Jarin Waje Na Kai Tsaye Da Kasar Sin Ta Shigo Da Shi Ya Karu Da Kaso 19.6 A Watanni 9 Na Farkon Bana
2021-10-20 20:58:41 CRI
Ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ta bayyana a Larabar nan cewa, jarin waje na kai tsaye (FDI) da kasar ta shigo da shi cikin kasar, da aka yi hakikanin amfani da shi, ya karu da kashi 19.6 bisa dari a watanni tara na farkon bana bisa makamancin lokaci na bara.
Daga watan Janairu zuwa na Satumba, jimillar jarin waje na kai tsaye wanda bai shafi harkokin kudi ba da aka shigo da shi cikin kasar, ya kai yuan biliyan 859.5. Idan ana batun dalar Amurka kuwa, jarin waje na kai tsaye da aka shigo da shi cikin babban yankin kasar Sin, ya kai dalar Amurka biliyan 129.3, wanda ya karu da kashi 25.2 bisa dari a kan makamancin lokaci na bara.
Jarin waje na kai tsaye a fannin hidimomi kuwa, ya karu da kashi 22.5 cikin dari na yuan, yayin da masana'antun fasahar zamani ke samun karuwar shigowar waje da ya kashi 29.1 bisa dari kan na shekarar da ta gabata, kamar yadda alkaluman ma’aikatar suka nuna.
Jarin waje da kungiyar kasashen kudu maso gabashin Asiya da kasashen da ke kan “shawarar ziri daya da hanya daya” suka zuba a babban yankin kasar Sin, sun karu da kashi 31.4 bisa dari da kashi 31.9 bisa dari bi da bi. (Ibrahim)
Labarai Masu Nasaba
- Amurka Ba Ta Da Hurumin Sukar Xinjiang Kan Kiyaye Hakkin Dan Adam
- Sin: Amurka tana ikirarin Sin ta tsaurara matakan kera makamai ne don neman karkatar da hankalin duniya
- Sin: Dimokuradiyya ba tsari ne da za a fake da shi ana danniya ba
- Sin: Nasarorin da kasar Sin ta samu wajen kare hakkokin dan Adam sun ja hankalin duniya