>
Babi12: Matan Sin
>>[Takaitaccen bayani]

Takaitaccen bayani a kan matan kasar Sin

Ya zuwa karshen shekarar 2002, yawan matan kasar Sin ya kai miliyan 620, wanda ya dau kashi 48.5 cikin kashi 100 na dukan yawan mutanen Sin. Gwamnatin kasar Sin ta dora muhimmanci sosai a kan samun ci gaban mata, har ma ta mayar da daidaici tsakanin maza da mata a matsayin wata ainihin manufar kasa. Kuma ta kan tsara manyan manufofin kasa bisa ka'idojin daidaici tsakanin maza da mata da samun bunkasuwa da kuma moriya tare. Wato ke nan, gwamnatin kasar Sin ta ba da tabbaci ga samun ci gaban mata a fannin siyasa da kuma na dokoki.

Tun tsakiyar shekarun 1990, bi da bi ne, gwamnatin kasar Sin ta tsara tsare-tsaren ka'idoji biyu kan bunkasuwar matan Sin, daya na shekaru 5, sauran kuma na 10, wadanda suka tabbatar da halalen ikon matan Sin da kuma kyautata halin da suke ciki, haka kuma sun ciyar da matan Sin gaba a fannoni daban daban. Matan Sin suna da iko daidai wa daida da na maza a fannonin siyasa da tattalin arziki da al'adu da zamantakewar al'umma da iyali da dai sauransu, har ma an mai da aikin kiyaye ikonsu na musamman a matsayin wani muhimmin kashi na kiyaye hakkin dan Adam da gwamnati ke yi, wanda kuma ke jawo kulawa daga gwamnati da zaman al'umma. Bisa kokarin da gwamnatin Sin da bangarori daban daban suke yi, an daukaka matsayin matan Sin sosai, kuma an kyautata halayensu a dukan fannoni, matan Sin sun riga sun shiga wani kyakkyawan mataki na bunkasuwa.

>>[Kungiyoyi]

Hadaddiyar kungiyar dukan matan Sin

Matan Sin daga kabilu da kuma bangarori daban daban sun kafa hadaddiyar kungiyar matan Sin ne a karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta Sin, don neman kara samun 'yancin kai. Ita kungiya ce ta talakawa da al'umma, wadda kuma ke wakiltar matan Sin. Ita kuma wata gada ce wadda ta hada jam'iyyar kwaminis ta Sin da gwamnatin kasar da mata talakawa na kasar Sin. Ita wata muhimmiyar madogara ce ta mulkin kasar.

An kafa kungiyar nan a watan Maris na shekarar 1949, ainihin sunanta shi ne "hadaddiyar kungiyar dimokuradiyya ta dukan matan Sin", daga baya, a shekarar 1957, an canja sunanta zuwa "hadaddiyar kungiyar matan jamhuriyar jama'ar kasar Sin". Ya zuwa shekarar 1978, an sake canja sunanta zuwa "hadaddiyar kungiyar dukan matan Sin".

Alhakin wannan kungiya shi ne hada kan mata da karfafa musu gwiwar shiga ayyukan raya tattalin arziki da zaman al'umma da kuma kiyaye moriyarsu da ingiza samun daidaici tsakanin maza da mata.

Sauran kungiyoyin mata

Kungiyar matasa mata kan addini Christa ta kasar Sin

Hadaddiyar kungiyar shugabanni mata na masana'antun kasar Sin

Kwamitin masu ilmin sanin ma'adinai na kungiyar ilmin sanin ma'adinai

ta kasar Sin

Kwamitin mata na kungiyar kwararru ta kasar Sin

Kungiyar sada zumunta ta mata masu aikin kimiyya ta kasar Sin

Kwamitin mata masu yawon shakatawa na hadaddiyar kungiyar kula da harkokin yawon shakatawa ta kasar Sin

Hadaddiyar kungiyar alkalai mata ta kasar Sin.

