Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shirin "Haske maganin duhu" ya kara karfafa imanin makomar mazauna zirin Gaza
2019-05-07 07:04:39        cri

Masu sauraro, a shekarar 2016, kasar Sin ta fara shiga ana damawa da ita cikin shirin "Haske maganin duhu" na sanya na'urorin samar da lantarki bisa karfin harsken rana a gidaje masu fama da kangin talauci a zirin Gaza da ke Palesdinu. A kwanan baya, wakilin CRI ya je zirin Gaza don ganin yadda ake gudanar da shirin da aka fara shekaru biyu da suka wuce. A cikin shirinmu na yau, za mu kawo muku wannan labari game da "Haske maganin duhu".

Manufar shirin "Haske maganin duhu" ita ce samar da haske wutar lantarki a gidajen dake zirin Gaza ta hanyar sanya musu na'urorin samar da lantarki bisa karfin hasken rana, ta yadda za a kyautata zaman rayuwarsu da kuma kara karfafa imaninsu game dan makomarsu. A ranar 6 ga watan Oktoba na shekarar 2016, Mr. Chen Xingzhong, shugaban ofishin kasar Sin da ke Palesdinu na wancan lokaci ya halarci bikin kaddamar da shirin"haske maganin duhu" da aka yi a jihar Khan Younis da ke zirin Gaza, inda ya yi fatan shirin zai kawo wa mazauna zirin Gaza alheri.

"Ina farin cikin halartar bikin kaddamar da shirin sanya wa gidaje na'urar samar da wutar lantarki bisa karfin hasken rana da aka yi a yankin Khuza'a na birnin Younis da ke zirin Gaza. Sin da Palesdinu aminai ne. A 'yan shekarun da suka gabata, kasashen biyu sun samu ci gaba sosai a fannin hadin kai da cudanyarsu. Ko da yaushe kasar Sin na goyon bayan sha'anin da Palesdinu ke gudanarwa yadda ya kamata. Sin ba ta manta da zirin Gaza ba yayin da take hadin gwiwa tare da Palesdinu. Muna lura da mazauna zirin Gaza ciki har da na yankin Khuza'a. Muna fatan wannan shirin zai taimakawa mazauna zirin yadda ta kamata, da kuma kawo musu alheri a zahiri."

Kungiyar kula da jin dadin jama'a ta Give ta kasar Palesdinu ita ce ta kula da wannan shirin, kungiya ce mai zaman kanta, kuma ba ta nasaba da wata hukumar gwamnati ko jam'iyya. Manufar kungiyar ita ce taimaka wa mutane masu fama da talauci ta hanyar samar musu da ayyukan taimako da horaswa, ta yadda za su samu ci gaba bisa karfin kansu. Riham al-Ghussain, wadda take kula da ayyukan zirin Gaza na kungiyar Give ta bayyana cewa, tun kusan shekarar 2016, ake damawa da kasar Sin a cikin ayyuka uku na zirin mai taken "haske maganin duhu". Tana mai cewa,

"An dukufa wajen warware matsalar karancin wutar lantarki da ake fama da ita a gidaje da asibitoci da ma cibiyoyin ba da jinya ta hanyar gudanar da wannan aiki na samar da wutar lantarki bisa karfin hasken rana, ta yadda za a iya biyan bukatun a wannan fanni. Kawo yanzu dai, an riga an kammala wasu ayyuka, lallai muna godiya ga gwamnatin kasar Sin matuka da taimako da goyon bayan da ta ke baiwa kungiyar Give. Aikin farko shi ne sanya kananan na'urorin samar da wutar lantarki bisa karfin hasken rana a gidaje 45 na birnin Rafah da ke kudancin zirin Gaza. Na biyu shi ne samar da irin wadannan na'urorin ga gidaje 55 da ke birnin Younis a yankin Khuza'a da ke zirin na Gaza. Aikin na uku da ake gudanarwa a kauyen Umm al-Nasr da ke arewacin birnin Gaza zai amfanawa gidaje 65 masu fama da fatara."

