logo

HAUSA

Kasar Sin Ta Zama Kasuwa Ta Biyu Mafi Girma A Duniya Wajen Shigo Da Kayayyaki Na Tsawon Shekaru 11 A Jere

2021-10-21 19:48:15 CRI

Wasu sabbin bayanai da kungiyar cinikayya ta duniya (WTO) ta fitar sun nuna cewa, rabon yawan kayayyakin da kasar Sin ta shigo da su cikin kasuwar hada-hadar shigo da kaya ta kasa da kasa ya karu da kashi 0.7 bisa dari zuwa kashi 12 cikin 100 a farkon rabin wannan shekara, wanda ya ba da gudummawar kashi 15 cikin 100 na karuwar shigo da kaya a duniya.

A wani taron manema labarai na yau da kullum da ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ta kira yau Alhamis din nan, kakakin ma’aikatar Shu Jueting ta bayyana cewa, a rubu’in ukun farko na bana, darajar kayayyakin da kasar Sin ta shigo da su, ta kai kusan dalar Amurka tiriliyan biyu, wanda ya karu da kashi 32.6 cikin100 kan makamancin lokaci na bara. Ta ce, kasar Sin ta kara bude kofofinta da ma kara shigo da kayayyaki daga ketare. Kana a cikin shekaru 11 a jere, kasar Sin ta zama kasuwa ta biyu mafi girma wajen shigo da kayayyaki a duniya, kana babbar kasuwar da kasashe da yankuna da dama ke shigo da hajojinsu. (Ibrahim)

Ibrahim