Hadaddiyar kungiyar mata masu bincike shari'a ta kasar Sin

Hadaddiyar kungiyar likitoci mata ta kasar Sin

Hadaddiyar kungiyar mata masu daukar hotuna ta kasar Sin

Kwamitin 'yan kwadago mata na babbar kungiyar 'yan kwadago na kasar Sin

Reshen kwamitin mata masu gari na kwamitin masu gari na kasar Sin

Kungiyar nazarin al'adun iyalan kasar Sin

Cibiyar nazarin tsoffin mata ta kasar Sin

Kungiyar asusun raya matan kasar Sin

>>[Mata a cikin harkokin siyasa da na tattalin arziki da kungitoyi]

Matan Sin a harkokin siyasa

Bisa tsarin mulkin kasar Sin, matan Sin suna da iko daidai wa daida da na maza a fannin siyasa: mata suna da 'yancin zabe ko a zabe su daidai da na maza, haka kuma suna da 'yanci daidai da na maza a wajen tafiyar da harkokin kasa ko zama jami'an gwamnati. A gun taron wakilan jama'ar kasar Sin na karo na 10, yawan wakilai mata ya kai 604, wanda ya dau kashi 20.2% na dukan yawan wakilai. Kuma daga cikinsu, 21 wakilai ne na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, wadandan suka kai 13.2% na yawan wakilan majalisar nan. A cikin kwamitin ba da shawara kan harkokin siyasa na zama na 10, yawan wakilai mata na kwamitin nan ya kai 373, wanda ya dau kashi 16.7% na yawan dukan wakilan wannan kwamiti. Don tabbatar da yawan matan da za su shiga cikin harkokin siyasa, ta yadda za su aiwatar da ikonsu a fannin siyasa kamar yadda ya kamata, har ma an kafa wani tsari kan yadda za a zabi shugabanni mata a kasar. A shekarar 2003, akwai mata 7 a kasar Sin wadanda ke kan kujerun manyan mukaman kasar, wato su ne: mataimakiyar firayin minista Wu Yi, mataimakan shugaban majalisar wakilan jama'ar kasar Sin He Luli da Gu XiuLian da Wuyunqimuge, wakiliyar majalisar gudanarwa ta kasar Sin Chen Zhili, da kuma mataimakan shugaban kwamitin ba da shawara kan harkokin siyasa na kasar Sin Liu Yandong da Hao Jianxiu. Ban da wannan kuma, daga cikin ma'aikatu 28 na majalisar gudanarwa ta kasar Sin, mun sami mace daya wadda ta zama minista, da kuma mataimakan minista mata 15. A duk fadin kasar kuma, yawan shugabanni mata na larduna ko kuma na birane sun kai 5056. Matan Sin sun karfafa ra'ayin shiga cikin harkokin siyasa sosai.

A cikin 'tsarin dokokin bunkasuwar matan kasar Sin'(2001-2010), an gabatar da burin da za a cimma cewa, za a kyautata karfin kwarewar mata a fannin tafiyar da harkokin kasa da na al'umma, kuma za a kara yawan matan da za su shiga cikin harkokin siyasa. Ban da wannan, an kuma tanadi cewa, a kalla dai, ya kamata a sami mace daya a cikin gwamnatoci na matakai daban daban, kuma ya kamata a kara yawan shugabanni mata, a fadada hanyar da mata za su bi don su sa hannu cikin harkokin siyasa.

Gwamnatin kasar Sin ita ma tana kokarin kago wani kyakkyawan muhallin don matan Sin su sa hannu cikin harkokin siyasa. Alal misali, tana kara horar da shugabanni mata da kwararru mata, tana kuma kokarin wayar da kansu wajen sa hannu cikin harkokin siyasa.

Matan Sin sun sa hannu cikin harkokin zamantakewar al'umma

Bisa bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewwar al'ummar kasar Sin, matan Sin su ma sun yi ta kara sa hannu cikin harkokin zamantakewar al'umma.

Bisa manufar raya yammacin kasar Sin, matan Sin sun tattara kudaden da yawansu ya kai kudin Sin miliyan 200 don gina ma'adanan ruwa a yammacin kasar, wadanda suka warware matsalar karancin ruwa da mutane dubu 780 na wurin ke fama da ita. Kuma sun aiwatar da "aikin dasa itatuwa na mata", har ma hukumar tsara shirin bunkasuwar muhallin dan Adam ta MDD ta bai wa hadaddiyar kungiyar matan Sin lambar yabo ta " fitattu 500 na duniya".