Akwai mazauna kusan miliyan 1.9 da ke zama a zirin Gaza a halin yanzu, kashi 80 bisa dari daga cikinsu na zaune ne bisa taimakon da kasa da kasa ke bayarwa. Tun bayan da kungiyar Hamas ta kwace ikon da zirin Gaza bisa karfin tuwa, ko da yaushe kasar Isra'ila ta sanya kangiya a zirin Gaza. yanzu kusan shekaru 11, matsalar jin kai ta zirin tana kara tsananta. A lokacin zafi na bara, Isra'ila ta hana shigar da man fetur da iskar gas cikin zirin Gaza domin ramuwar gayya kan makaman roka da aka harba mata daga zirin Gaza. Lamarin da ya sa aka katse wutar lantarki har na tsawon awoyi 20 a ko wace rana a zirin, sai dai a yi amfani da janareta wajen samar da wutar lantarki. Ko da yake Isra'ila ta rage matakin hana shigar da man fetur da ta yi wa zirin a watanin nan, amma yayin da wakilinmu ke zirin, otel din da ya sauka kan gamu da matsalar katsewar wutar lantarki na wasu 'yan lokuta a kullum. Matsalar ta fi tsanani ga mazauna zirin. Madam Ghussain, wadda ke kula da harkokin zirin Gaza na kungiyar Give ta bayyana cewa,

"bisa binciken da muka yi, katsewar wutar lantarki ta kawo illa sosai ga zirin Gaza. Alal misali, a asibiti, matsalar ta tilasta dakatar da tiyata, lamarin da ya sa tiyatar ta ci tura. Matsalar ta sa ba a iya yin amfani da wasu na'urorin aikin jiyya da majinyata ke dogaro a kai wajen rayuwa. Ban da wannan kuma, matsalar katsewar wutar lantarki ta yi illa sosai ga gidaje, ganin yadda ake samun dimbin marasa lafiya da nakasassu a cikinsu, lamarin da ya haddasa yiwuwar karuwar mutuwarsu. Kamar a kauyen Umm al-Nasr da ake gudanar da aikinmu yanzu, wasu mazauna kauyen na kamuwa da cutar kansa da ciwon zuciya da ciwon koda, wasu kuwa na bukatar taimakon musamman, suna bukatar amfani da na'urorin jiyya masu amfani da wutar lantarki a zaman yau da kullum. Don haka samar musu na'urorin samar da lantarki bisa karfin hasken rana zai taimaka musu wajen rage illar da matsalar karancin lankarki ta haifar musu, har ma da kubutar da rayukansu."

Mohammed Abu Hawaishel mai shekaru 30 da haihuwa yana zaune a kauyen Umm al-Nasr, yana kwanciya jiyya a duk shekara. A cikin gidansa mai bene hawa biyu, bene na farko ne kawai akwai kofa da raga. A cikin dakin kuwa, gado da tebur da kujera ne kawai. Sakamakon kangin talaucin da yake fama da shi, rodi da simintin dake jikin ginin duk a waje suke. Ibrahim Abu Hawaishel, kanen Muhammed da ya kawo masa ziyara, ba ya aiki tun watanni da dama da suka wuce, matarsa kuwa 'yar gudun hijira ce, suna da wata jaririya, don haka dukkan 'yan uwan biyu na fuskantar matsalar rayuwa. Ibrahim ya fadawa wakilinmu cewa, shirin "Haske mmaganin duhu" ya taimakawa rayuwar wansa sosai. Yana mai cewa,

"Wana kan kwanta jiyya a duk shekara, shirin 'Haske maganin duhu' ya taimaka masa sosai. Ya dade yana fama da karancin wutar lantarki a gidansa. Amma tun bayan da aka sanya masa na'urar samar da lantarki bisa karfin hasken rana, wannan matsala ta kau kwata kwata. Mun gode kwarai."

Kauyen Umm al-Nasr wani kauye ne da ke fama da fatara a zirin Gaza, matalauta da 'yan gudun hijira ne duk suka zaune a nan. Dattijo Silmy Ahmed mai shekaru 60 da haihuwa na da yara da jikoki da dama, ban da yaransa da suka bar wajen bayan sun yi aure, kawo yanzu 'yan iyalinsa 12 ne ke cunkushe a cikin dakuna hudu. Sakamakon karancin lantarki, a baya tafasa ruwa da dafa abinci abin damuwa ne a gare su. Amma bayan da suka samu karamar na'urar samar da wutar lantarki bisa karfin hasken rana, wannan matsala ta zama tarihi. Silmy ya gaya wa wakilinmu cewa, sun sha wahala sosai sakamakon rashin lantarki, shirin 'Haske maganin duhu' ya kyautata zaman rayuwarsu matuka. Har ma a lokacin hunturu, na'urar na iya samar da lantarki, lamarin da ya sa su sake gano makomarsu. Ahmad ya ce,

"Muna matukar godiya da sun wutar lantarki. Mu da yaranmu muna zaune a zirin da aka yiwa kagiya. Wannan shirin samar da lantarki bisa karfin hasken rana ya amfana wa gidaje 65 na kauyenmu. Hakan ya saukawa yaranmu, mata kuma na amfani da wasu kananan na'urorin lantarki, kamar su talibijin da fanka. Lallai shirin ya sake tabbatar da imanin zamanmu a nan gaba. Sin aminiyarmu ce, har abada."(Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China