarin taurarin dan adam na lura da harkokin sufuri na "Beidou'', wajen kula da ayyukan gona daban daban dake dukkan gonakinsu. A cikin gonaki, wakilin CRI ya ga yadda ake amfani da irin wannan tarakta maras matuki wajen huda da shuka iri. A cewar Zhou Run, shugaban kungiyar manoma, ana iya kula da yadda injunan ke gudanar da ayyukansu.

"Ta wadannan fasahohi na zamani, muna iya amfani da gonakinmu yadda ya kamata, wato ba tare da lalata su ba. Sa'an nan tsarin taurarin dan Adam na ba da jagora ga injunan, abin da ya rage mana wahala. Na uku, fasahar na taimakawa wajen kashe kwari, da tabbatar da ingancin amfanin gona."

A da, yayin da manoma suke sarrafa tarakta, su kan yi kuskure, inda suka sanya tayar tarakta ta rika taka shuke-shuke, gami rashin ba da tazarar da ta dace tsakanin shuke-shuken, lamarin da ya hana samar da amfanin gona masu yawa sosai. Yanzu an daidaita matsalar daga tushe, ta hanyar yin amfani da tsarin taurarin dan Adam na sufuri. Wani ma'aikacin kungiyar manoma ta Hong-Xing-Xiang mai suna Zhu Wende ya gaya ma wakilin CRI cewa, fasahar zamani da ake amfani da ita ta sa manoma samun karin riba. A cewarsa,

"A shekarun baya, mu kan samar da amfanin gona da nauyinsu ya kai fiye da kilo 100 a filin gona mai eka daya. Yawancinmu mun yi asarar kudi a lokacin. Yanzu ta hanyar kara ingancin amfanin gona, da kula da aikin gona ta hanyar zamani, da yin amfani da tsarin sufuri na Beidou, da fesa maganin kashe kwari da jirage marasa matuki, mun ninka yawan amfanin gonar da muke samu."

A nasa bangare, wani saurayi mai suna Jiang Jinyu, ya sayi jiragen sama marasa matuki guda 2, yana kuma ba da su haya ga manoma wajen taimakawa fesa maganin kashe kwari. A cewarsa, jirgi daya zai iya fesa magani a gonakin da fadinsu ya kai eka 700 zuwa 800 a kowace rana. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China