Bisa "tsarin kai'dojin raya da'ar jama'a", matan kasar Sin sun aiwatar da harkar karanta littattafai masu kishin kasa tsakanin yara da matasa, wadda ta ba da taimako ga matasa da su samu nagartattun halaye.

Sun kuma mai da hankali a kan sabunta ra'ayin tarbiyar iyali, sun kafa ma'aikatun mahaifa dubu 300 bisa hadin gwiwar ma'aikatun da abin ya shafa, wadanda suka bai wa iyaye taimako wajen kyautata tarbiyar iyali.

Harkokin jin dadin al'umma da suka shirya, ciki har da shirin ba da ilmi ga yara mata da shirin zaman lafiya da ranar ba da taimako ga yaran Sin, sun sami goyon baya sosai daga gida da kuma waje, har ma an tattara kudaden da yawansu ya kai kudin Sin yuan miliyan 300, wadanda suka ba da babban taimako wajen kyautata halin rayuwar yara da ke shiyyoyi masu talauci.

Tun shekarar 1950, hadaddiyar kungiyar matan Sin ta fara aikin zaben kyawawan iyalai. Ya zuwa karshen shekarar 1999, iyalai na wurare daban daban da yawansu ya kai kusan dubu 30 sun sami wannan lambar yabo a matsayin larduna ko na kasa. An kuma bayar da labaran wadannan iyalai a kafofin yada labaru. Hadaddun kungiyoyin matan Sin sun kuma shirya aikace-aikace iri daban daban kan al'adun iyali, ta yadda za a samu daidaitattun ra'ayoyi game da duniya da zaman rayuwa da dai sauransu.

A kauyuka ma, sun yi wa manoma jagoranci wajen yin watsi da miyagun al'adu da karfafa ra'ayoyin kiwon lafiya da kyautata muhalli.

>>['Yan mata masu suna]

Mata 'yan siyasa

Song Qingling (1893-1981)

'Yar siyasa, tana daya daga cikin muhimman shugabannin jamhuriyar jama'ar kasar Sin. Ta zo ne daga garin Wenchang na lardin Guangdong. A shekarar 1913, Song Qingling ta gama karatu a jami'ar Weslyan ta mata da ke birnin Macon na jihar Georgia ta kasar Amurka. Sa'an nan a shekarar 1915, ta auri Sun Zhongshan. Bayan da Sun Zhongshan ya riga ta gidan gaskiya a shekarar 1925, ta ci gaba da bin manufofi uku na hada kai da Rasha da jam'iyyoyin kwaminis da kuma goyon bayan manoma da 'yan kwadago. A shekarar 1927 da ta 1929, ta zama shugaba mai daukaka ta kawancen yaki da daulantaka na duniya, wato ke nan, ta zama daya daga cikin muhimman shugabannin kwamitin yaki da fascist na duniya. A shekarar 1931, Song Qingling ta dawo mahaifarta, inda ta dukufa a kan aikin jin dadin al'umma da kuma ayyukan kin harin japanawa. Ta kuma yi suka ga gwamnatin jam'iyyar kwamintang da ta ba da kai ga Japanawa 'yan hari da zaluncin jama'a a gida.

A karshen shekarar 1932, ta kafa "kawancen tabbatar da hakkin Sinawa" don kubutar da 'yan juyin juya hali wadanda ke neman hakkin diplomasiyya. Bayan aukuwar yakin kin harin Japan a kasar Sin, Song Qingling ta kafa "kawancen kare kasar sin" a birnin Hongkong, inda take kokarin tattara magunguna da kayayyaki don nuna goyon baya ga yaki da harin Japanawa da Sinawa ke yi.

