Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An shirya bikin nunin fasahohin Sin da Afirka a Zimbabwe
2019-05-07 08:03:05        cri

A ranar 29 ga watan Afrilun bana, an kaddamar da bikin nunin fasahohin kasar Sin da kasashen Afirka bisa shawarar ziri daya da hanya daya karo na biyu a dakin nunin hotunan zane-zanen kasar Zimbabwe, babba taken bikin shi ne "shiga Zimbabwe domin kara fahimtar fasahohin Afirka", inda aka yi nune-nunen hotunan zane-zane sama da 120 da 'yan fasahan kasar Sin da kasashen Afirka suka samar.

A yammacin ranar 29 ga watan jiya ne, aka kaddamar da bikin nunin sakamakon cudanyar fasahohin kasar Sin da kasashen Afirka bisa shawarar ziri daya da hanya daya karo na biyu da taron dandalin tattaunawa kan cudanyar al'adun dake tsakanin Sin da Afirka a dakin nunin hotunan zane-zanen kasar Zimbabwe, inda manyan bakin da suka kunshi jami'an gwamnati da 'yan fasaha da jakadun kasashen duniya dake wakilci a Zimbabwe da wasu fararen hula sama da dari daya suka halarci bikin.

Hotunan da 'yan fasahan kasashen Sin da Kenya da Ruwanda da Uganda da Zimbabwe da sauransu suka zana sun nuna sakamakon da aka samu tun bayan da aka fara aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya, haka kuma sun nuna yanayin musamman na al'adun kasashen Afirka.

Kafin bikin, an gudanar da taron kolin dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa bisa shawarar ziri daya da hanya daya karo na biyu a nan birnin Beijing ba da dadewa ba, yayin taron, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da wani muhimmin jawabi, inda ya yi nuni da cewa, abu mafi muhimmanci yayin da ake aiwatar da shawarar shi ne kara karfafa cudanyar dake tsakanin kasa da kasa, musamman ma a bangaren al'adu, game da wannan, jakadan kasar Sin dake Zimbabwe Guo Shaochun ya bayyana cewa, bikin nunin sakamakon cudanyar fasahohin dake tsakanin Sin da Afirka zai taimaka wajen kara fahimtar juna tsakanin al'ummun Sin da Zimbabwe, haka kuma zai taimaka wajen kara cudanyar jama'ar sassan biyu, yana mai cewa, "A cikin jawabin da ya gabatar yayin taron kolin dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar kasa da kasa karo na biyu da aka kammala kwanakin baya a birnin Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada cewa, ya dace a kara karfafa cudanyar dake tsakanin al'ummun kasa da kasa, haka kuma ya yi alkawari cewa, kasarsa za ta kara zurfafa hadin gwiwar al'adun tsakanin kasarsa da sauran kasashen duniya. Zimbabwe muhimmiyar kasa ce dake gudanar da hadin gwiwa da kasar Sin bisa shawarar ziri daya da hanya daya, musamman ma a cikin 'yan shekarun da suka gabata, sassan biyu wato Sin da Zimbabwe sun riga sun samu babban sakamakon hadin gwiwa a fannonin al'adu da fasahohi da kiwon lafiya da ba da ilmi da sauransu, duk wadannan za su taimaka wajen kara fahimtar juna dake tsakanin al'ummun kasashen biyu, za kuma su ciyar da huldar dake tsakanin sassan biyu gaba yadda ya kamata."

A watan Oktoban bara ne, ma'aikatar kula da wasannin motsa jiki da al'adu ta kasar Kenya ta shirya bikin nunin sakamakon cudanyar fasahohin Afirka da Sin bisa shawarar ziri daya da hanya daya karo na farko a dakin adana littattafan kasar Sin cikin nasara, yanzu ana gudanar da bikin a Zimbabwe, wadda ke da dadadden huldar zumunci da kasar Sin, mukadashin ministan ma'aikatar kula da wasannin motsa jiki na matasa da fasahohi da harkokin nishadi ta Zimbabwe Kezembe Kazembe ya bayyana ta bakin sakatarensa cewa, har kullum Zimbabwe tana ba da muhimmanci matuka kan dadadden zumuncin dake tsakaninta da kasar Sin, tana fatan za ta kara zurfafa cudanyar al'adu dake tsakanin sassan biyu, yana mai cewa, "Gwamnatin Zimbabwe ta yi farin ciki matuka saboda yadda huldar dake tsakaninta da kasar Sin ta samu ci gaba cikin sauri, muna sa ran cewa, bikin nunin sakamakon cudanyar fasahohin Sin da Afirka zai taimaka wajen kara karfafa cudanyar al'adun dake tsakanin kasashen biyu."

Hakika bikin ya samar da damammakin cudanya ga 'yan fasahan Sin da Afirka, 'dan fasahan Zimbabwe Calvin Chimutuwah wanda ya halarci bikin sau biyu ya bayyana cewa, cudanyar dake tsakanin Sin da Afirka a bangarorin al'adu da fasahohi za ta taimakawa cudanyar dake tsakanin sassan biyu daga duk fannoni, a cewarsa: "Mun lura cewa, shawarar ziri daya da hanya daya tana shafar hanyar siliki, lamarin da ya nuna cewa, tun can can da kasar Sin tana kokarin yin cudanya da kasashen Afirka, yanzu an wannan cimma burin, ina fatan shawarar za ta samar wa 'yan fasaha wani dandalin samar da fasahohi mai inganci."

An shirya karo na biyu na bikin ne karkashin jagorancin ma'aikatar al'adun Zimbabwe, tare kuma goyon bayan ofisoshin jakadancin kasar Sin da kasashen Afirka dake Zimbabwe da kuma asusun cudanyar al'adun Sin da Afirka baki daya.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China