Bayan da kasar Sin ta ci nasarar yakin kin harin Japan a watan Satumba na shekarar 1945, Madam. Song Qingling ta yi kira ga jama'ar Amurka da su hana goyon bayan Jiang Jieshi wajen ta da yakin basasa da gwamnatin Amurka ke yi. Ta kuma kafa asusun jin dadin al'ummar kasar Sin, inda ta himmantu a kan aikin jin dadin zaman mata da yara. Bayan kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin, an zabe ta a matsayin mataimakiyar shugaban gwamnatin tsakiya ta jama'ar kasar Sin. Daga baya, bi da bi ne ta hau kan kujerun mataimakiyar shugaban kasa da mataimakiyar shugaban majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da shugaba mai daukaka ta hadaddiyar kungiyar matan Sin da kuma shugabar kwamitin kare yara na jama'ar kasar Sin. A shekarar 1951, ta sami kudin yabo na Stalin kan karfafa zaman lafiya na duniya. A shekarar 1952, ta zama shugabar kwamitin cudanya kan zaman lafiya na shiyyar Asiya da tukun Pacific.

Cai Chang (1900-1990)

Madam Cai Chang mataimakiyar shugaba ce ta majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta hudu da ta biyar. Ita kuma fitacciyar 'yar juyin juya hali ce ta ajin talakawa da shugabar harkar matan Sin kuma shahararriyar 'yar harkar neman ci gaban matan duniya. Ta zo ne daga garin Xiangxiang na lardin Hunan na kasar Sin.

A farko farkon shekarunta, ta je kasar Faransa don yin karatu, a shekarar 1923, ta shiga jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin. A watan Oktoba na shekarar 1934, ta shiga shahararriyar doguwar tafiya mai tsawon kilomita dubu 12.5. Bayan da aka kafa sabuwar kasar Sin a shekarar 1949, ta zama shugabar hadaddiyar kungiyar matan Sin ta farko da ta biyu da ta uku, da kuma shugaba mai daukaka ta kungiyar nan ta hudu. Ita ma wakiliyar kwamitin tsakiya ta takwas da ta tara da ta goma da kuma ta sha daya ta jam'iyyar kwaminis ta Sin. Ban da wannan, ta taba zama wakiliyar majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta daya da ta biyu da ta uku da kuma mataimakiyar shugaban majalisar nan ta hudu da ta biyar.

Deng Yingchao (1904-1992)

'Yar juyin juya hali ce ta ajin talakawa, kuma 'yar siyasa da shugabar harkar matan Sin. An haife ta ne a birnin Nanning na lardin Guangxi, amma 'yar asalin garin Guangshan da ke lardin Henan ce. A shekarar 1919, ta shiga shahararriyar harkar matasa ta 5.4, wato "ran 4 ga watan Mayu", don yaki da daulantaka da mulkin gargajiya, kuma ta shugabanci harkar kishin kasa ta daliban birnin Tianjin tare da tsohon firayin ministan kasar Sin Zhou Wenlai. A shekarar 1925, ta auri Zhou Enlai. Daga baya, ta shiga doguwar tafiya mai tsawon kilomita dubu 12.5. Ta taba zama wakiliyar kwamitin kasar Sin na kungiyar kin harin waje ta duniya. Bayan da jamhuriyar jama'ar kasar Sin ta kafu, ta taba zama mataimakiyar shugaban hadaddiyar kungiyar matan Sin ta farko zuwa ta uku da mataimakiyar sakataren reshen jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin na kungiyar nan da kuma shugaba mai daukaka ta kungiyar ta hudu. Ban da wannan, ta taba hawa kan kujerun mataimakiyar shugaban kwamitin kare yara na jama'ar kasar Sin da shugaba mai daukaka ta hadaddiyar kungiyar sada zumunta da kasashen waje ta kasar Sin. Daga baya, ta zama wakiliyar kwamitin tsakiya na 8 zuwa 12 na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da wakiliyar ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na 11 da na 12, da sakatariya ta biyu na kwamitin bincike shari'a na tsakiya da wakiliyar majalisar wakilan jama'ar kasar Sin na 1 zuwa 3 da kuma mataimakiyar shugabar majalisar nan na 4 da na 5 da wakiliyar majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa na farko da shugabar majalisar nan ta 6.

Shi Liang (1900-1985)

'Yar garin Changzhou ce ta lardin Jiangsu. Ta taba zama mataimakiyar shugaban majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta 5 da ta 6 da mataimakiyar shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta 5 da kuma ministar dokoki ta farko ta gwamnatin jamhuriyar jama'ar kasar Sin. Tana daya daga cikin shugabannin harkar matan Sin, ita kuma 'yar siyasa da shahararriyar lauya ce. Ta kama aikin lauya a shekarar 1931. A shekarar 1936, gwamnatin Kwamintang ta kama ta sabo da ta shugabanci harkar kin harin Japan don ceton jama'ar kasar. Bayan kafuwar sabuwar kasar Sin, ta hau kan kujerar ministar dokoki ta farko ta gwamnatin tsakiya ta jama'ar kasar Sin da wakiliyar kwamitin dokoki na majalisar gudanarwa. Daga baya, bi da bi ne ta zama wakiliyar taron wakilan jama'ar kasar Sin ta farko zuwa ta shida da wakiliyar majalisar wakilan jama'ar kasar ta 2 zuwa ta 5 da mataimakiyar shugaban kwamitin dokoki. Ban da wannan, ta taba zama wakiliyar majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta 1 zuwa 4 da mataimakiyar shugaban majalisar nan ta 5. Sa'an nan, ita ma wakiliyar ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na farko na kawancen dimokuradiyya da mataimakiyar shugaban kwamitin tsakiya na farko zuwa na uku da shugabar kwamitin tsakiya na hudu da na biyar na kawancen nan da kuma mataimakiyar shugaban hadaddiyar kungiyar matan Sin ta 1 zuwa ta 4.

Wu Yi (1938- )

Ita mataimakiyar firayin minista ce ta kasar Sin. 'Yar asalin garin Wuhan na Lardin Hubei. Ta koyi aikin tace man fetur ne a jami'ar koyon ilmin man fetur ta Beijing. A watan Afril na shekarar 1962, Wu Yi ta shiga jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma ta fara aiki a watan Agusta na shekarar 1962. A shekarar 1983 zuwa 1988, ta zama mataimakiyar manajan kamfanin masana'antar man fetur mai suna Yanshan na Beijing da sakatariyar kwamitin jam'iyyar kwaminis ta Sin na kamfanin nan. Tana kan kujerar mataimakiyar mai garin Beijing daga shekarar 1988 zuwa 1991. Kuma daga shekarar 1991 zuwa 1993, tana kan kujerar mataimakiyar ministan harkokin ciniki da kasashen waje da mataimakiyar sakataren reshen jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin. Tun shekarar 1993, ta zama ministar hadin gwiwar ciniki da tattalin arziki da kasashen waje da sakataren reshen jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin na ma'aikatarta. Tana kan mukamin wakiliyar majalisar gudanarwa ne daga shekarar 1998 zuwa 2003. A watan Maris na shekarar 2003, ta zama mataimakiyar firayin ministan kasar Sin da kuma ministar kiwon lafiya a watan Afril na shekarar. Ita kuma ba cikakkiyar wakiliya ba ce a kwamitin tsakiya na 13 na jam'iyyar kwaminis ta Sin, kuma wakiliyar kwamitin nan na 14 zuwa 16 da wakiliyar da ba cikakka ba ta ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na 15 na jam'iyyar kwaminis ta Sin da wakiliyar ofishin nan na kwamitin tsakiya na 16.

Mata 'yan cibiyar nazarin kimiyya ta kasar Sin

Lin Qiaozhi

Kwararriya wajen aikin likitan mata, an haife ta a birnin Xiamen da ke lardin Fujian, a ran 23 ga watan Disamba na shekarar 1901. A shekarar 1929 ta gama karatunta cikin jami'ar koyon ilimin likita ta hadin gwiwa ta birnin Beijing (Peking Union Medical College), kuma ta samu digiri na 3 wajen aikin likita. Ta taba yin bincike kan numfashin da jariri ke yi a cikin mahaifa, da kuma yadda za a warkar da ciwon fukar kwankoson mata. Ban da wannan kuma ta taba yin ayyukan farfaganda domin wayar da mutane da kansu. Ta taba zaman shugaban sashen aikin likitan mata na Asibitin Hadin Gwiwa, da kuma mataimakiyar shugaban cibiyar nazarin aikin likita ta kasar Sin. A shekarar 1955 an zabe ta don ta zama wakiliyar cibiyar nazarin kimiyya ta kasar Sin. Ta rasu a shekarar 1983.

Xie Xide

Kwararriya ce wajen ilimin aikin kira, wato Physics a bakin Turawa. Farofesa na Jami'ar Fudan ta kasar Sin. An haife ta a birnin Quanzhou da ke lardin Fujian, a ran 19 ga watan Maris a shekarar 1921. A shekarar 1946 ta gama karatunta da ke cikin Jami'ar Xiamen. A Shekarar 1951 ta samu digiri na uku wajen ilimin aikin kira a cikin Jami'ar Massachusettes Institute of Technology da ke kasar Amurka. Ban da wannan kuma ta taba samun digiri na uku na daukaka sunanta a cikin jami'o'i masu yawa na kasashen duniya.A shekara 1988, ta zama wakiliyar cibiyar nazarin kimiyya ta duniya ta uku. A shekarar 1980, ta zaman daya daga cikin wakilan cibiyar nazarin kimiyya ta kasar Sin, kuma ta rasu a ran 4 ga watan Maris a shekarar 2000.

He Zehui

Kwararriya ce wajen ilimin Physics na nukiliya. An haife ta a shekarar 1914 a birnin Suzhou da ke lardin Jiangsu. A shekarar 1936 ta gama karatunta a jami'ar Tsinghua. Daga baya ta samu digiri na uku a cikin Jami'ar Masana'antu ta Berlin da ke kasar Jamus a shekarar 1940. A shekarar 1980 an zabe ta don ta zama wakiliyar cibiyar nazarin kimiyya ta kasar Sin.

Jiang Lijin

Kwararriya ce wajen kimiyyar Chemistry, an haife ta a birnin Beijing a shekarar 1919. A shekarar 1944 ta samu digiri na farko a cikin Jami'ar Furen da ke kasar Sin, daga baya ta samu dairi na biyu a cikin jami'ar a shekarar 1946. a shekarar 1951 ta samu digiri na uku a cikin Jami'ar Minnesota da ta Amurka. Kuma ta taba yin nazari a cikin Jami'ar Kansas da ta Massachusettes Institute of Technology da ke kasar Amurka. A shekarar 1955 ta koma kasar Sin. A shekarar 1980 ta zama wakiliyar cibiyar nazarin kimiyyar ta kasar Sin.

Yin Wenying

Kwararriya ce wajen nazarin kwari, an haife ta a shekarar 1922 a Pingxiang da ke lardin Hebei. Ta gama karatunta da ke cikin Jami'ar Tsakiya a shekarar 1947. A shekarar 1991 an zabe ta don ta zama waliliyar cibiyar nazarin kimiyya ta kasar Sin. Yanzu tana aiki a cikin cibiyar nazarin kwari da ke birnin Shanghai.

>>[Kiyaye ikon 'yan mata]

Dokokin da aka kafa domin kiyaye ikon 'yan mata

Yanzu a kasar Sin, ban da dokar kiyaye ikon 'yan mata, an rubuta ka'idoji game da kiyaye ikon 'yan mata a cikin sauran dokoki masu yawa, kamarsu dokar farar hula, da dokar shari'a, da dokar zabe, da dokar kwadago, da dokar aure, da dokar shirya yawan mutanen kasa, da kuma dokar hayan gonaki da dai sauran makamantansu. Tun da aka gabatar da dokar kiyaye ikon 'yan matan kasar Sin a watan Afrilu na shekarar 1992, zaunanen kwamitin majalisar wakilan jama'a ta kasar Sin ya shirya dokoki 12 da suka shafi aikin kiyaye ikon mata, kamarsu dokar kwadago, da dokar kiyaye ikon tsofaffi, da dokar shirya yawan mutanen kasa, da dai sauransu.

Ban da wannan kuma, kasar Sin ta kafa dokar zabe da ta shari'a da ta aure da dai sauran dokoki 4 wadan da suka shafi aikin kiyaye ikon 'yan mata. Majalisar gudanarwa ta kafa ka'idoji 7 da suka shafi kiyaye ikon mata, kuma sauran sassan da abun ya shafa sun gabatar da ka'idoji 98. Domin neman tabbatar da za a gudanar da dokar kiyaye ikon 'yan mata da kyau, an yi ayyukan farfaganda masu yawa, yadda za a wayar wa mutane da kansu wajen kiyaye ikon mata bisa doka.

Ikon yin aiki na 'yan matan kasar Sin

Domin kiyaye ikon yin aiki na 'yan mata, sassan da abun ya shafa na kasar Sin suna kokarin aiwatar da dokar kwadago, inda aka kayyade cewa, a daina nuna ra'ayin bambanci ga 'yan mata yayin da suke neman samun ayyuka, kuma a tabbtar da 'yan mata za su samu albashin da yawansa ya tashi daya da na maza, kuma a kara yawan ayyukan da 'yan mata za su zaba. Ban da wannan kuma, ana bukatar cewa, a kara mai da hankali kan ma'aikata 'yan mata lokacin da suke al'ada da haihuwa da kuma rena yara, kuma a kara bayar da taimako ga 'yan mata da ke zaune a kauyuka, yadda za su samu gonaki da ayyuka.

Ikon koyon ilimi na 'yan matan kasar Sin

Cikin tsarin mulkin kasar Sin da dokar ba da ilimin tilas da dokar kiyaye ikon 'yan mata da dai sauran dokokin da abun ya shafa duka, an kayyade cewa, 'yan mata suna da ikon koyon ilimi kamar yadda maza suke da shi. A shekarar 2001, kashi 99.1 % da ke cikin yaran kasar Sin da shekarunsu ya dace da shiga makaranta suna cikin makaranta, wajen yara 'yan mata kuma, jimlar nan ta kai kashi 99.01%. A shekarar 2002, yawan dalibai 'yan mata da ke cikin makarantar sakandare ya kai miliyan 38.7, wato kashi 46.7 % cikin yawan daliban makarantar sakandare. A cikin jami'o'i ma, yawan dalibai 'yan mata ya kai miliyan 3.97, wato kashi 44% cikin daliban jami'a, jimlar ta karu da 6% bisa jimlar da aka samu a shekaru 5 da suka wuce.

An samo tabbaci ga kiwon lafiyar 'yan matan kasar Sin

Shekarun nan, lafiyar jikin 'yan mata ta kyauttu sosai. Zuwa shekarar 2002, yawan mata masu ciki wadanda suka samu taimakon likita ya kai kashi 86% cikin dukan 'yan mata masu ciki. Yawan mata da suka haihu a cikin asibitin ya kai kashi 78.8 %, ya karu da 12% bisa yawansu na shekaru 5 da suka wuce. Yawan mata da suka mutu yayin da suke kan gwiwa ya ragu daga 63.5 bisa dubu dari na shekarar 1997 zuwa 50.2 bisa dubu dari na shekarar 2002. Matsakaicin tsawon ran 'yan mata ya kai shekaru 73.6 da haihuwa, ya fi na maza da shekaru 3.8.

Yanzu kasar Sin ta kafa kananan asibitoci da yawa a kauyuka. Tun daga shekarar 2000 zuwa ta 2001, gwamnatin kasar Sin ta kara ba da taimako ga wuraren da ke fama da talauci wajen horar da likitoci, musamman ma masu aikin likitan mata, ta haka aka sa masu juna biyu na wurare masu talauci wadanda suke mutuwa ya ragu ainun.

A watan Afril na shekarar 2001, majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta ba da doka kan yadda za a tafiyar da dokar kiyaye lafiyar jikin jariri da na uwarsa, inda aka kayyade ayyukan da asibiti za su yi domin tabbatar da lafiyar jikin jariri da na uwarsa. Zuwa shekarar 2002, ya kasance da asibitocin mata da jarirai 3067, inda yawan gadaje ya kai dubu 80.

Gwamnatin kasar Sin tana mai da hankali kan aikin yaki da cutar AIDS, musamman ma a kan aikin wayar da kan mata da samari kan yadda za a yi rigakafin cutar AIDS da cututtukan da a kan kamu da su ta hanyar jima'i.

Zaman daidaituwa a cikin iyali

A kasar Sin ya kasance da iyalai miliyan 350, yawancinsu an kafa su ne bisa tushen soyaya. A kan samu daidaituwa da jituwa a cikin iyalan, mata suna da ikon yin abin da suka ga dama da kuma rike dukiyoyi.

A watan Afril na shekarar 2001, zaunanen kwamitin na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya bayar da sabuwar dokar aure, inda aka hana auren mata (miji) fiye da guda, da yin zina, da kuma yin kazamin fada a cikin iyali. Ban da wannan kuma an kayyade yawan kudin da za a bayar wa mata bayan da aka sallame ta, domin kiyaye matsayin 'yan mata a cikin iyali.

Domin neman samun daidaituwa da jituwa a cikin iyali, a kan yi gasa a tsakanin iyalai, inda za a nada wa wasu iyalai suna ' iyali mai kyau'. A shekarar 2000, hadaddiyar kungiyar 'yan mata da kuma hukumar alkaluma ta kasar Sin sun zabi wasu 'yan mata na birane da na kauyuka su yi bincike kan matsayinsu a cikin iyalansu, wadanda kashi 93.2% daga cikinsu sun nuna gamsuwa ga matsayinsu da ke cikin iyali.

>>[Musanye]

Mu'amalar da ake yi a tsakanin 'yan matan kasar Sin da na kasashen waje

A watan Yuni na shekarar 1995, an yarda da hadaddiyar kungiyar 'yan matan kasar Sin da ta halarci tarurukan MDD bisa matsayinta na NGO (wato kungiyar da ba ta karkashin jagorancin gwamnati ba). Daga baya, wakilan kungiyar sun halarci tarurukan MDD masu yawa, kamarsu taron kwamitin ikon dan Adam, da taron kwamitin matsayin 'yan mata, da taron musamman kan batun 'yan mata da yara, da kuma taron shugabannin kasashe kan neman samun cigaba mai dorewa, da dai makamantansu. A gun wadannan taron hadaddiyar kungiyar 'yan matan kasar Sin ta bayar da ra'ayinta, ta yadda ta bayar taimako wajen wanzar da zaman lafiya a duk duniya da kiyaye moriyar kasashe masu bunkasuwa da kuma kyautata halin da 'yan mata suke ciki.

Yanzu hadaddiyar kungiyar 'yan matan kasar Sin tana kara yin mu'amala da kungiyoyin kasashen waje, ta riga ta kulla hulda tare da kungiyoyin 'yan mata da yara 700 na kasashe 151. Ban da wanna kuma, ta kira taruruka masu yawa, ciki ya hada da taron 'yan matan kasashen duniya na karo na 4, da taron tattaunawa na kasar Sin da kungiyar EU kan batun 'yan mata, da taron shugabanni 'yan mata na kungiyar APEC, da dai sauran manyan tarurukan duniya. Kungiyar ta riga ta zama kungiyar 'yan mata wadda ke da babban tasiri ga duk duniya.

Hadin gwiwar da ke tsakanin kungiyoyin

'yan matan kasar Sin da na kasashen waje

Yanzu kasashen duniya na kara yin mu'amala da juna, a sabili da haka kuma, kungiyoyin 'yan matan kasashen duniya suna kara yin hadin gwiwarsu wajen kyautata halin da 'yan mata suke ciki. A cikin shekaru 5 da suka wuce, hadaddiyar kungiyar 'yan matan kasar Sin ta yi hadin gwiwa da kungiyoyin kasashen duniya wajen ayyukan kyautata lafiyar jikin 'yan mata, da na yaki da jahilci, da na bayar da bashi, yadda aka bayar da taimako wajen kyautata halin da 'yan mata da yara na kasar Sin suke ciki. Saboda aiwatar da ayyukanta da kyau, kungiyar ta samu yabo mai yawa.

A shekarun nan, kungiyoyin 'yan mata na kasar Sin sun hada kanuwansu da kungiyoyin kasashen duniya wajen aiwatar da ayyuka masu yawa, kamarsu wayar da 'yan mata da kanuwansu game da dokokin da za su yi amfani da du domin kiyaye kansu, da kuma yin yaki da sace mata da ake yi a wasu wurare.

© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China